{"id":72969,"date":"2022-12-19T21:19:35","date_gmt":"2022-12-19T20:19:35","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=72969"},"modified":"2022-12-19T21:19:35","modified_gmt":"2022-12-19T20:19:35","slug":"rahoto-musamman-yadda","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/","title":{"rendered":"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja."},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: left\">RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja.<br \/>\nDAGA: Abbas Badmus da Kabir Abdulsalam<br \/>\nFASSARA: Rabiu Sani Hassan<br \/>\nA shekarar 2018 da Abdulrahman Yusuf ya baro garin Damboa, fitacciyar karamar hukuma a jihar Borno zuwa birnin tarayya Nijeriya Abuja, sakamakon matsalar ayyukan mayakan boko haram da na ISWAP.<br \/>\nCikin kankanin lokaci, ya zauna a babban birnin kasar kuma nan da nan ya fitar da tunanin da yake ciki na irin kisan gilla da \u2018yan ta\u2019adda suka yi wa al\u2019ummarsa da sauran yankunan Arewa maso gabas<br \/>\nDomin tsayawa da kafar sa, Yusuf mai kimanin shekaru 33 a duniya, a lokacin ya sayi babur, wanda zai ke neman taro da kwabo.<br \/>\nBayan mallakar babur din yana amfani dashi wajen kasuwanci wato dai \u2018Achaba\u2019 babur din ya taimaka masa wajen rike kansa da iyalansa da suka yi gudun hijira, zuwa birnin Abuja.<br \/>\nAmma fa wannan ya kasance kawai na tsawon shekaru biyu ne, har zuwa watan Yunin 2021. Tun daga wannan lokaci, rayuwa ta sauyawa Yusuf.<br \/>\nA baya-bayan nan, makomar matashin dan gudun hijira daga jihar Borno ta shiga watangaririya, tun daga lokacin daga aka jefa aikin sa cikin halin ni\u2019yasu, idan ba\u2019a dauki matakin lura da Yusuf ba, akwai yiwuwar cewa zai iya shiga cikin bata gari domin aikata laifuka saboda mawuyacin halin da uake ciki.<br \/>\nDalili: Ma\u2019aikatan Babban birnin tarayya Abuja, FCT karkashin hukumar dake lura da titunan Birnin ta DRTS, ta kwace babur dinsa a watan Julin 2021,<br \/>\nAn \u2018kone\u2019 Babura 1,500 da aka kwace<br \/>\nAmma hukumar ta DRTS bata tsaya nan ba, ta kone a kalla babu 1,500 wanda ta kwace tsakanin watan janairu zuwa Julin 2021; wanda akwai na Yusuf a ciki.<br \/>\nIdan aka lisafta Naira dubu 400,000 akan ko wanne babur, yanzu Babura 1,500 da aka lalata sun tashi a naira 600,000,000.<br \/>\nPRNigeria ta tattaro cewa an kama wasu baburan \u2018Achaba\u2019 1,500. Wanda da alaman an kamasu ne a \u2018yan tsakanin nan, kaga nan ba da jimawa ba zasu fuskanci kwatankwacin halin da dan uwansu ya shiga.<br \/>\nAn kara latata wasu baburan Achaba 1,500<br \/>\nBajimawa sabon daraktan hukumar ta DRTS, Mista Abdullateef Bello, ya bayyana cewa Karin Babura 1,500 da aka kwace hannun masu aikin Achaba a birnin a lalata su.<br \/>\nWannan shine rukuni na biyu na baburan \u2018Achabar\u2019 da aka lalata karkashin hukumar DRTS, cikin watanni 15.<br \/>\nYace \u201cbaburan ana amfani da su ne domin harkokin kasuwanci, wannan ne yasa aka lalata su bayana matukan su sun karya dokokin tuki a birnin.<br \/>\nA shekarar tada gabata wanda Bello ya gada Wadata Bodinga, a watan disamba 2021, da kansa ya sanya idanu domin kona Babura na farko da aka kama.<br \/>\nBello, ya kara da cewa \u201ckamar yadda mukayi shekarar data gabata, wadannan Babura da aka kwace na zaman jiran lokacin da za\u2019a kone\/lalata su.<br \/>\nYa kuma bayyana cewa \u201cidan aka gudanar da wannan aiki, a birnin tarayyar kadai an lalata Babura dubu 3,000 na wadanda ke amfani da su a cikin kwaryar birnin cikin watannin 16, wand aya kara yawan matasa da rayuwar su ta dogara kacokan a wannan aiki na Achaba.<br \/>\nDokar Aikin \u2018Achaba\u2019 a birnin Tarayya Abuja<br \/>\nPRNigeria ta tattaro cewa hukumar babban birnin tarayya, FCTA, a shekarar 2015 ta fidda wata sanarwar dake umartar matuka baburan na \u2018Achaba\u2019 dake Abuja da su daina gudanar da ayyukan su kan manyan titunan dake tsakiyar birnin.<br \/>\nYadda dokar ta yamutsa hazo<br \/>\nKo da yake dokar nada matukar amfani, amma masu kalubantar ta na jefa ayar tambaya kan yadda gwamnati da hukumomin da ke da alhakin dokar, ta yadda suka kirkiri dokar ba tare da jin tausayin na kasaba ko halin da zasu sanya wadanda suka sanyawa dokar.<\/p>\n<p>Sun yi da halin da matuka Babura da suka karya irin wannan doka ke ciki, wanda kama yayi aci tarar sub a wai a kune baburan ba, amma sai mayuka suka wayi gari ana kune musu Babura.<br \/>\nSuna kalubalantar hukuncin, kan domin matuka baburan sun karya dokokin hanyoyi a birnin, mai zai saka a lalata musu Baburan da suke amfani dasu domin gudanar da rayuwar su ta yau da kullum, wannan rashin adalci ne.<br \/>\nKamar dai motoci, suma baburan idan akayi amfani da su wajen sana\u2019ar \u2018Achaba\u2019 suma suna tallafawa wajen habaka tattalin arziki, da kuma ragewa mutane radadi wajen rage musu yin tattaki ko tafiyar kafa.<br \/>\nHaka kuma, samun matasan dake gudanar da sana\u2019ar ta Achaba yana da matukar muhimmancin wajen hana aikata laifuka a duk duniya.<br \/>\nWani binciken wata kungiya ya bankado cewa aikata lafuka ya karu a birnin Abuja da kashi 62 cikin dari (60%) a cikin shekaru 3.<br \/>\nSana\u2019ar Achaba a India<br \/>\nBincike ya nuna cewa a kasar Indiya kasar dake da yawan Babura miliyan 37 (kasa data fi kowacce kasa yawan sa a duniya) ba\u2019a murkushe sub a, duk laifin da masu amfani dashi ke aikatawa.<br \/>\nSaboda mayar da miliyoyin matasan dake sana\u2019ar Achaba marasa aikin yi, kasar ta amince da hukuncin cin tara mai yawan gaske da zaman gidan yari, ga masu keta dokar Ababan hawa a kasar dake yankin Asiya.<br \/>\nAbinda Matakain Vio Ya Haifar Kan \u2018Yan Achaba<br \/>\nKamar yadda akayi tsammani, binciken PRNigeria ya nuna cewa matuka baburan na Achaba, wadanda suka rasa aikin su sakamakon kwace babu da DRTS, wadanda akafi sani da VIO suka yi, tare da murkushe Babura, sun rungumi aikata manayan lafuka.<br \/>\nSukan aikata laifuka daban-daban wanda ke kara ta\u2019azzara rashin tsaro a Abuja.<br \/>\nWannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da rashin aiki yi ga matasa a babban birnin tarayya Abuja ke kara karamari, inda ake samun yawaitar fashi da makami, fashi da makami, \u2018yan fashi da makami, da ayyukan garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.<br \/>\nDuk da haka, ya dace a nuna cewa matsalar rashin aikin yi ba ta dawata matsala a birnin Abuja.<br \/>\nA wani taro daya gudana baya-bayannan, shugaban bankin raya Afirka na AfDB Akinwummi Adesina, ya koka da yadda \u2018yan nijeriya ke fama da matsalar rashin ayyukan yi, indayace kusan kashin 40 na matsan kasar basu da aikin yi.<br \/>\nA cewar Adesina wanda tsohon ministan hukumar noma da raya karkara, matansa Nijeriya \u201csun karaya, sun fusata kasanewar suna neman makomar da bazata kai su ga gaci ba.<br \/>\nWadanda Murkushe Baburan Achabar Ya Shafa<br \/>\nKasancewar s ana wanda wannan lamari ya rutsa dashi, Yahaya lawal ya bayyana yadda aka kama babur dinsa.<br \/>\nA wata tattaunawa da PRNigeria, \u201c watanni 7 da suka gabata, ina kan hanya ta domin kai ziyara da mahaifina wanda tsoho, dake zaune a jihar Kano. Na dauki babur din na bawa dana domin yayi sana\u2019ar Achaba da babur din. Amma kwanaki kadan da yin balaguron, na sami wani kira cewa jami\u2019an karta kwana (tasksforce) sun kama babur dina, tun wancen lokacin yana tsare a hannun su.<br \/>\n\u201cMaganar gaskiya, wannan babur din shine kadai abinda na mallaka. Dashi nake amfani wajen taimakawa iyaye na, na ciyar da \u2018ya\u2019yana, na kuma biya musu kudin makaranta.<br \/>\n\u201cYanzu kuma an karbe shi daga hannun mu da karfin. Ina rokon ka don girman Allah, ka taimake mu su dawo mana da babur di na.<br \/>\n\u201cku fada mususu sakar mana baburan mu, saboda idan babu shi mun gama yawo. Baza ku fahimci halin da muke ciki a yanzu ba.<br \/>\n\u201cYarana basa zuwa makaranat yanzu, an koro su gida, saboda na kasa biya musu kudin makaranta. Saboda yanzu hakan bani da aikin yi,\u201d lawal ya fadawa PRNigeria.<br \/>\nWani matukin babur din Achaba, wanda ya bayyana sunan sa da Abdulrahman, ya bukaci gwamanti ta sauya ko ta duba manufofin ta kan sana\u2019ar ta Achaba a birnin tarayyar.<br \/>\n\u201cSana\u2019ar Achaba itace kadai hanyar da muke bi domin mu rayu. Da ita muke amfani domin taimakawa iyalan mu. Ita kadai ce zaben daya rage mana, idan muka daina achaba zai zame mana wahala mu rayuwa cikin walwala da jin dadi.<br \/>\n\u201cGwamnati da na DRTS su daina kamawa da murkushe baburan mu. Da fatan za\u2019a taimake mu. Mun bar Arewa maso gabas ne saboda rashin tsaro, muka dawo nan don mu samawa iyalan mu abinci.<br \/>\n\u201cAmma har yanzu ba mu da \u2018yancin yin kasuwanci mu na halal. Ya kamata gwamnati ta yi wani Abu, \u201cin ji shi.<br \/>\nWani magidanci dake da mata biyu, Alhaji Babangida, ya ce, \u201cwurin da muka fito daga arewa bashi da aminci ga irin sana\u2019ar mu. Abuja it ace kadai wurinda yawancin mu ke tunanin za mu iya yin Achaba cikin \u2018yanci.<br \/>\n\u201cka tuna wasu cikin mu nada mataye 2. Wasu kuma nada hudu da tarin yara, da kuma wasu dake dogara dasu.<br \/>\nBabangida wanda aka kama babur dinsan babu jimawa, yace \u201cbabur din nasa yana ofishin VIO. Inda aka bukaci ya biya dubu 100 matsayin tara kafin ya karbe shi. Amma jami\u2019an VIO ko saurare basa yi, a kokarin da nake na biyan tarar.<br \/>\nMartanin Kwantirolan Vio<br \/>\nMista Dele YAro, mataimakin kwantrolan, sashen Sumame a shalkwatar Hukumar ta VIO a birnin tarayya Abuja, ya fadawa PRNigeria cewa gwamanti na nuna tausayi ga \u2018yan Achabar dake birnin tarayyar.<br \/>\n\u201cwasu kasashen dama wasu jihohi a Nijeriya sun haramta sana\u2019ar tukin Babura. Amma nan birnin tarayya babu hana ba. Kawai mun sanya musu shinge ne da wasu wurare, a cewar sa.<br \/>\nYaro yace: \u201cHanyoyin sufuri a babban birnin tarayya Abuja sun hadar da dogayen motoci da kanana. Daga baya muka amince da yin amfani Babura masu kafa 3 (Keke NAPEP), a unguwanni Birnin.<br \/>\n\u201cakwai dalilin daya sanya mu daukar wannan mataki na takaita sana\u2019ar Achaba anan. Mun sami rahoton lafuka da suka hadar kwacen jaka, tukin ganganci da wasu lafuka da suka shafi matuka \u2018yan Achaba. Kafin mu haramta achabar a shekarar 2006, asibitocin mu sun cika makil da hadduran da \u2018yan Achaban suka haddasa\u201d.<br \/>\nYa ce wayarda kan Jama\u2019a na guda ciki nauyin daya rataya a wuyan DRTS kuma muna sauke nauyin mu.<br \/>\nMataimakin kwantirolan ya kara da cewa, \u201c mun fara Nikawa\/lalata baburan da muka kama ne bayan gudanar da zanga-zangar EndSars a shekarar 2020, inda mahaya baburan suka kutsa cikin Ofishin mu da karfin tuwo suka kuma kwashe baburan da muka kama.<br \/>\n\u201cDon haka hukumar mu ta dauki gabarar lalata baburan data kama domin kiyaye aukuwar hakan nan gaba.<br \/>\n\u201cMun lalata Babura 1,500 shekarar data gabata, bayan da hukumar ta sami sahalewar babbar kotun tarayya Nijeriya.<br \/>\nYaro yace sanya tara ga \u2018yan Achaba dake Abuja, tamkar bayarda dama ne a cigaba da karya dokokin da aka samar.<br \/>\nA cewar sa \u201chanya daya itace a kwace babur din a lalata shi, haka ne kadai iya zama izini ga sauran.<br \/>\nMun yi musu dukkannin abinda ya dace na wayar da kai. Ko da daraktan mu sai da ya zagaya birnin tarayya domin wayar musu da kai, ana tsaka da haka ya zama darakta.<br \/>\n\u201cAmma duk da haka har yanzu suna karya dokokin hanya, ta yadda akasarin su ke yayo da makamai a jikin su, wanda suke amfani dasu wajen cimma al\u2019umma. Meye yasa suke yawo da makamai indai inda abinda suke akwai gaskiya a cikin sa?<br \/>\nKungiyar Matuka Babura<br \/>\nShugaban kungiyar matuka baburan ta MRA dake Lugbe Yusuf Tahir, yace kungiyar na ta tsaya kai da fata wajen wayar da kan mambobin kan iyakar da aka gindaya musu, na kada su ketara zuwa manyan hanyoyi.<br \/>\nHaka kuma ya kara da cewa \u201c bama kalubalantar gwamnati kan dokar data sakawa \u2018yan Achaba zuwa kwaryar birnin. Amma lalata dubunnan baburan \u2018yan Achaban da aka kama ya jefa da dama cikin rishin aikin yi, wanda ke sake rura wuta rashin tsaro<br \/>\n\u201cina gani da gwamnati ta dauki gabarar horar da mambobin mu ta hanyar shirya bitoci da zasu tabbatar da su wajen dokoki da ka\u2019idojin tuki.<br \/>\n\u201c a kuma girke jami\u2019an tsaro dare da rana akan manya hanyoyin dake Abuja. Wannan zai taimaka wajen haramtawa \u2018yan Achaban gudanar da sana\u2019ar su a kana titunan.<br \/>\n\u201c ina tunani lalata baburan da da aka kama na kara ta\u2019azza gudanar da muggana laifuka. Haka kuma wasu baburan ma\u2019aikatan gwamnati ne suka sayawa matukan domin sake samun kudin shi.<br \/>\n\u201cidan aka lalata baburan da aka kama hakan ka iya zama gagarumar matsala ga mai dukiyar da kuma wanda ke sarrafa ta. Don haka za\u2019a iya saka tara ga wanda ya karya doka. Ko kuma VIO suja hankali ma\u2019aikatan gwamnati dasu san suwa suke bawa dukiyar s uku kuma su basu shawarar bayar da baburan ga matasan da suka san yakamata.<\/p>\n<p>Mafita daga kwararru<br \/>\nSanata Iruegbi, wani mai sharhi kan abinda ya shafi Al\u2019umma, ya nuna bacin rai kan matakin da Gwamnatin ta dauak na lalata baburan daga kama, yace: \u201c ina ganin wannan lamari ne da za\u2019a kira matsayin \u201cCatch-22\u201d, wanda ko dai ya kamata ku mayar da hankali kan tsaron sama da tsaftace muhalli da kyawun birni. Ko kuma akasin haka. Amma kamawa da lalata Babura Achaba ka iya haifar da sakamako maras kyau.<br \/>\nIruegbo, wanda babban Adita ne a Global Sentinel, ya yi Karin haske game da zamantake hadi da tsaro kan dokar Achaba a cikin birnin Abuja.<br \/>\nYa ce; \u201cka ga an yi asara mai tarin yawa domin wadanda abin ya shafa ba kawai baburansu ba ne kawai suka rasa, sun rasa kkudin da sukayi amfani dashi wajen sayo su, da kuma abin suke dogaro da shi.<br \/>\n\u201cduk da haka, kamar yadda na ambata a baya har yanzu gwamnati na bukatar ta kula da tsarin da kuma samar da nutsuwa a cikin babban birnin tarayya Abuja, da kuma gujewa gurbacewar muhalli sanadiyyar \u2018yan Achaba.<br \/>\n\u201c fiye da wannan, ya kamata a samar da mafitar da zata sanya kowa ya gamsu. Ma\u2019ana, ya kamata matuka baburan su rike sana\u2019ar sub a tare da kawo tasgaro ga tsaron da muhalli ga birnin tarayyar kasar ba.<br \/>\nShima a nasa bangare Mista Chidi Omeje, kwararre a harkar tsaro a Abuja, yayi wwatsi da manufar murkushe \u2018yan Achaba.<br \/>\nYace: \u201cAl\u2019amarin yayi muni sosai. Hakan ya nuna irin zaluncin da gwamanti da hukumominta ke yin a lalata hanyoyin rayuwa da wasu \u2018yan Nijeriya amfani da ita.<br \/>\n\u201cta hanyar Murkushe mashinan Achaba na mutane, kuna kuna kiwon masu aikata laifuka; mutanen da basu da wani abu da zasu ji fargabar rasawa, zasu saki tudun dafarwar su, su kuma yada ta\u2019addanci a cikin Al\u2019umma.<br \/>\nAn samar da wannan rahoto ne bisa tallafin cibiyar Nazarin Harkokin Jarida ta wole Soyinka (WSCIJ) a karkashin Hadin Gwiwar Media Engagement for development inclusivity da Accountability Project (CMEDIA) wanda gidauniyar MacArthur ta samar.<br \/>\nBy PRNigeria<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. DAGA: Abbas Badmus da Kabir Abdulsalam FASSARA: Rabiu Sani Hassan A shekarar 2018 da Abdulrahman Yusuf ya baro garin Damboa, fitacciyar karamar hukuma a jihar Borno zuwa birnin tarayya Nijeriya Abuja, sakamakon matsalar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":454,"featured_media":72971,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[1,20115],"tags":[],"byline":[],"class_list":["post-72969","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-general","category-labarai"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. DAGA: Abbas Badmus da Kabir Abdulsalam FASSARA: Rabiu Sani Hassan A shekarar 2018 da Abdulrahman Yusuf ya baro garin Damboa, fitacciyar karamar hukuma a jihar Borno zuwa birnin tarayya Nijeriya Abuja, sakamakon matsalar [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:author\" content=\"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2022-12-19T20:19:35+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/2022\/12\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"661\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"440\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:creator\" content=\"@Rabiusanihassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"11 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"headline\":\"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja.\",\"datePublished\":\"2022-12-19T20:19:35+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/\"},\"wordCount\":2403,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/12\\\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg\",\"articleSection\":[\"General\",\"Labarai\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/\",\"name\":\"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/12\\\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg\",\"datePublished\":\"2022-12-19T20:19:35+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/12\\\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/12\\\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg\",\"width\":661,\"height\":440},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/12\\\/19\\\/rahoto-musamman-yadda\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja.\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\",\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"caption\":\"Rabiu Sani Hassan\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/web.facebook.com\\\/yaronkirki\",\"official_yaron_kirki143\",\"https:\\\/\\\/x.com\\\/@Rabiusanihassan\",\"@Rabiusanihassan\"],\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/hassanrabiusani\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. - PRNigeria Hausa","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. - PRNigeria Hausa","og_description":"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. DAGA: Abbas Badmus da Kabir Abdulsalam FASSARA: Rabiu Sani Hassan A shekarar 2018 da Abdulrahman Yusuf ya baro garin Damboa, fitacciyar karamar hukuma a jihar Borno zuwa birnin tarayya Nijeriya Abuja, sakamakon matsalar [&hellip;]","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_author":"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","article_published_time":"2022-12-19T20:19:35+00:00","og_image":[{"width":661,"height":440,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/2022\/12\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Rabiu Sani Hassan","twitter_card":"summary_large_image","twitter_creator":"@Rabiusanihassan","twitter_misc":{"Written by":"Rabiu Sani Hassan","Est. reading time":"11 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/"},"author":{"name":"Rabiu Sani Hassan","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"headline":"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja.","datePublished":"2022-12-19T20:19:35+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/"},"wordCount":2403,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/12\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg","articleSection":["General","Labarai"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/","name":"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja. - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/12\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg","datePublished":"2022-12-19T20:19:35+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/12\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/12\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg","width":661,"height":440},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/12\/19\/rahoto-musamman-yadda\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"RAHOTO NA MUSAMMAN: Yadda Manufofin Yaki Da \u2018Yan Achaba Ke Haifar Da Asarar Rayuka, Tare Da Ta\u2019azzara Rashin Tsaro A Birnin Abuja."}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8","name":"Rabiu Sani Hassan","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","caption":"Rabiu Sani Hassan"},"sameAs":["https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","official_yaron_kirki143","https:\/\/x.com\/@Rabiusanihassan","@Rabiusanihassan"],"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/hassanrabiusani\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/12\/Confisticated-Okada-Motorcycles-for-Destruction-in-Abuja.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/72969","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/454"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=72969"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/72969\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/72971"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=72969"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=72969"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=72969"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=72969"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}