{"id":71046,"date":"2022-04-12T15:43:44","date_gmt":"2022-04-12T14:43:44","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=71046"},"modified":"2022-04-12T15:43:44","modified_gmt":"2022-04-12T14:43:44","slug":"bincike-yadda-ganduje-sahale","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/","title":{"rendered":"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi."},"content":{"rendered":"<p><strong>Daga<\/strong>: Usman Bello Balarabe, Kano.\u00a0<strong>Fassara<\/strong>: Rabiu Sani Hassan<\/p>\n<p><strong>Bincike ya tabbata da Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sahalewa damar aikin Hanya a shekara 2019, babu wannan kamfani kwatakwata.<\/strong><\/p>\n<p>Ko da yake dai suma Jami\u2019an Gwamnatin Jihar da aka tambaye su, sun kasa tantance zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 110 da aka sahale domin samar da hanyar da ta lalace sakamakon rashin gyara.<\/p>\n<p>Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karkashin Dafta Abdullahi Umar Ganduje ta fara sahale aikin hanyar Ado Bayero dake Unguwar Dorayi Babba a Karamar Hukumar Gwale ne a shekarar 2019, kuma aka amince aikin zai ci Naira Miliyan 110 a cikin kasafin kudin shekarar 2019, 2020 da kuma shekarar 2021.<\/p>\n<p>An amince da Naira Miliyan 38 domin gudanar da aikin a shekarar 2019, sannan sauran sahalewar ta biyo baya, sai dai Jaridar <a href=\"https:\/\/economicconfidential.com\/\">Economic Confidential<\/a> ta bankado cewa anyi watsi da aikin, ba tare da nuna wata alamar za\u2019a cigaba da yi ba.<\/p>\n<p>Haka kuma jaridar ta <a href=\"https:\/\/economicconfidential.com\/\">Economic Confidential<\/a> ta gano cewa\u00a0 kamfanin da aka sahalewa kwangilar na STONEGATE QUARIES LIMITED, bashi da rijista kwatakwata da hukuma, kuma duk kokarin da jaridar tayi ta kasa gano adreshin kamfanin.<\/p>\n<p>Bisa la\u2019akari da yadda kwararrun ma\u2019aikatan awo tsawon hanya da kuma wasu cikin Al\u2019ummar dake zaune a yankin sun tabbatar da titin nada nisan Kilomita guda (1).<\/p>\n<p><strong>*Babu Kamfanin*<\/strong><\/p>\n<p>STONEGATE QUARIES LTD, wanda ake ba da adreshin sa da gini mai lamba 1011 Domkat Bali Ln. Mabushi District, Abuja, shi ne Kamfanin gine-gine da aka ce ya sami kwangilar. Haka aka rubuta a jikin allon karfe dake dauke da cikakken bayani game da aikin, Dan kwangila da kuma wanda ke lura da aikin.<\/p>\n<p>Dangane da bayanin da aka samu daga Hukumar dake Lura da yiwa Kamfanoni Rejista (CAC) ya bayyana cewa babu kamfanin cikin jadawalin kamfanonin da suka yi Rijista da ita, wannan ya nuna cewa kamfanin babu shi kwata kwata cikin kundin doka.<\/p>\n<p>Sai dai duk kokarin Jaridar ta <a href=\"https:\/\/economicconfidential.com\/\">Economic Confidential<\/a> na nemo sunan kamfanin a kafar yanar gizo, shafin Google bai nuna mata cewa akwai wannan kamfani ba.<\/p>\n<p>Sai dai wani rahoto a hukumanci daga hukumar ta CAC ya bayyana a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022 yace akwai kamfanin gine gine wanda yayi kama da wannan amma sai dai adreshin su ya bambamta.<\/p>\n<p>Kamfanin da gwamnatin Jihar Kano ta sahalewa Aikin sunan shi \u201cSTONEGATE QUARIES LTD\u201d wanda ke da adreshin gini mai lamba 1011 Domkat Bali LN. Mabushi District, Abuja, amma \u00a0shafin hukumar ta CAC akwai kamfani mai suna \u201cSTONEGATE ENGINEERING AND QUARIES LTD\u201d wanda ke da adreshin gini mai lamba 5, Gana Unguwar, Maitama, Abuja,<\/p>\n<p>*Mazauna Yankin Sun Kashe Sama da Naira Miliyan 14 Wajen Gyaran Hanyar*<\/p>\n<p>Duk da Gwamnati ta amince ta naira miliyan 110 tun a shekarar 2019, al\u2019ummar yankin sun yi karo karo inda \u00a0suka hada kudi sama da Naira miliyan 14, suka kashe wajen gyaran titin domin su samu sukuni.<\/p>\n<p>A wata ziyara da tawagar <a href=\"https:\/\/economicconfidential.com\/\">Economic Confidential<\/a> tayi ta iske titin dauke da manyan ramukan da ruwa ke kwanciya, baya ga rashin ingantattun magudanan ruwa, duk da cewa tsaron shekaru 14 mazauna yankin na kokawa kan yadda hanyar ke cikin wannan yanayi, baya ga yanayin wahalar zirga zirga da suke fuskanta, sun koka kan yadda kanana da matsakaitan sana\u2019oi ke fuskantar gagarumar matsala lokacin damuna saboda yanayin hanyar.<\/p>\n<p>Shugaban Al\u2019ummar yankin, Alhaji Usman Aliyu, wanda ke zaune a kan hanyar ta Ado bayero na tsahon shekaru 15, yace mazauna yankin sun bi dukkan hanyoyin da suka kamata wajen sanar da Gwamnatin halin da hanyar ke ciki ko ta dauki mataki amma hakarsu bai cimma ruwa ba.<\/p>\n<p>\u201cTsawon shekaru 14 muna hada kudi a tsakanin mu domin gyaran wannan hanyar, mukan kashe a kalla Naira Miliyan 1 wajen gyara, wani lokacin mukanyi sau 1 wani lokacin sau 2 har sau 3 nuna yi domin gyaran hanyar a shekara, duk da kudin da Al\u2019ummar wannan yanki suka hada.<\/p>\n<p>\u201cA shekarar 2019, Mun ga alamun yinkurin aikin hanyar ta Ado Bayero, inda aka ce gwamnatin Jihar Kano ta saki kudi saboda gyaran, inda aka jibge manyan motocin aiki na tsahon makwanni 2 kafin daga bisani a kwashe su\u201d Kamar yadda yace.<\/p>\n<p>Usman ya kara da cewa hanyar ta Ado Bayero, hanya ce da ta dake sada al\u2019ummar yankin da makarantu, da kuma babban masallaci, Dan Sarari, ga kuma yadda mazauna yankin dake fama da cututtukan dake da nasaba da huhu ke shan wahala, sakamakon shakar kura mai sakamakon watsin da akayi da aikin.<\/p>\n<p>*Yadda Masu Kananan Sana\u2019oi Ke Fuskantar Matsala*<\/p>\n<p>Kananan \u2018Yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwanci akan titin na Ado Bayero sun shaidawa Jaridar <a href=\"https:\/\/economicconfidential.com\/\">Economic Confidential<\/a> yadda rashin kyauwun hanyar ke shafar harkokin kasuwancin su sakamakon rashin ingancin hanyar \u00a0baya ga biyan makudan kudin sufurin kayayyakin.<\/p>\n<p>Wani Dan Kasuwa mai suna Ambasada Abdulyasar Aminu yace watsi da aikin titin ba kawai yana kawo cikas ga ci gaban kasuwancin al\u2019ummar yankin \u00a0ba ne kadai, yana shafar ci gaban tattalin Arziki da dorewar sa a Jihar Kano.<\/p>\n<p>\u201cIn takaici maka bayani ko da a shekara data gabata wakilin kafar BBC ya ziyarci yankin don yin rahoto game da ambaliyar da muke fuskanta duk lokacin damuna, abinda baya rasa nasaba da watsi da wannan aikin hanya da kuma rashin magudanar ruwa a hanyar.<\/p>\n<p>\u201cMuna kira ga gwamnati da ta yi abinda ya kamata saboda yadda gidajen mu ke fama da ambaliyar ruwa a lokacin damuna, yayin da muke fama da karancin abokan hulda kasuwanci sakamakon kurar da ke shiga Shaguna, Rumfuna da Gidajen mazauna wannan yanki.<\/p>\n<p>Wani Dan Kasuwa dake kasuwanci a yankin, Mahdi Bashir ya bayyana cewa akwai fargabar Al\u2019ummar wannan yanki ka iya tashi su koma wata unguwar sakamakon watsi da hanyar da aka yi.<\/p>\n<p>Bashir ya kara da cewa \u201cLokacin damuna yanayin yafi kazanta ga dukkan \u2018Yan kasuwa da mazauna yankin, ta yadda suke shan wahala tare da gwagwarmayar killace gidajen su daga ambaliyar ruwa, lokacin rani kuwa kurar dake tasowa daga titin ita ce babbar matsalar da Al\u2019ummar yankin ke fuskanta.<\/p>\n<p>*Yadda Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano ya Kalubalanci Dan Jarida: \u201cMene ya shafe ka da aikin hanyar?\u201d*<\/p>\n<p>A kokarin samar da da daidaito ta hanyar jin ta bakin ko wanne bangare kamar yadda Aikin Jarida yayi tanadi, <a href=\"https:\/\/economicconfidential.com\/\">Economic Confidential<\/a> ta tuntubi kwamishinan ayyuka na Jihar Kano Engr. Idris Wada Saleh, bayan kiran wayar tarho da sakon karta kwana da aka yi masa, daga karshe ya nemi wakilinmu da ya bayyana masa shin aikin hanyar na mazaba ne ko Jiha ko kuma gwamnatin tarayya, ko kuma aikin wani mutum guda ne.<\/p>\n<p>Bayan da wakilin namu yayi masa cikakken bayani kan aikin, sai ya kada baki yace \u201cWaye ya ce maka bai cancanta ba?, kuma menene matsalarka da hakan? Ba a yi aikin yadda ya kamata ba ko kuma bai biya harajin sa ba?.\u201d<\/p>\n<p>Daga: <a href=\"https:\/\/economicconfidential.com\/\">Economic Confidential<\/a><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga: Usman Bello Balarabe, Kano.\u00a0Fassara: Rabiu Sani Hassan Bincike ya tabbata da Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sahalewa damar aikin Hanya a shekara 2019, babu wannan kamfani kwatakwata. Ko da yake dai suma Jami\u2019an Gwamnatin Jihar da aka tambaye su, sun kasa tantance zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 110 da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":454,"featured_media":71048,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20115],"tags":[20410,3885,20411],"byline":[],"class_list":["post-71046","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-aikin-hanya","tag-dr-abdullahi-ganduje","tag-jihar-kano"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi. - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi. - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Daga: Usman Bello Balarabe, Kano.\u00a0Fassara: Rabiu Sani Hassan Bincike ya tabbata da Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sahalewa damar aikin Hanya a shekara 2019, babu wannan kamfani kwatakwata. Ko da yake dai suma Jami\u2019an Gwamnatin Jihar da aka tambaye su, sun kasa tantance zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 110 da [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:author\" content=\"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2022-04-12T14:43:44+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/2022\/04\/download.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"266\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"189\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:creator\" content=\"@Rabiusanihassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"headline\":\"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi.\",\"datePublished\":\"2022-04-12T14:43:44+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/\"},\"wordCount\":1134,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/04\\\/download.jpg\",\"keywords\":[\"Aikin hanya\",\"Dr. Abdullahi Ganduje\",\"Jihar Kano\"],\"articleSection\":[\"Labarai\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/\",\"name\":\"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi. - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/04\\\/download.jpg\",\"datePublished\":\"2022-04-12T14:43:44+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/04\\\/download.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/04\\\/download.jpg\",\"width\":266,\"height\":189},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/04\\\/12\\\/bincike-yadda-ganduje-sahale\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi.\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\",\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"caption\":\"Rabiu Sani Hassan\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/web.facebook.com\\\/yaronkirki\",\"official_yaron_kirki143\",\"https:\\\/\\\/x.com\\\/@Rabiusanihassan\",\"@Rabiusanihassan\"],\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/hassanrabiusani\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi. - PRNigeria Hausa","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi. - PRNigeria Hausa","og_description":"Daga: Usman Bello Balarabe, Kano.\u00a0Fassara: Rabiu Sani Hassan Bincike ya tabbata da Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sahalewa damar aikin Hanya a shekara 2019, babu wannan kamfani kwatakwata. Ko da yake dai suma Jami\u2019an Gwamnatin Jihar da aka tambaye su, sun kasa tantance zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 110 da [&hellip;]","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_author":"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","article_published_time":"2022-04-12T14:43:44+00:00","og_image":[{"width":266,"height":189,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/2022\/04\/download.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Rabiu Sani Hassan","twitter_card":"summary_large_image","twitter_creator":"@Rabiusanihassan","twitter_misc":{"Written by":"Rabiu Sani Hassan","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/"},"author":{"name":"Rabiu Sani Hassan","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"headline":"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi.","datePublished":"2022-04-12T14:43:44+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/"},"wordCount":1134,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/04\/download.jpg","keywords":["Aikin hanya","Dr. Abdullahi Ganduje","Jihar Kano"],"articleSection":["Labarai"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/","name":"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi. - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/04\/download.jpg","datePublished":"2022-04-12T14:43:44+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/04\/download.jpg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/04\/download.jpg","width":266,"height":189},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/04\/12\/bincike-yadda-ganduje-sahale\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Bincike: Yadda Ganduje ya Sahale Aikin Hanya Mai Nisan Kilomita daya (1) ga Kamfanin \u2018Yan Kwangilar da Babu Shi."}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8","name":"Rabiu Sani Hassan","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","caption":"Rabiu Sani Hassan"},"sameAs":["https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","official_yaron_kirki143","https:\/\/x.com\/@Rabiusanihassan","@Rabiusanihassan"],"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/hassanrabiusani\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/04\/download.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/71046","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/454"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=71046"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/71046\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/71048"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=71046"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=71046"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=71046"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=71046"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}