{"id":73819,"date":"2023-03-29T22:33:01","date_gmt":"2023-03-29T21:33:01","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=73819"},"modified":"2023-03-29T22:33:01","modified_gmt":"2023-03-29T21:33:01","slug":"azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/","title":{"rendered":"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna"},"content":{"rendered":"<p><strong>Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Karyewar jari da damfara da miyagun mafarke-mafarke, shan talgen tuwo da gur\u0253ataccen ruwa da kuma murnar sha\u0199ar iskar &#8216;yanci na cikin abubuwan da har yanzu ke cikin zukatan wasu fasinjojin jirgin \u0199asan Abuja zuwa Kaduna da &#8216;yan Boko Haram suka sace, shekara \u0257aya da ta wuce a jihar Kaduna.<\/p>\n<p>\u018aaya daga cikin fasinjojin 64, Mukhtar Bala Mohammed ya ce bai ta\u0253a zaton zai ku\u0253uta ya koma cikin iyalinsa da rayuwa ba.<\/p>\n<p>&#8220;Har yanzu idan na ji \u0199arar jirgi, sai na firgita, na ruga da gudu,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Mummunan hari ne da ya yi matu\u0199ar tada hankalin Najeriya da dugunzuma &#8216;yan \u0199asar tun bayan sace &#8216;yan matan Chibok a 2014 da jerin satar gomman \u0257alibai &#8216;yan makarantun sakandire a jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna.<\/p>\n<p>Da maryacen ranar Litinin ne 28 ga watan Maris \u0257in 2022, gungun &#8216;yan bindiga suka kai wa jirgin \u0199asan da su Mukhtar ke ciki, yana tsakiyar tafiya a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja hari.<\/p>\n<p>Wani babban al&#8217;amari ne da ya canza rayuwar \u0257an kasuwar mai harkar dillancin man fetur gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>Hukumomi tun a wancan lokaci sun tabbatar da cewa &#8216;yan Boko Haram ne suka kai harin tare da sace gomman fasinjojin jirgin \u0199asan. A cewar Mukhtar Bala sai da ya shafe tsawon kwana 197 cikin dokar daji a hannun masu garkuwar.<\/p>\n<p>Wani babban abu da ya fi bijiro masa a rai yanzu lokacin azumin Ramadan, shi ne yadda suka ri\u0199a shan ruwa bara, idan sun kai azumi da talgen tuwo.<\/p>\n<p>&#8220;Talgen tuwo ne za a zuba mana a cikin \u0257an \u0199aramin kofi. Sai \u0257an \u0199osai haka tsalli&#8221; in ji Mukhtari. &#8220;Ka gan ni nan, wallahi ko azumi \u0257aya ban sha ba. Duk da yake a cikinmu akwai wa\u0257anda suka sha azumi kamar biyu zuwa uku saboda wahala&#8221;.<\/p>\n<p>Ya ce yana farin ciki da ya ku\u0253utarsa, inda a yanzu yake iya shan ruwa bayan ya kai azumi da nau&#8217;in abincin da yake so a cikin iyali.<\/p>\n<p>Gwamnatin jihar Kaduna ta ce &#8220;&#8216;yan ta&#8217;addan da suka kai harin sun karkatar da jirgin \u0199asan daga kan hanyarsa da \u0199arfe 7 na maryace bayan sun \u0257ana abin fashewar da ya tarwatsa wani \u0253angare na kwangirin. Daga nan kuma suka bu\u0257e wa taragon jirgin wuta, kafin sace fasinjojin da ke ciki&#8221;.<\/p>\n<p>Sanarwar da gwamnatin ta fitar don cika shekara \u0257aya da kai mummunan harin ta ce daga bisani an tabbatar da kashe fasinja tara a harin, sai wa\u0257anda aka sace fiye da sittin, baya ga mutum 20 da suka ji raunuka.<\/p>\n<p>Mukhtar Bala Mohammed, magidanci \u0257an shekara 43, ya ce maharan sun kwashe su zuwa \u0257an wani tudu inda suka yi jiran fiye da tsawon sa&#8217;a \u0257aya, kafin su \u0257auke zuwa cikin daji kuma suka shafe kimanin sa&#8217;a biyar suna tafiya.<\/p>\n<p>Ya ce sun yi rayuwa cikin tsoro da barazana, kuma sun ga rashin \u0199auna a tsawon kusan wata bakwai da suka yi a cikin daji.<\/p>\n<p>&#8220;Don gaskiya akwai alamun duk a gun za mu halaka&#8230;. Ga wasu abubuwa da ke zuwa daga cikin gari, na nuna mana rashin \u0199auna. Ko shi ma ya sa duk mun sada\u0199ar a hannunsu za mu mutu. Ga yawan barazanar cewa za a yanka mu. Suna cewa mu mushirikai ne da sauransu,&#8221; a cewar Mukhtar.<\/p>\n<p>Wani lokaci in ji shi, sukan zo, su yi ta yi mana shagu\u0253e, suna cewa idan mallam ya ce a fara yanka ku, ta kan wane da wane, za a fara.<\/p>\n<p>Harkokinmu duk sun dur\u0199ushe<br \/>\nMukhtar Bala ya ce ya yi imani wa\u0257anda suka sace su &#8216;yan Boko Haram kamar yadda gwamnati ta shaida tun ana tsare da su a cikin daji. A cewarsa: &#8220;Yan Boko Haram ne suka ha\u0257u da wani \u0253angare na &#8216;yan ta&#8217;addan daji kuma suka musuluntar da su&#8221;.<\/p>\n<p>Ya ce yana cikin sahun \u0199arshe na fasinjojin da suka ku\u0253uta daga hannun maharan ta hanyar wani kwamitin shiga tsakani da hukumomin Najeriya suka kafa don ganin an ku\u0253utar da dukkaninsu lafiya.<\/p>\n<p>A cewarsa, bayan ya dawo gida ne ya taras duk an sayar da kadarorin da ya mallaka a \u0199o\u0199arin iyali da dangi na ganin an ha\u0257a ku\u0257a\u0257en da za a kar\u0253o shi.<\/p>\n<p>&#8220;Rayuwa a yanzu ta yi min wahala saboda kusan duk harkokina sun tsaya. Jarina ya karye. Ga shi kuma duk an damfari iyalinmu,&#8221; in ji Mukhtar.<\/p>\n<p>Ya ce akwai gida da ya mallaka bayan tsawon lokaci yana tanadi don ya tare da iyalinsa gaba \u0257aya, amma bayan ya ku\u0253uta sai ya taras an sayar da gidan don a ku\u0253utar da shi.<\/p>\n<p>Haka zalika, harkarsa ta dillancin man fetur ma a yanzu ta dur\u0199ushe saboda jarinsa ya karye.<\/p>\n<p>&#8220;Ina zuwa asibiti don kula da lafiyata amma saboda yawan shan magani da \u0199arancin ku\u0257i, sun sa na daina zuwa. Matata har yanzu ta kasa sabawa da halin da nake ciki na firgici da tashin hankali.<\/p>\n<p>Kullum yana zuwa asibiti kuma yana shan in ji Mukhar Bala, amma ba ya ganin sau\u0199i. Wasu \u0199uraje masu kama da \u0199yazbi duk sun fito masa a kai, ga tsananin ciwon kai da yakan yi fama da shi.<\/p>\n<p>Kuma &#8220;Ga mantuwa, sannan abu ka\u0257an ne zai ru\u0257a ni, abu ka\u0257an zan ji ya fusata ni&#8221;.<\/p>\n<p>Ya ce rayuwa a yanzu ta kasance mai matu\u0199ar wahala a gare su. Duk da yake, ya ce yana samun tallafi daga abokan arzi\u0199i.<\/p>\n<p>Gwamnatin jihar Kaduna dai ta ce shekara \u0257aya bayan aukuwar hari a yankin Kasarami-Audu Jangom cikin \u0199aramar hukumar Chikun, har yanzu akwai fasinjojin jirgin \u0199asa da ba su je sun kar\u0253i jakunkunansu ba.<\/p>\n<p>Da take sake mi\u0199a sa\u0199on jajentawa ga iyalan fasinjojin jirgin, gwamnatin Kaduna ta ce bayan bincike da aikin ceto, dakarun tsaro a bara, sun gano jakunkunan fasinjoji da dama kuma sun dam\u0199a su hannunta.<\/p>\n<p>Daga bisani dangi ko iyalan fasinjojin jirgi 62 sun je sun kar\u0253i jaka 94 wa\u0257anda suka \u0199unshi muhimman takardu da fasfuna da mukullan mota da na gida da kudi da katun cirar ku\u0257i da wayoyin salula da kwamfyutocin tafi-da-gidanka da litattafai da turarurruka da tufafi da kuma sar\u0199o\u0199i da &#8216;yan kunnaye.<\/p>\n<p>Sai dai har yanzu akwai sauran jakunkuna guda 16 da ba a je an kar\u0253a ba \u0199unshe da kayayyaki kamar darduma da litattafai da kuma tufafi.<\/p>\n<p>Ga fasinjojin jirgin \u0199asan Kaduna da aka sace kamar Mukhtar Bala, babban abin da suka ce sun fi so a yanzu, ba tsofaffin kayansu ba ne da akasari ba sa bu\u0199atar su, sai dai \u0199wa\u0199\u0199waran tallafi ga lafiya da kuma sake gina rayuwarsu da ta dur\u0199ushe.<\/p>\n<div><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna &nbsp; Karyewar jari da damfara da miyagun mafarke-mafarke, shan talgen tuwo da gur\u0253ataccen ruwa da kuma murnar sha\u0199ar iskar &#8216;yanci na cikin abubuwan da har yanzu ke cikin zukatan wasu fasinjojin jirgin \u0199asan Abuja zuwa Kaduna da &#8216;yan Boko Haram suka sace, shekara [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":453,"featured_media":73820,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20098],"tags":[20777,20778],"byline":[43],"class_list":["post-73819","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-taska","tag-yan-boko-haram","tag-jirgin-kasan-abuja-kaduna","byline-prnigeria"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna &nbsp; Karyewar jari da damfara da miyagun mafarke-mafarke, shan talgen tuwo da gur\u0253ataccen ruwa da kuma murnar sha\u0199ar iskar &#8216;yanci na cikin abubuwan da har yanzu ke cikin zukatan wasu fasinjojin jirgin \u0199asan Abuja zuwa Kaduna da &#8216;yan Boko Haram suka sace, shekara [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2023-03-29T21:33:01+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"300\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"168\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"garbakubura\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"garbakubura\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"garbakubura\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"headline\":\"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna\",\"datePublished\":\"2023-03-29T21:33:01+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/\"},\"wordCount\":1132,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/03\\\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg\",\"keywords\":[\"'Yan Boko Haram\",\"Jirgin Kasan Abuja-Kaduna\"],\"articleSection\":[\"Taska\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/\",\"name\":\"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/03\\\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg\",\"datePublished\":\"2023-03-29T21:33:01+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/03\\\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/03\\\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg\",\"width\":300,\"height\":168,\"caption\":\"Abuja-Khaduna Captives\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2023\\\/03\\\/29\\\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\",\"name\":\"garbakubura\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"caption\":\"garbakubura\"},\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/garbakubura\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna - PRNigeria Hausa","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna - PRNigeria Hausa","og_description":"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna &nbsp; Karyewar jari da damfara da miyagun mafarke-mafarke, shan talgen tuwo da gur\u0253ataccen ruwa da kuma murnar sha\u0199ar iskar &#8216;yanci na cikin abubuwan da har yanzu ke cikin zukatan wasu fasinjojin jirgin \u0199asan Abuja zuwa Kaduna da &#8216;yan Boko Haram suka sace, shekara [&hellip;]","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2023-03-29T21:33:01+00:00","og_image":[{"width":300,"height":168,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/2023\/03\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"garbakubura","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"garbakubura","Est. reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/"},"author":{"name":"garbakubura","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"headline":"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna","datePublished":"2023-03-29T21:33:01+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/"},"wordCount":1132,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/03\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg","keywords":["'Yan Boko Haram","Jirgin Kasan Abuja-Kaduna"],"articleSection":["Taska"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/","name":"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/03\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg","datePublished":"2023-03-29T21:33:01+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/03\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/03\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg","width":300,"height":168,"caption":"Abuja-Khaduna Captives"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2023\/03\/29\/azumin-bara-talge-muka-ri-a-sh\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Azumin Bara: Talge Muka Ri\u0199a Sha a Hannun Maharan Jirgin \u0199asan Abuja-Kaduna"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450","name":"garbakubura","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","caption":"garbakubura"},"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/garbakubura\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/03\/Abuja-Kaduna-Captives.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/73819","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/453"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=73819"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/73819\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/73820"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=73819"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=73819"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=73819"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=73819"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}