{"id":76979,"date":"2025-04-23T12:29:49","date_gmt":"2025-04-23T11:29:49","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=76979"},"modified":"2025-04-23T12:55:02","modified_gmt":"2025-04-23T11:55:02","slug":"bincike-shin-gaske-babban","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/","title":{"rendered":"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris?"},"content":{"rendered":"<p>\u200eIkirari: Wani rubutu da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani da suka hadar da Facebook da shafin X da aka sani da Twitter, ya bayyana cewa babbana bankin Nijeriya (CBN) na shirin samar da takarda kudi ta naira dubu 5 da dubu 10 dake dauke da hotunan manyan shuwagabannin Nijeriya. Dalilin yin takardun kudin kuma shine domin samar da mafita ga matsalar \u0199arincin takardun \u0199udi da ake fada da shi a \u0199asar. Wallafar dai da bayyana cewa ana tsammanin ku\u0257in za su fara fitowa cikin al\u2019umma daga 1 ga watan\u00a0 Mayun 2025. Wanda a jikin rubutun aka hada da hotunan sabbin takardun \u0199udin.<\/p>\n<p>Labarin da aka wallafa a ranar 2 ga watan Afrilun 2025, aka kuma ala\u0199antashi da <a href=\"https:\/\/x.com\/sebastineogb\/status\/1907544069141827810?t=w7BDeNR7-zOEdP4PsTQ2Yg&amp;s=08\">babban bankin \u0199asar cewa ya gabatar da sabbin kudin a hukumance<\/a> da suka ha\u0257ar da Naira dubu 5 da dubu 10 a matsayin wani yun\u0199uri na daidaita hada-hadar kudi da kuma ha\u0253aka tsarin.<\/p>\n<p>A cikin sanarwa, mai dauke da sa hannun mataimakin Gwamnan babban bankin, Dr. Ibrahim Tahir Jr., ta ce samar da sabbin ku\u0257in zai taimakawa \u01b4an Nijeriya matu\u0199a wajen gudanar da harkokin ku\u0257i masu tarin yawa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. haka kuma sanarwa ta kara da cewa matakin ya yi daidai da yadda tsarin ke tafi a duniya gami da inganta harkokin tattalin arziki.<\/p>\n<p>Labarin ya ce naira dubu N5 din na dauke da hoton <a href=\"https:\/\/x.com\/sebastineogb\/status\/1907544069141827810?t=w7BDeNR7-zOEdP4PsTQ2Yg&amp;s=08\">Chief Obafemi Owolowo, ya yi da naira dubu N10 ta ke dauke da hoton Dr. Nnamdi Azikiwe, wanda haka ke matsayin wata girmamawa a garesu bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban \u01b4an Nijeriya<\/a>. Haka kuma ku\u0257in na kunshe da ingantaccen tsaron kudi da suka hadar da launi da dai sauransu.<\/p>\n<p>Sanarwar da bayyana cewa ku\u0257in zasu isa hannun mutane daga ranar 1 ga watan Mayun 2025, ta kuma umarci bankunan kasar da su tabbatar da sun sanya ta a na\u2019urar cirar kudi ta ATM da kuma cikin bankunan ga wadanda za su kar\u0253i kudin a hannu. Haka kuma sanarwa ta shawarci al\u2019ummar \u0199asar da su tabbatar da sun kai an sauya musu tsuffin kudaden su daga 30 da watan Yunin 2025.<\/p>\n<p>An saka adireshin \u00a0<a href=\"http:\/\/cbn.gov.ng\/newcurrency\">cbn.gov.ng\/newcurrency<\/a>, da samfurin kudin a cikin sakon da aka wallafa.<\/p>\n<p>Tarihin yadda Babban Bankin Nijeriya ke gabatar da sabbin ku\u0257i:<\/p>\n<p>\u200eBabban bankin Nijeriya (CBN) shi yake da alhakin samarwa da kuma lura da kudin al\u2019ummar Nijeriya. Ta karkashin sashen dake lura da gudanarwar kudi na babban bakin \u0199asar da aka fi sani da (<em>Currency Operations Department<\/em>) shi ke da alhakin samarwa, lura, rabawa da kuma \u0199one wadanda suka lalace cikin takardun kudin da tsaba.<\/p>\n<p><a href=\"https:\/\/en.m.wikipedia.org\/wiki\/Nigerian_naira#:~:text=Banknotes%20of%20Nigeria,-Old%20Nigerian%20currency&amp;text=In%201991%2C%20%E2%82%A650%20notes,%E2%82%A650%20banknotes%20were%20introduced\">Tun bayan gabatar da kudin \u0199asar a shekarar 1973, an sami \u0199arin samfurin kudin da suka hadar da N 50 a shekarar 1991, N 100 a shekarar 1999, N 200 a shekarar 2000, N 500 a shekarar 2001 da kuma N 1,000 a shekarar 2005<\/a>. Naira dubu daya ta sami sauye sauye \u00a0na inganta tsaron ku\u0257i da suka hadar da sauya launi da kuma kirar ku\u0257in.<\/p>\n<p>A shekarar 2007, an samar da kudin samfurin leda wato (Polymer) na \u20a65 zuwa \u20a650, ledar ku\u0257i ta \u20a620 ita ce ta farko a cikin kudin leda a shekarar 2009, daga bisani aka samar da \u20a65, \u20a610, and \u20a650. Haka kuma an \u0199addamar \u20a6100 ta musamman a shekarar 2014 ga al\u2019ummar Nijeriya, wadda aka mata salo na musamman domin tarihi.<\/p>\n<p>A shekarar 2022, babban bankin na CBN ya bayyana yun\u0199urinsa na sake fasalin kudin domin tallafawa tsarinsa na komawa amfani da hanyar hada-hadar kudi ta zamani (digital currency). Wannan yunkuri na sabunta kudin an kaddamar da shi ne a watan Disambar 2022, ta inda dukkan kudin dake yawo a hannun mutane zai koma banki a karshen shekarar 2023. Sai dai yunkurin ya haifar da matsala a bangaren hada-hadar kudin wanda ya kai ga haifar da zanga-zanga a kasar.<\/p>\n<p>Duk da wannan \u0199alubale da aka samu, bankin CBN ya mayar da hankali gami da jajircewa da kare mutuncin naira ta hanyar sabuntawa lokaci zuwa lokaci da samar da tsaron nairar.<\/p>\n<p>Tabbatar da Sahihancin labari: Domin tabbatar da sahihani ikirarin da ke yawo a kafafen sada zumunta ta zamani, tawagar masu bincike sahihancin labari ta <a href=\"https:\/\/prnigeria.com\/\">PRNigeria<\/a> sun yi amfanin da na\u2019ura binciken hoto ta Reverse Image Search kan ikirarin da aka wallafa a shafin X da aka fi sani da twitter a watan afrilun 2025.<\/p>\n<p>\u200e\u200ebayan binciken da tawagar suka kara fa\u0257a\u0257awa kan wannan sanarwa da ta ambaci \u201cDr. Ibrahim Tahir Jr\u201d. matsayin mataimakin Gwamnan babban bankin dake lura da sashen ku\u0257i da gudanarwa na bankin. Binciken ya duba <a href=\"https:\/\/www.cbn.gov.ng\/\">shafin bankin da kuma rahoton<\/a> shugabancin bankin ya nuna babu wani mai irin wannan sunan da ya gama aiki ko kuma yake aiki a halin yanzu. Babban bankin Nijeriya yana da maitaimaka Gwamnan guda hudu, wa\u0257anda sunayen su yake a bayyana ne amma babu sunan Ibrahim Tahir Jr.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, hotunan dake yawo a kafafen sada zumuntar na \u20a65,000 da \u20a610,000 musamman manhajar WhatsApp, Facebook da Instagram basu da ingantaccen tsarin zane.<\/p>\n<p>Wani bincike na kai da kai da <a href=\"https:\/\/prnigeria.com\/\">PRNigeria<\/a> ta gudanar ya bayyana wasu kura \u2013kura da suka bayyana akan i\u0199irarin sabbin takardun kudin da suka hadar da:<\/p>\n<p>Rashin daidaituwar rubutun jikin kudin \u00a0idan aka kwatanta da wadanda ake amfani da su tun da fari (takardun kudin Nijeriya)<\/p>\n<p>Rashin bayyanar alamun tsaron takardun kudi da suka hadar da:<\/p>\n<p>Wani buyayyen zane (Watermarks)<\/p>\n<p>Tsaron jikin kudi<\/p>\n<p>Launin samfurin kudi<\/p>\n<p>Launin takardun kudin<\/p>\n<p>Wasu daga cikin hoton dake jikin takardun da ake zargin sune sabbin \u0199udin, sun nuna an kwafo su ne a jikin tsuffin ku\u0257in kasar ko kuma kudin \u0199asashen waje.<\/p>\n<p>Launin da aka yi amfani da shi a jikin ku\u0257in ya nuna cewa an yi amfani da na tsuffin ku\u0257in ne karara.<br \/>\nHakazalika, babban bankin na Nijeriya yana gudanar da ayyukan sadarwarsa ta tsatstsauran yanayi. Dukkannin wani mataki mai muhimmanci, musamman wanda ya shafi harkokin kudi, yakan yada ta kafafensa na da suka hadar da:<\/p>\n<p>CBN\u2019s<a href=\"https:\/\/www.cbn.gov.ng\/\">\u00a0official website<\/a><\/p>\n<p>Shaharrun shafukansa na sada zumunta (misali.,<a href=\"https:\/\/twitter.com\/cenbank\">\u00a0@cenbank on X\/Twitter<\/a>)<\/p>\n<p>Taron ganawa da manema labarai da kuma takardar sanarwa.<\/p>\n<p>Jaridun kasa da kuma jaridu masu zaman kansu.<\/p>\n<p>A lokacin da mu ke gudanar da wannan bincike babu wata sanarwa daga wadancan shafuka da ta fito.<\/p>\n<p>Amma, bankin na CBN ya musanta jita-jita, in da ya fitar da sanarwar kai tsaye cewa al\u2019umma su yi watsi da dukkanin nau\u2019in labarai na karya da ake yadawa. A cewa CBN:<\/p>\n<p>\u201c<a href=\"https:\/\/x.com\/cenbank\/status\/1907481966963822681?t=vMFGc-1DKaI1j5mV8fYoRQ&amp;s=08\">Wannan labarin ba daga Babban bankin Nijeriya<\/a> yake ba. Ku fahimci cewa shafin internet mallakin CBN shine cbn.gov.ng.\u201d<\/p>\n<p>\u200eKammalawa: binciken sahihancin labarai da <a href=\"https:\/\/prnigeria.com\/\">PRNigeria<\/a> ta gudanar kan i\u0199irarin da ke cewa babban bankin Nijeriya ya gabatar dabbin takardun kudi na \u20a65,000 da \u20a610,000, ta gano labari ne ba na gaskiya ba. Sanarwar da ke yawo kamar wutar daji a cikin al\u2019umma ba daga CBN ta fito ba, haka kuma bankin ya ce bashi da wata alaka da ita.<\/p>\n<p>Hukunci:\u00a0<a href=\"https:\/\/prnigeria.com\/\">PRNigeria<\/a> ta tabbatar da cewa wannan i\u0199irarin \u0198ARYA ne!<\/p>\n<p><a href=\"https:\/\/prnigeria.com\/\">PRNigeria<\/a><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u200eIkirari: Wani rubutu da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani da suka hadar da Facebook da shafin X da aka sani da Twitter, ya bayyana cewa babbana bankin Nijeriya (CBN) na shirin samar da takarda kudi ta naira dubu 5 da dubu 10 dake dauke da hotunan manyan shuwagabannin Nijeriya. Dalilin yin takardun [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":454,"featured_media":76980,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[21262],"tags":[],"byline":[],"class_list":["post-76979","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-bincike"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris? - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris? - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"\u200eIkirari: Wani rubutu da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani da suka hadar da Facebook da shafin X da aka sani da Twitter, ya bayyana cewa babbana bankin Nijeriya (CBN) na shirin samar da takarda kudi ta naira dubu 5 da dubu 10 dake dauke da hotunan manyan shuwagabannin Nijeriya. Dalilin yin takardun [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:author\" content=\"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-04-23T11:29:49+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2025-04-23T11:55:02+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2025\/04\/SABON-KUDI.png\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"696\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"346\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/png\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:creator\" content=\"@Rabiusanihassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"headline\":\"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris?\",\"datePublished\":\"2025-04-23T11:29:49+00:00\",\"dateModified\":\"2025-04-23T11:55:02+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/\"},\"wordCount\":1177,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2025\\\/04\\\/SABON-KUDI.png\",\"articleSection\":[\"Bincike\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/\",\"name\":\"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris? - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2025\\\/04\\\/SABON-KUDI.png\",\"datePublished\":\"2025-04-23T11:29:49+00:00\",\"dateModified\":\"2025-04-23T11:55:02+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2025\\\/04\\\/SABON-KUDI.png\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2025\\\/04\\\/SABON-KUDI.png\",\"width\":696,\"height\":346},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/04\\\/23\\\/bincike-shin-gaske-babban\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\",\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"caption\":\"Rabiu Sani Hassan\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/web.facebook.com\\\/yaronkirki\",\"official_yaron_kirki143\",\"https:\\\/\\\/x.com\\\/@Rabiusanihassan\",\"@Rabiusanihassan\"],\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/hassanrabiusani\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris? - PRNigeria Hausa","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris? - PRNigeria Hausa","og_description":"\u200eIkirari: Wani rubutu da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani da suka hadar da Facebook da shafin X da aka sani da Twitter, ya bayyana cewa babbana bankin Nijeriya (CBN) na shirin samar da takarda kudi ta naira dubu 5 da dubu 10 dake dauke da hotunan manyan shuwagabannin Nijeriya. Dalilin yin takardun [&hellip;]","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_author":"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","article_published_time":"2025-04-23T11:29:49+00:00","article_modified_time":"2025-04-23T11:55:02+00:00","og_image":[{"width":696,"height":346,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2025\/04\/SABON-KUDI.png","type":"image\/png"}],"author":"Rabiu Sani Hassan","twitter_card":"summary_large_image","twitter_creator":"@Rabiusanihassan","twitter_misc":{"Written by":"Rabiu Sani Hassan","Est. reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/"},"author":{"name":"Rabiu Sani Hassan","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"headline":"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris?","datePublished":"2025-04-23T11:29:49+00:00","dateModified":"2025-04-23T11:55:02+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/"},"wordCount":1177,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2025\/04\/SABON-KUDI.png","articleSection":["Bincike"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/","name":"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris? - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2025\/04\/SABON-KUDI.png","datePublished":"2025-04-23T11:29:49+00:00","dateModified":"2025-04-23T11:55:02+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2025\/04\/SABON-KUDI.png","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2025\/04\/SABON-KUDI.png","width":696,"height":346},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/04\/23\/bincike-shin-gaske-babban\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8","name":"Rabiu Sani Hassan","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","caption":"Rabiu Sani Hassan"},"sameAs":["https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","official_yaron_kirki143","https:\/\/x.com\/@Rabiusanihassan","@Rabiusanihassan"],"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/hassanrabiusani\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2025\/04\/SABON-KUDI.png","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/76979","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/454"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=76979"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/76979\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/76980"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=76979"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=76979"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=76979"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=76979"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}