{"id":79944,"date":"2026-03-16T14:15:43","date_gmt":"2026-03-16T13:15:43","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=79944"},"modified":"2026-03-16T14:15:43","modified_gmt":"2026-03-16T13:15:43","slug":"tura-kai-bango-bayan-mutuwar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/","title":{"rendered":"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta"},"content":{"rendered":"<p>Daga Yushau A. Shuaib<\/p>\n<p>Kisan da aka yi wa Malam Bashar Sani, wani babban jami\u2019i a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake \u00a0Maru, wani abin takaici ne da ke nuna irin kalubalen tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya.<\/p>\n<p>Duk da cewa \u2018yan uwan shi sun biya sama da naira miliyan 25.7 a matsayin kudin fansa tare da bayar da babura, wayoyi da katunan waya duk domin a saki dan uwansa da aka sace tsawon shekaru, a \u0199arshe \u2018yan bindigar da suka karbi wadannan makudan kudi ne suka kashe shi.<\/p>\n<p>Shekaru da dama, wa\u0257annan \u2018yan bindiga suna kai hare-hare ga iyalinsa: sun sace matansa biyu, \u0199aninsa, sannan daga baya suka sace shi tare da matarsa da \u2018yarsa da wasu ma\u0199wabta. Duk lokacin da hakan ta faru, iyalan suna sayar da kadarorin da suka mallaka gami da neman taimako domin biyan bukatun \u2018yan bindigar da kullum ke \u0199aruwa.<\/p>\n<p>Ko bayan sun biya naira miliyan 20 tare da \u0199arin babura, sai aka ce musu su jira \u0199arin umarni. Amma ba tare da saninsu ba, Malam Bashar ya riga ya rasu a hannun \u2018yan bindigar sakamakon azabtarwa da raunukan da ba a kula da su ba. Matarsa da \u2018yarsa sun dawo gida; shi kuwa bai dawo ba.<\/p>\n<p>Wannan lamari ba shi ka\u0257ai ya shafa ba, ba kuma a kansa farauba. Yana nuna yadda rashin tsaro ke \u0199ara tsananta a Jihar Zamfara da sauran sassan Arewaci, inda al\u2019umma ke shiga cikin wani Mawuyacin hali na biyan ku\u0257in fansa, gami da kar\u0253ar haraji daga \u2018yan bindiga.<\/p>\n<p>A wasu wurare, kauyuka gaba \u0257aya sun zama kufai. Wasu kuma suna biyan haraji ga \u2018yan bindiga domin su iya noma, aiki ko kuma su sami kwanciyar hankali da daddare. Iyalan mutane suna jinginar da gidajensu, sayar da dukiyoyinsu, ko neman tallafin jama\u2019a domin ceto \u2018yan uwa nsu.<\/p>\n<p>Abin da ya fi tayar da hankali shi ne cewa yawancin masu aikata wannan ta\u2019asa mutane ne da ke magana da harshenmu, suna bin addininmu, kuma kuma al\u2019adunmu daya. Duk da haka suna aikata zalunci da rashin tausayi da ya sabawa Dan Adamtaka. Ba za mu iya ci gaba da cewa wai wasu ba\u0199i ko fatalwowi ne kawai ke aikata hakan ba. Ya zama dole Arewa ta fuskanci wannan Gaskiyar mai daci, mutanenmu na cikin wannan rikici.<\/p>\n<p>A shekarar 2018, na rubuta wata makala mai taken <em>\u201cStill on Murderous Fulani Kidnappers\u201d<\/em>, inda na yi nazari kan yadda wasu da ake dangantawa da Fulani suka shiga harkar garkuwa da mutane wata sana\u2019a da a baya ake dangantawa da wasu \u2018yan bindiga a wasu yankuna.<\/p>\n<p>A wancan lokaci, rahotannin \u2018yan sanda sun nuna cewa wasu da aka kama sun amsa aikata fyade, kisa da sauran miyagun laifuka.<\/p>\n<p>Tambayoyin da na yi a lokacin har yanzu suna nan ba su da amsa:<br \/>\nTa yaya makiyaya suka bar sana\u2019arsu ta gargajiya suka koma garkuwa da mutane? Wa ke ba su makamai na zamani? Me yasa suke kashe mutane ko bayan sun kar\u0253i ku\u0257in fansa? Ta yaya suka koyi dabarun da suka sa suke aiki kamar sojojin suka sami horo? Kuma mafi muhimmanci, ta yaya gwamnati da al\u2019umma za su ha\u0257a kai su kawo \u0199arshen wannan bala\u2019i?<\/p>\n<p>Tun a wani taron \u0199asa da \u0199asa kan kiwo da aka yi a 2014, an yi gargadin cewa \u2018yan ta\u2019adda na iya \u0253oye kansu a cikin makiyaya domin amfani da rikicin manoma da makiyaya. An ba da shawarwari na tsaro, amma ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba.<\/p>\n<p>Yanzu rikicin ya wuce rikicin kiwo kawai. Ya zama rikici da ke da nasaba da talauci, gazawar tsarin tsaro, da kuma shigar \u0199ungiyoyin masu aikata laifi, musamman a wuraren hakar ma\u2019adinai a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Misali, yankin Maru na da ma\u2019adinan zinariya da lithium, wanda ya jawo masu hakar ma\u2019adinai ba bisa ka\u2019ida ba da kuma masu aikata laifi.<\/p>\n<p>\u0198ir\u0199irar Federal Ministry of Livestock Development mataki ne mai kyau, amma dole ne a ha\u0257a shi da tsare-tsaren amfani da \u0199asa, tantance hanyoyin kiwo, da kuma sabbin hanyoyin kiwo kamar ranching da fasahar sa ido kan dabbobi.<\/p>\n<p>Haka kuma, ya zama dole a \u0199arfafa tsaron karkara ta hanyar \u2018yan, tsarin gargadin gaggawa, da kuma kula da iyakoki.<\/p>\n<p>Tattaunawa na da muhimmanci, amma yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka yi a baya sau da yawa sun gaza. Don haka dole ne a magance matsalar \u2018yan bindiga tun daga tushe: dawo da ikon gwamnati a yankunan karkara, gyara rayuwar wa\u0257anda suka tuba, da kuma rusa hanyoyin biyan ku\u0257in fansa.<\/p>\n<p>Amma ba gwamnati ka\u0257ai ba ce ke da alhaki. Arewa kanta dole ta farka. Ba wata \u0199asa ko wata runduna daga waje da za ta zo ta ceci mu. Da za su iya kare kauyukanmu ko gonakinmu. Wannan alhakin na wuyanmu.<\/p>\n<p>Sarakunan gargajiya, malamai, dattawa, matasa da \u0199ungiyoyin farar hula dole su ha\u0257a kai domin dawo da tsaro a cikin al\u2019ummarmu. A lokaci guda kuma, dole ne a samawa matasan karkara hanyoyin rayuwa masu kyau kamar horon sana\u2019o\u2019i, rance ga \u0199ananan sana\u2019o\u2019i, da damar aikin noma.<\/p>\n<p>Arewa ba za ta iya ci gaba da mi\u0199a rayuwarta ga wasu ba. Ba Donald Trump ko wata \u0199asa daga waje da za ta zo ta warware wannan matsala.<\/p>\n<p>Ceton Arewa zai fito ne daga Arewa kanta ko kuma a ci gaba da zama a haka.<\/p>\n<p>Dole mu kare al\u2019ummarmu, mu nemi shugabanni da hukumomin tsaro su yi abin da ya dace, kuma mu \u0199i mi\u0199a \u0199asarmu ga masu laifi da ke magana da harshenmu amma suna cin amanar addininmu da al\u2019adunmu.<\/p>\n<p>A cikin Al-Kur\u2019ani mai girma akwai ayar da ta dace da wannan hali:<\/p>\n<p>Da Allah mahalicci ke cewa<em>\u201cKu ji tsoron fitina wadda ba za ta shafi wa\u0257anda suka aikata zalunci kawai ba daga cikinku, har da marasa laifi.\u201d<\/em> (Al-Anfal: 25)<\/p>\n<p>Wannan fitina ta riga ta zo. Idan ba mu ha\u0257a kai muka fuskanci matsalar \u2018yan bindiga da gaske ba, wannan tashin hankali zai ci gaba, kuma ya zama karshen rayuwar mutanen da ba su ji ba basu gani ba kamar na Malam Bashar Sani.<\/p>\n<p>Tambayar yanzu ita ce: za mu tashi mu yi wani abu kafin karin rayuka su salwanta?<\/p>\n<p>Makomar mu tana hannun mu.<\/p>\n<p>Kuma lokacin \u0257aukar mataki shi ne yanzu.<\/p>\n<p>Yushau A. Shuaib, Marubuci kuma Kwarre a harkar sadarwa, duba www.YAShuaib.com\u00a0 Email: yashuaib@yashuaib.com<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Yushau A. Shuaib Kisan da aka yi wa Malam Bashar Sani, wani babban jami\u2019i a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake \u00a0Maru, wani abin takaici ne da ke nuna irin kalubalen tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya. Duk da cewa \u2018yan uwan shi sun biya sama da naira miliyan 25.7 a matsayin kudin fansa tare [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":454,"featured_media":79945,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20115],"tags":[792],"byline":[],"class_list":["post-79944","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-yushau-a-shuaib"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Daga Yushau A. Shuaib Kisan da aka yi wa Malam Bashar Sani, wani babban jami\u2019i a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake \u00a0Maru, wani abin takaici ne da ke nuna irin kalubalen tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya. Duk da cewa \u2018yan uwan shi sun biya sama da naira miliyan 25.7 a matsayin kudin fansa tare [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:author\" content=\"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-03-16T13:15:43+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/03\/Bashar.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"696\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"522\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:creator\" content=\"@Rabiusanihassan\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Rabiu Sani Hassan\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"headline\":\"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta\",\"datePublished\":\"2026-03-16T13:15:43+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/\"},\"wordCount\":1087,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/03\\\/Bashar.jpeg\",\"keywords\":[\"Yushau A. Shuaib\"],\"articleSection\":[\"Labarai\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/\",\"name\":\"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/03\\\/Bashar.jpeg\",\"datePublished\":\"2026-03-16T13:15:43+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\"},\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/03\\\/Bashar.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/03\\\/Bashar.jpeg\",\"width\":696,\"height\":522},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/03\\\/16\\\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8\",\"name\":\"Rabiu Sani Hassan\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g\",\"caption\":\"Rabiu Sani Hassan\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/web.facebook.com\\\/yaronkirki\",\"official_yaron_kirki143\",\"https:\\\/\\\/x.com\\\/@Rabiusanihassan\",\"@Rabiusanihassan\"],\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/hassanrabiusani\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta - PRNigeria Hausa","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta - PRNigeria Hausa","og_description":"Daga Yushau A. Shuaib Kisan da aka yi wa Malam Bashar Sani, wani babban jami\u2019i a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake \u00a0Maru, wani abin takaici ne da ke nuna irin kalubalen tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya. Duk da cewa \u2018yan uwan shi sun biya sama da naira miliyan 25.7 a matsayin kudin fansa tare [&hellip;]","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_author":"https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","article_published_time":"2026-03-16T13:15:43+00:00","og_image":[{"width":696,"height":522,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/03\/Bashar.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Rabiu Sani Hassan","twitter_card":"summary_large_image","twitter_creator":"@Rabiusanihassan","twitter_misc":{"Written by":"Rabiu Sani Hassan","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/"},"author":{"name":"Rabiu Sani Hassan","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"headline":"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta","datePublished":"2026-03-16T13:15:43+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/"},"wordCount":1087,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/03\/Bashar.jpeg","keywords":["Yushau A. Shuaib"],"articleSection":["Labarai"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/","name":"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/03\/Bashar.jpeg","datePublished":"2026-03-16T13:15:43+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8"},"breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/03\/Bashar.jpeg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/03\/Bashar.jpeg","width":696,"height":522},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/03\/16\/tura-kai-bango-bayan-mutuwar\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"TURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci Matsalolinta"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/ddcbd7faa9958a524c6552574f64e2a8","name":"Rabiu Sani Hassan","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/40189f48112f99e40431a8d80aeedd556953b8edb8b1af0b972b84d72304eda9?s=96&r=g","caption":"Rabiu Sani Hassan"},"sameAs":["https:\/\/web.facebook.com\/yaronkirki","official_yaron_kirki143","https:\/\/x.com\/@Rabiusanihassan","@Rabiusanihassan"],"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/hassanrabiusani\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/03\/Bashar.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/79944","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/454"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=79944"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/79944\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/79945"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=79944"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=79944"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=79944"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=79944"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}