{"id":77380,"date":"2025-08-15T15:21:45","date_gmt":"2025-08-15T14:21:45","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=77380"},"modified":"2025-08-18T09:25:07","modified_gmt":"2025-08-18T08:25:07","slug":"biya-inmu-son-bashin","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/","title":{"rendered":"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati &#8211; ASUU"},"content":{"rendered":"<p>\u0198ungiyoyin ma&#8217;aikatan manyan makarantun Najeriya na ci gaba da yin watsi da sabon shirin da gwamnatin tarayyar kasar ta \u0253ullo da shi domin inganta jin dadin ma&#8217;aikata, da ha\u0253aka \u0199warewar aiki, ga ma&#8217;aikatan manyan makarantun \u0199asar.<\/p>\n<p>Ita dai gwamnatin Najeriyan ta \u0199addamar da wani sabon shiri wanda aka tsara zai bayar da bashin kudi har naira miliyan 10 ga ma&#8217;aikatan manyan makarantun \u0199asar da suka ha\u0257a da na jami&#8217;a da kwalejin kimiyya da fasaha da kuma kwalejin ilimi.<\/p>\n<p>To sai dai \u0199ungiyoyin ma&#8217;aikatan na ganin cewa ba hanyoyin samar da bashi gare su ya kamata gwamnatin ta \u0253ullo da su ba a wannan lokaci da ake ciki.<\/p>\n<p>Sun ce kamata ya yi gwamnatin ta mayar da hankali wajen inganta albashinsu da kuma biyan su \u0257imbin basukan albashi da na alawus-alawus da suke bin ta.<\/p>\n<p>Kungiyar malaman jami&#8217;o&#8217;i ta Najeriya (ASUU) na cikin masu wannan ra&#8217;ayi, kuma Farfesa Ibrahim Tajo Suraj, shugaban reshen kungiyar na Jami&#8217;ar Bayero ta Kano ya ce su ma labarin Shirin bayar da bashin kawai suka ji a jaridu, amma babu wanda ya tuntu\u0253e su kafin sanarwar gwamnatin.<\/p>\n<p>&#8221;Abin da muke dubawa shi ne, mutum ne yada da ha\u0199\u0199o\u0199insa da ya ke bin ka, maimakon ka biya shi ha\u0199\u0199o\u0199insa sai ka ce za ka ba shi bashi.&#8221; In ji Farfesa Tajo Suraj.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa &#8221;Akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi mana, ba a zo an yi ba na ha\u0199\u0199o\u0199i, kawai sai ka ce za ka bamu bashi. Bashin kuma ai ba nema muka yi ba, na ta\u0253a ba mutum bashi bai nema ba? mu kullum abin da muke cewa shi ne, in dai ka yi shi ne don ka inganta rayuwar ma&#8217;aikatan jami&#8217;oi, mai zai hana ka inganta tsarin albashinsu ba bashi ba.&#8221;<\/p>\n<p>Farfesa Tajo Suraj ya koka da yadda tun 2009 ake ta jan \u0199afa da neman kaucewa yarjejeniyar da suka \u0199ulla da gwamnatin Najeriya, lamarin da ya kai ga an yi wa yarjejeniyar gyaran fuska a lokuta daban-daban har ta kai an cimma matsayar amincewa da ita a bara, abin da ya rage kawai shi ne sa mata hannu ta fara aiki.<\/p>\n<p>&#8221;To maimakon a sa mata hannu ta fara aiki shi ne kuma suka kawo wannan abin na kauda hankalin mutane don su nuna suna \u0199o\u0199arin wai su inganta rayuwar malamnin jami&#8217;a.&#8221;<\/p>\n<p>Malamin jami&#8217;ar ya kuma zayyana abubuwan da \u0199ungiyarsu ke fatan gwamnatin Najeriya ta yi wanda zai kawo mafita ga dukkan \u0199orafin da suke da shi.<\/p>\n<p>Ya ce kamata ya yi gwamnatin ta biya malaman ha\u0199\u0199o\u0199insu da ke kanta, da sake zama domin sabinta yarjejeniyar da \u0253angarorin suka \u0199ulla tun 2009 a kuma sa mata hannu, daga nan kuma &#8221;idan suna son bayar da bashin, to sai su bada bashinsu daga baya, wannan kuma wanda ke so sai ya je ya kar\u0253a, amma ba yadda za ai kana bin mutum bashi, ya \u0199i biyan bashin da kake binsa sai ya ce zai ba ka bashi.&#8221;<\/p>\n<p>To sai dai duk da irin sukar da wannan shiri ya fuskanta daga ma&#8217;aikatan manyan makarantun Najeriya, wa\u0257anda gwamnatin ta ce domi su ta \u0253ullo da shi, gwamnatin ta \u0199addamar da shirin nata, tare da bayanin irin matakai da sharu\u0257\u0257an cikawa kafin ma&#8217;aikatan manyan makarantun su ci gajiyar shirin.<\/p>\n<p>\u0198aramin ministan ilimi a Najeriya Dr Tunji Alausa, ya ce sun \u0199addamar da Shirin, kuma suna sa ran ma&#8217;aikatan manyan makarantun \u0199asar za su shiga domin amfana da shi.<\/p>\n<p>Ya yi bayanin cewa wa\u0257anda ke so za su iya kar\u0253ar bashin har naira miliyan 10, wanda za a rarraba yadda za su biya gwamnatin ku\u0257in a cikin shekaru biyar.<\/p>\n<p>Dr Alausa ya ce shirin wata hanya ce ta sau\u0199a\u0199en wa ma&#8217;aikatan manyan makarantun hanyar samun kudin sayen ababen hawa da samun jarin noma da kuma damar amfani da ku\u0257in wajen zurfafa iliminsu.<\/p>\n<p>Gwamnati da malaman manyan makarantu a Najeriya sun da\u0257e suna musayar kalamai da sukar juna a kan \u0199o\u0199arin inganta tsarin ilimin, inda a lokuta da dama malaman, musamman na jami&#8217;oi ke zargin gwamnatin da nuna halin ko in kula da bu\u0199atun gyara ilimi a \u0199asar, yayin da ita kuma gwamnatin ke dagewa cewa tana bakin \u0199o\u0199arin ta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u0198ungiyoyin ma&#8217;aikatan manyan makarantun Najeriya na ci gaba da yin watsi da sabon shirin da gwamnatin tarayyar kasar ta \u0253ullo da shi domin inganta jin dadin ma&#8217;aikata, da ha\u0253aka \u0199warewar aiki, ga ma&#8217;aikatan manyan makarantun \u0199asar. Ita dai gwamnatin Najeriyan ta \u0199addamar da wani sabon shiri wanda aka tsara zai bayar da bashin kudi har [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":454,"featured_media":71191,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[1,20115],"tags":[],"byline":[],"class_list":["post-77380","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-general","category-labarai"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUU - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUU - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"\u0198ungiyoyin ma&#8217;aikatan manyan makarantun Najeriya na ci gaba da yin watsi da sabon shirin da gwamnatin tarayyar kasar ta \u0253ullo da shi domin inganta jin dadin ma&#8217;aikata, da ha\u0253aka \u0199warewar aiki, ga ma&#8217;aikatan manyan makarantun \u0199asar. Ita dai gwamnatin Najeriyan ta \u0199addamar da wani sabon shiri wanda aka tsara zai bayar da bashin kudi har [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:author\" content=\"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2025-08-15T14:21:45+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2025-08-18T08:25:07+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/05\/ASUU-STRIKE.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1200\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"933\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:creator\" content=\"@Rabiusanihassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"4 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"headline\":\"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati &#8211; ASUU\",\"datePublished\":\"2025-08-15T14:21:45+00:00\",\"dateModified\":\"2025-08-18T08:25:07+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/\"},\"wordCount\":740,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/05\\\/ASUU-STRIKE.jpg\",\"articleSection\":[\"General\",\"Labarai\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/\",\"name\":\"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUU - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/05\\\/ASUU-STRIKE.jpg\",\"datePublished\":\"2025-08-15T14:21:45+00:00\",\"dateModified\":\"2025-08-18T08:25:07+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/05\\\/ASUU-STRIKE.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2022\\\/05\\\/ASUU-STRIKE.jpg\",\"width\":1200,\"height\":933},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2025\\\/08\\\/15\\\/biya-inmu-son-bashin\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati &#8211; ASUU\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\",\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"caption\":\"Rabiu Sani Hassan\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/web.facebook.com\\\/yaronkirki\",\"official_yaron_kirki143\",\"https:\\\/\\\/x.com\\\/@Rabiusanihassan\",\"@Rabiusanihassan\"],\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/hassanrabiusani\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUU - PRNigeria Hausa","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUU - PRNigeria Hausa","og_description":"\u0198ungiyoyin ma&#8217;aikatan manyan makarantun Najeriya na ci gaba da yin watsi da sabon shirin da gwamnatin tarayyar kasar ta \u0253ullo da shi domin inganta jin dadin ma&#8217;aikata, da ha\u0253aka \u0199warewar aiki, ga ma&#8217;aikatan manyan makarantun \u0199asar. Ita dai gwamnatin Najeriyan ta \u0199addamar da wani sabon shiri wanda aka tsara zai bayar da bashin kudi har [&hellip;]","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_author":"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","article_published_time":"2025-08-15T14:21:45+00:00","article_modified_time":"2025-08-18T08:25:07+00:00","og_image":[{"width":1200,"height":933,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/05\/ASUU-STRIKE.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Rabiu Sani Hassan","twitter_card":"summary_large_image","twitter_creator":"@Rabiusanihassan","twitter_misc":{"Written by":"Rabiu Sani Hassan","Est. reading time":"4 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/"},"author":{"name":"Rabiu Sani Hassan","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"headline":"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati &#8211; ASUU","datePublished":"2025-08-15T14:21:45+00:00","dateModified":"2025-08-18T08:25:07+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/"},"wordCount":740,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/05\/ASUU-STRIKE.jpg","articleSection":["General","Labarai"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/","name":"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUU - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/05\/ASUU-STRIKE.jpg","datePublished":"2025-08-15T14:21:45+00:00","dateModified":"2025-08-18T08:25:07+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/05\/ASUU-STRIKE.jpg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/05\/ASUU-STRIKE.jpg","width":1200,"height":933},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2025\/08\/15\/biya-inmu-son-bashin\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"A biya mu ha\u0199\u0199o\u0199inmu, ba mu son bashin gwamnati &#8211; ASUU"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8","name":"Rabiu Sani Hassan","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","caption":"Rabiu Sani Hassan"},"sameAs":["https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","official_yaron_kirki143","https:\/\/x.com\/@Rabiusanihassan","@Rabiusanihassan"],"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/hassanrabiusani\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2022\/05\/ASUU-STRIKE.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/77380","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/454"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=77380"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/77380\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/71191"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=77380"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=77380"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=77380"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=77380"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}