{"id":79980,"date":"2026-04-20T21:57:52","date_gmt":"2026-04-20T20:57:52","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=79980"},"modified":"2026-04-20T21:57:52","modified_gmt":"2026-04-20T20:57:52","slug":"shari-masaraukar-kano-kotu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/","title":{"rendered":"Yadda Shari&#8217;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli"},"content":{"rendered":"<p><strong>Yadda Shari&#8217;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari&#8217;ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammad Sanusi kan wane ne halastaccen Sarkin na Kano.<\/p>\n<p>A wani zaman da ta yi a Abuja, kotun ta \u0199oli ta \u0257age zaman sauraron shari&#8217;ar zuwa ranar 19 ga watan Afrilun 2027, wato kimanin shekara \u0257aya daga yanzu.<\/p>\n<p>A watan Mayun 2024 ne dai Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya rushe tsarin masarautar Kano na lokacin wanda ke da sarakuna biyar ciki har da Sarki Aminu na Kano, bayan sauya dokokin da suka kafa masarautun na jiha.<\/p>\n<p>Tun lokacin ne Sarki Aminu Bayero ke \u0199alubalantar sauye-sauyen inda suka je kotuna daban-daban kafin zuwa kotun \u0199olin da ta \u0257age zaman har na tsawon shekara biyu.<\/p>\n<p>Aminu Babba \u018aan Agundi ne yake jagorantar \u0199arar a madadin \u0253angaren Sarki Aminu Ado Bayero wajen \u0199alubalantar matakin gwamnatin na Kano na rushe masarautun, musamman ma Sarki Aminu.<\/p>\n<p>Abin da ya wakana a kotu<\/p>\n<p>Barista Bashir Yusuf Muhammad, shi ne lauya mai wakiltar Sarki Muhammadu Sanusi II, ya bayyana wa BBC cewa yanayin aikin kotu ne ya sa kotun ta \u0257age shari&#8217;ar zuwa ba\u0257i.<\/p>\n<p>&#8220;Ka san asalin shari&#8217;ar, Aminu Babba \u018aan Agundi ne ya shigar da \u0199ara, yana \u0199alubalantar hukuncin kotun \u0257aukaka \u0199ara wadda ta ce kotun tarayya da ke Kano ba ta da hurumin sauraron \u0199arar tun a farko,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Lauyan ya ce a zaman kotun ne hukumar DSS suka ce sun bayar da bayanansu a ranar 14 ga watan da ake ciki.<\/p>\n<p>&#8220;A \u0199a&#8217;ida lauyoyin Babba \u018aan&#8217;agundi na da kwana 15 domin mayar da martani, amma kwana 5 ne kawai ke tsakani daga ranar da DSS ta yi bayani. Sai suke nemi kotu ta \u0257age shari&#8217;ar domin su samu damar mayar da martani.&#8221;<\/p>\n<p>Barista Bashir ya ce sun yi \u0199o\u0199arin jan hankalin kotu kan cewa lauyoyin sun gabatar da bayani a watan Disamban bara, amma ya ce kotun ta ce doka ce ta ba lauyoyin damar kwana 15.<\/p>\n<p>&#8220;Wannan ne ya sa kotun ta auna yanayin lokacin da take da shi na zama, sai ta \u0257age shari&#8217;ar har zuwa Afrilun ba\u0257i.&#8221;<\/p>\n<p>Za a iya dawo da shari&#8217;ar baya?<\/p>\n<p>Ganin yadda lokacin da aka \u0257auka domin cigaba da sauraron shari&#8217;ar ya \u0257auki hankali, Barista Bashir ya ce kotun \u0199oli na da aikace-aikace da yawa.<\/p>\n<p>&#8220;Ka san damar bayar da lokacinn zama dama ce ta kotu, kuma Kotun \u0198oli na da aikace-aikace da yawa. Mu kanmu mun yi mamaki, kasancewar shari&#8217;ar na da \u0257aukar hankali sosai,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa babu yadda za su yi saboda sun san kotun \u0199olin na da aiki da yawa. &#8220;Ba za ta neman shawarar lauyoyi ba wajen bayar a lokaci,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Sai dai ya ce za su yi yun\u0199urin neman kotun ta \u0199oli ta rage yawan lokacin na cigaba da sauraron shari&#8217;ar.<\/p>\n<p>&#8220;Za mu rubuta a rubuce domin mu nemi idan akwai hali a dawo da shari&#8217;ar baya. lallai akwai bu\u0199atar a kammala shari&#8217;ar nan,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>Wa\u0257anda Babba \u018aan&#8217;agundi ke \u0199ara<\/p>\n<p>Gwamnatin jihar Kano<br \/>\nMajalisar dokokin jihar Kano<br \/>\nOfishin Atoni-Janar na Kano<br \/>\nKwamishinan \u01b4ansanda<br \/>\nHukumar DSS<br \/>\nRundunar civil defence<br \/>\nBabban sufeto-janar na \u01b4ansanda<\/p>\n<p>Yadd rikicin ya samo asali<\/p>\n<p>A watan Mayun shekarar 2024 ne majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta \u0199ir\u0199iri sababbin masarautu ta shekarar 2019.<\/p>\n<p>Majalisar ta bayyana cewa rushe sabuwar dokar na nufin cewa za a koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.<\/p>\n<p>Sabon matakin da majalisar ta \u0257auka ne ya rushe sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da \u0198araye, da Gaya, da Rano.<\/p>\n<p>A lokacin ne kuma majalisar ta gabatar da sabuwar dokar da za ta \u0199ir\u0199iri sabbin sarakuna masu daraja ta biyu.<\/p>\n<p>A sabuwar dokar, gwamnatin Kano ta tsara masarautun kamar haka:<\/p>\n<p>Masarautar Kano: Masarautar Kano ita ce mai daraja ta \u0257aya, inda sauran sarakuna masu daraja ta biyu za su zama \u0199ar\u0199ashin ikon sarkin Kano mai daraja ta \u0257aya. Masarautar mai daraja ta \u0257aya na da iko na kai tsaye da hakiman \u0199ananan hukumomi 36 daga cikin 44 na jihar.<br \/>\nMasarautar Rano: Sarki mai daraja ta biyu na wannan masarauta na da \u0199ananan hukumomi uku wato Rano da Bunkure da Kibiya.<br \/>\nMasarautar \u0198araye: Ita kuma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta \u0199unshi \u0199ananan hukumomi guda biyu na \u0198araye da Rogo.<br \/>\nMasarautar Gaya: Ita ma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta \u0199unshi \u0199ananan hukumomi uku na Gaya da Ajingi da kuma Albasu.<\/p>\n<p>Shari&#8217;o&#8217;i kan rikicin sarautar Kano<\/p>\n<p>A ranar Litinin, 15 ga watan Yuli ne mai shari&#8217;a Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hu\u0257u na Rano, \u0198araye, Bichi da Gaya da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai.<\/p>\n<p>Kotun ta kuma umarci sarakunan biyar da su mi\u0199a duk wasu kaya na sarauta mallakar masarauta ga gwamnatin jiha.<\/p>\n<p>Majalisar dokokin jihar Kano ce dai ta shigar da Aminu Ado Bayero da \u01b4an sanda da sojoji a gaban kotun.<\/p>\n<p>To sai dai kuma kafin hukuncin, babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.<\/p>\n<p>A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari&#8217;a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai ba ne gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yun\u0199uri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.<\/p>\n<p>Mai shari&#8217;a Liman ya ce &#8220;A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta \u0257auka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi&#8221;.<\/p>\n<p>Kotun ta ce &#8220;An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari&#8217;ar suka \u0257auka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba.&#8221;<\/p>\n<p>Bisa dokar ne dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake na\u0257a Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tu\u0253e shi a 2020.<\/p>\n<p>A ranar 23 ga watan na Mayu ne \u0257aya daga cikin masu na\u0257a sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba \u018aan Agundi ya \u0199alubalanci dokar a babbar kotun tarayyar da ke Kano, sannan ya ce za su garzaya kotu na gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Yadda Shari&#8217;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli &nbsp; Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari&#8217;ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammad Sanusi kan wane ne halastaccen Sarkin na Kano. A wani zaman da ta yi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":453,"featured_media":79981,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20098],"tags":[9822,14689,20375,1499],"byline":[],"class_list":["post-79980","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-taska","tag-abba-kabir-yusuf","tag-alhaji-aminu-ado-bayero","tag-kotun-koli","tag-malam-muhammadu-sanusi-ii"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Yadda Shari&#039;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"description\" content=\"Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari&#039;ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki\" \/>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Yadda Shari&#039;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari&#039;ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-04-20T20:57:52+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/aminuabba-da-Sanusi.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"296\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"171\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"garbakubura\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"garbakubura\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"garbakubura\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"headline\":\"Yadda Shari&#8217;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli\",\"datePublished\":\"2026-04-20T20:57:52+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/\"},\"wordCount\":1142,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/aminuabba-da-Sanusi.jpg\",\"keywords\":[\"Abba Kabir Yusuf\",\"Alhaji Aminu Ado Bayero\",\"Kotun Koli\",\"Malam Muhammadu Sanusi II\"],\"articleSection\":[\"Taska\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/\",\"name\":\"Yadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/aminuabba-da-Sanusi.jpg\",\"datePublished\":\"2026-04-20T20:57:52+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"description\":\"Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari'ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/aminuabba-da-Sanusi.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/aminuabba-da-Sanusi.jpg\",\"width\":296,\"height\":171,\"caption\":\"Aminu, Abba da Sanusi\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/20\\\/shari-masaraukar-kano-kotu\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Yadda Shari&#8217;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\",\"name\":\"garbakubura\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"caption\":\"garbakubura\"},\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/garbakubura\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Yadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli - PRNigeria Hausa","description":"Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari'ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Yadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli - PRNigeria Hausa","og_description":"Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari'ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2026-04-20T20:57:52+00:00","og_image":[{"width":296,"height":171,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/aminuabba-da-Sanusi.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"garbakubura","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"garbakubura","Est. reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/"},"author":{"name":"garbakubura","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"headline":"Yadda Shari&#8217;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli","datePublished":"2026-04-20T20:57:52+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/"},"wordCount":1142,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/aminuabba-da-Sanusi.jpg","keywords":["Abba Kabir Yusuf","Alhaji Aminu Ado Bayero","Kotun Koli","Malam Muhammadu Sanusi II"],"articleSection":["Taska"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/","name":"Yadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/aminuabba-da-Sanusi.jpg","datePublished":"2026-04-20T20:57:52+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"description":"Kotun \u0199oli ta dage sauraron shari'ar rikicin masarautar Kano da ya \u0199i ci ya \u0199i cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/aminuabba-da-Sanusi.jpg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/aminuabba-da-Sanusi.jpg","width":296,"height":171,"caption":"Aminu, Abba da Sanusi"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/20\/shari-masaraukar-kano-kotu\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Yadda Shari&#8217;ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta \u0199oli"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450","name":"garbakubura","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","caption":"garbakubura"},"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/garbakubura\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/aminuabba-da-Sanusi.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/79980","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/453"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=79980"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/79980\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/79981"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=79980"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=79980"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=79980"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=79980"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}