{"id":80014,"date":"2026-04-25T21:41:53","date_gmt":"2026-04-25T20:41:53","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=80014"},"modified":"2026-04-25T21:41:53","modified_gmt":"2026-04-25T20:41:53","slug":"bayani-juyin-mulki-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/","title":{"rendered":"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya"},"content":{"rendered":"<p><strong>Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar &#8211; to amma bayan gurfanar da wa\u0257anda ake zargi gaban kotu a wannan mako, a karon farko an fara samun sashihin bayani game da wani gagarumin shirin da aka yi na kawar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.<\/p>\n<p>An shirya aiwatar da juyin mulkin ne a ranar 1 ga watan Oktoban 2025 &#8211; ranar da Najeriya ke bikin cika shekara 65 da samun \u01b4ancin kai daga Birtaniya.<\/p>\n<p>Amma gab da lokacin bikin ne sai aka soke faretin da ak shirya yi, wanda shugaba Tinubu zai halarta &#8211; sai dai gwamnati da kuma sojoji duk sun yi gum da bakinsu game da dalilin hakan.<\/p>\n<p>Sai a watan Janairun 2026 ne hukumomin soji na \u0199asar suka sanar da batun a cikin wata sanarwa da ba ta \u0199unshi cikakken bayani ba, cewa wasu sojoji 16, wa\u0257anda ba a bayyana sunayensu ba za su gurfana a kotun soji kan zargin kitsa juyin mulki &#8211; wanda hakan ya tabbatar da cewa an da\u0199ile yun\u0199urin ham\u0253arar da gwamnati.<\/p>\n<p>Takardun da masu shigar da \u0199ara na gwamnati suka gabatar a Babbar Kotun Tarayya a Abuja, sun bayyana sunayen wa\u0257anda ake zargi, tare da bayyana cewa \u0257aya daga cikin manufofin masu kitsa juyin mulkin shi ne su haifar da husuma a \u0199asar gabanin tuntsurar da gwamnati.<\/p>\n<p>Mutane shida da aka gabatar gaban babbar kotun su ne wa\u0257anda ba za a iya yi wa shari&#8217;a a kotun soji ba &#8211; wasu daga cikinsu fararen hula ne, wani kuma sufeta ne a rundunar \u01b4ansanda sai kuma sauran wa\u0257anda sojoji ne da suka yi ritaya.<\/p>\n<p>Dukkaninsu sun musanta zarge-zarge 13 da aka yi musu, ciki har da zargin cin amanar \u0199asa, da ta&#8217;addanci da kuma halasta ku\u0257a\u0257en haram &#8211; kuma duk da cewa mutanen da aka gabatar a kotun ba su ne jagororin kitsa juyin mulkin ba, amma ya \u0199ara haske kan batun wanda ake zargin ya \u0199unshi mutane daban-daban daga dukkanin hukumomin tsaro na \u0199asar.<\/p>\n<p>Najeriya tana da da\u0257a\u0257\u0257en tarihin yawan faruwar juyin mulki, sai dai \u0199asar ta kasance a \u0199ar\u0199ashin mulkin dimokura\u0257iyya tun daga shekarar 1999.<\/p>\n<p>Akwai \u0199asashen yammacin Afirka da dama da suka fuskanci juyin mulki a shekarun baya-bayan nan, kuma wasu na tsoron kada Najeriya ta bi sahunsu saboda matsin tattalin arzi\u0199i da kuma zargin bada\u0199ala a harkar siyasa.<\/p>\n<p>Wane ne asalin wanda ya kitsa shirin?<\/p>\n<p>Takardun kotu sun bayyana Kanar Mohammed Ma\u2019aji a matsayin babban ginshiki wajen kitsa yunkurin juyin mulkin.<\/p>\n<p>Babu wasu cikakkun bayanai game da mutumin mai shekara 50 a duniya, wanda Musulmi ne da aka haifa a jihar Neja, ya kwashe mafi yawan rayuwarsa ne a yankin Neja-Delta kuma akasarin ayyukansa sun wakana ne a shekarun 2000.<\/p>\n<p>A wannan lokaci ne ayyukan masu tayar da kayar baya na yankin suka kai matuka, lokacin da suke amfani da kananan jiragen ruwa masu gudun gaske wajen kai hare-hare kan cibiyoyin hakar man fetur da kuma yin garkuwa da \u2018yan kasar waje domin neman kudin fansa.<\/p>\n<p>An bayyana cewa a wancan lokacin ne ya kulla alaka ta kut da kut da babban dan kasuwar man fetur kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, wanda ya taka rawa sosai wajen ganin \u2018yan tayar da kayar bayan sun amince su ajiye makamai, lamarin da ya haifar shirin yin afuwa na gwamnati a shekarar 2009.<\/p>\n<p>Ma\u2019aji shi ne ya zama mai tsara wa Sylva matakan tsaro a lokacin da ya yi yunkurin komawa wa\u2019adi na biyu a matsayin gwamna a shekarar 2015, lamarin da bai yi nasara ba, kamar yadda jaridu da dama suka ruwaito.<\/p>\n<p>Ana ganin wannan alaka ce tushen kitsa juyin mulkin da ake zargi.<\/p>\n<p>Daga ina aka samu kudin aiwatar da shirin?<\/p>\n<p>Daya daga cikin jami\u2019an soji masu bincike, wanda ya tattauna da BBC bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba, ya ce a nan ne Timipre Sylva ya taka tasa rawar.<\/p>\n<p>Tsohon gwamnan mai shekara 67 ba ya cikin wadanda aka gurfanar a gaban kotu a wannan mako, amma sunansa na cikin tuhume-tuhume 7 daga cikin 13 &#8211; inda aka rika bayyana cewa \u201cya tsere\u201d a duk inda aka ambaci sunansa.<\/p>\n<p>Sylva ya rike mukamin ministan man fetur a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya kammala mulkinsa a 2023, saboda haka masu gudanar da bincike sun yi amannar cewa yana cikin manyan wadanda suka samar da kudin kitsa juyin mulkin da ake zargi.<\/p>\n<p>Sylva mamba ne na jam\u2019iyyar APC mai mulkin Najeriya sai dai an yi amannar cewa bai goyi bayan takarar shugabancin kasar Bola Tinubu ba a 2023.<\/p>\n<p>Jim kadan bayan soke faretin bikin zagayowar ranar ranar samun \u2018yancin kai, jami\u2019an tsaro sun kai samame a gidan Timipre Sylva da ke Abuja, kuma a wannan lokacin mai magana da yawunsa ya musanta cewa yana da hannu a zargin kitsa juyin mulkin.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa zargin da ake yi wa Sylva da kuma wata takardar izinin kame da kotu ta bayar kansa bisa zargin rashawa bi-ta-da-kullin siyasa ne.<\/p>\n<p>Mai magana da yawun taohon gwamnan ya dage kai da fata cewar Sylva na kasar Birtaniya ne inda yake yin jinya, kuma zai koma Najeriya da zaran ya warware. Sai dai har yanzu bai koma ba.<\/p>\n<p>Da alama an bukaci makudan kudade na sayen kayan aiki da kuma neman goyon baya gabanin shirin tuntsurar da gwamnatin. Ana zargin cewa an vai wa fararen hula da ake zargi da hannu wajen kitsa juyin mulkin kudade &#8211; wadamda suka kama daga naira miliyan 2 zuwa naira miliyan 50 domin gudanar da wasu ayyuka &#8211; inda aka zarge su da cewa ya kamata su san cewa an fitar da kudaden ne da mummunar manufa\u2026don aikin ta\u2019addanci.<\/p>\n<p>Me aka shirya aikatawa a ranar juyin mulkin?<\/p>\n<p>Babu cikakken bayanin abinda aka so aikatawa a cikin takardun da aka gabatar a kotu amma jami\u2019in sona mai bincike ya yi bayani kan yadda mutanen suka kitsa yadda za su yi wa fadar shugaban kasar Najeriya dirar mikiya a ranar 1 ga watan Oktoba.<\/p>\n<p>Fadar na cikin wurare mafiya tsaro a Najeriya &#8211; to amma an ce mutanen da ake zargin sun riga sun gina tsarin tattar bayanan sirri ta hanyar wasu na cikin gida.<\/p>\n<p>Misali, daya daga cikin fararen hula da ake zargi da hannu &#8211; Zekeri Umoru &#8211; ya kasance mai aikin gyaran wuta a fadar shugaban kasar.<\/p>\n<p>Bayan kwace iko, shirin ya tsara yadda za a tsare shugaban kasar da kuma manyan jami\u2019an gwamnati. Jami\u2019in sojin ya ce masu kitsa juyin mulkin sun shirya kashe Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, da shugaban majalisar dattijai Godswill Akpabio da na majalisar wakilai Tajudeen Abbas.<\/p>\n<p>To amma rahotanni sun bayyana cewa shirin nasu ya fada a hannun gwamnati, inda aka samu nasarar kama wasunsu gabanin ranar bikin zagayowar ranar samun \u2018yancin kai.<\/p>\n<p>Amma duk da haka tsoron gudun abin da zai je ya dawo ya sanya sojoji suka soke faretin nasu na ranar samun \u2018yancin kai, sannan aka ci gaba da yin bincike da kuma kame.<\/p>\n<p>Jami\u2019in sojin ya bayyana cewa masu kitsa juyin mulki sun sayo motoci, manya da kanana domin aiwatar da shirin nasu.<\/p>\n<p>An so a yi amfani da motocin ne wajen kaiwa zuwa wasu muhimman wurare, kamar filayen jirgin sama da wasu wuraren.<\/p>\n<p>Dakarun tsaron Najeriya na da bangarori uku &#8211; sojin kasa da na sama da na ruwa.<\/p>\n<p>A tsakanin rundunar sojin akwai bangarori 8 da ke fadin kasar, da kuma dakarun fadar shugaban kasa domin bayar da kariya ga fadar ta Aso Rock.<\/p>\n<p>Daga cikin manyan sojoji 16 da aka kama, 14 sojojin kasa ne wadanda aka karkasa su zuwa wurare daban-daban, sai jami\u2019in sojin ruwa daya da kuma jami\u2019in sojin sama daya.<\/p>\n<p>Me ya sa aka kama malamin addini?<\/p>\n<p>Sani Abdulkadir suna ne da ya sha bamban daga cikin sunayen fararen hula da ake zargi.<\/p>\n<p>Sanannen malami ne daga garin Zariya a jihar Kaduna.<\/p>\n<p>Iyalansa sun bayar da rahoton rashin ganin sa a karshe-karahen shekarar 2025, inda suka rika neman sa har da cigiya a gidajen rediyo.<\/p>\n<p>Sun bayyana cewa ya tafi babban birnin kasar ne domin tantance abin da ya sa aka toshe asusun ajiyarsa na banki. Amma sai bayan watanni ne bayanai suka tabbatar da cewa ana tsare da shi ne.<\/p>\n<p>A ranar Litinin kotu ta bukaci a sake shi sannan a biya shi kudi sama da dala 3,500 a matsayin diyyar take masa hakki sannan kuma aka bukaci hukumomin tsaro su nemi afuwa daga gare shi.<\/p>\n<p>Sai dai duk da haka, a washegarin ranar da kotu ta bayar da umarni , an sake ambato shi a cikin masu hannu a zargin kitsa juyin mulkin sannan kuma aka ci gaba da tsare shi.<\/p>\n<p>Takardun da aka gabatar wa kotu sun bayyana cewa ya karbi kudi kimanin dala 1,500 daga hannun daya daga cikin masu kitsa juyin mulkin.<\/p>\n<p>Jami\u2019in soja mai bincike ya ce ba wai an ba malamin kudi ne domin ya yi wa\u2019azin da zai janyo tarzoma ba, an ba shi ne domin ya yi wa masu kitsa juyin mulki addu\u2019o\u2019in samun nasara.<\/p>\n<p>Sheikh Abdulkadir malami ne mazaunin unguwar Kusfa da ke Zaria &#8211; wurin da ya shahara wajen tarin malamai wadanda kan yi wa mutane addua idan suna bukata, wata al\u2019ada da aka saba gani a arewacin Najeriya.<\/p>\n<p>Ko za a kara kama wasu mutanen da ake zargi?<\/p>\n<p>Akwai yiwuwar hakan, in ji wata majiya da ke kusa da binciken da ake yi.<\/p>\n<p>Wani zuzzurfan bincike da jaridar Premium Times ta Najeriya ta yi kafin yanzu ya lissafo sunayen mutum 40 da ake zargi da hannu, wadanda mafi yawansu sojoji ne.<\/p>\n<p>A ranar Juma\u2019a an sanar da cewa an kaddamar da kotun soji &#8211; inda rahotanni suka ce za a yi wa sojoji sama da 30 shari\u2019a. Sai dai za a yi shari\u2019ar ne a cikin sirri.<\/p>\n<p>Amma ana ci gaba da tambayoyi kan daya daga cikin fararen hula wanda aka ga sunansa a cikin jerin sunayen da ya bulla, amma ba a gan shi a kotu ba, wato sanannen dan fim ka darakta a masana\u2019antar Nollywood, Stanley Amandi, wanda ake wa lakabi da \u201cStan K\u201d.<\/p>\n<p>A watan Janairu kungiyar \u2018yan fim ta Najeriya ta tabbatar wa BBC cewa dan fim din dan asalin Enugu na hannun hukumomi bisa zargin cewa an dauke sa a matsayin mai aikin yada farfaganda na masu kitsa juyin mulkin.<\/p>\n<p>An yi amannar cewa an kama dan fim din ne a watan Satumba.<\/p>\n<p>Majiyar ta shari\u2019a ta ce aikinsa, kamar yadda aka tsara, shi ne zai yi amfani da kafafen yada labarai wajen yada farfagandar neman goyon baya ga masu tsara juyin mulkin.<\/p>\n<p>Kungiyar \u2018yan fim din ta ce ta tuntubi rundunar tsaron farin kaya ta kasar DSS domin ganin yadda za a samar wa dan fim din lauyan da zai kare shi, da kuma barin matarsa da likitansa su gan shi.<\/p>\n<p>To amma hukumar ta ce ba ya hannunta, yana hannun hukumar tattara bayanan sirri ta rundunar sojin kasar.<\/p>\n<p>Hr yanzu an gaza samun yadda za a yi magana sa Amandi domin jin ta bakinsa kan zargin da ake masa.<\/p>\n<p>Yanzu haka an tsare wadanda aka gurfanar gaban Babbar kotun tarayya a hannun rundunar tsaro ta DSS bayan kai su kotun a ranar Laraba, har sai zuwa ranar 27 ga watan Afrilu inda za a saurari bukatar neman beli.<\/p>\n<p>Ya zuwa yanzu bayanan da aka samu game da yunkurin kifar da gwamnatin ya bai wa \u2018yan Najeriya mamaki &#8211; kasar ta fuskanci juyin mulki da dama, amma lokaci na karshe da aka samu juyin mulki shi ne a shekarar 1993 karkashin Janar Sani Abacha.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya &nbsp; An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar &#8211; to amma bayan gurfanar da wa\u0257anda ake zargi gaban kotu a wannan mako, a karon farko an fara samun sashihin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":453,"featured_media":80015,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20098],"tags":[20852,21423,18824],"byline":[],"class_list":["post-80014","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-taska","tag-juyin-mulki","tag-mohammed-aji","tag-timipre-sylva"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"description\" content=\"An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar\" \/>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-04-25T20:41:53+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/Juyin-Mulki.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"686\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"386\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"garbakubura\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"garbakubura\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"garbakubura\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"headline\":\"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya\",\"datePublished\":\"2026-04-25T20:41:53+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/\"},\"wordCount\":1944,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/Juyin-Mulki.jpg\",\"keywords\":[\"Juyin Mulki\",\"Mohammed Ma'aji\",\"Timipre Sylva\"],\"articleSection\":[\"Taska\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/\",\"name\":\"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/Juyin-Mulki.jpg\",\"datePublished\":\"2026-04-25T20:41:53+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"description\":\"An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/Juyin-Mulki.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/04\\\/Juyin-Mulki.jpg\",\"width\":686,\"height\":386,\"caption\":\"Juyin Mulki\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/04\\\/25\\\/bayani-juyin-mulki-najeriya\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\",\"name\":\"garbakubura\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"caption\":\"garbakubura\"},\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/garbakubura\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya - PRNigeria Hausa","description":"An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya - PRNigeria Hausa","og_description":"An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2026-04-25T20:41:53+00:00","og_image":[{"width":686,"height":386,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/Juyin-Mulki.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"garbakubura","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"garbakubura","Est. reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/"},"author":{"name":"garbakubura","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"headline":"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya","datePublished":"2026-04-25T20:41:53+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/"},"wordCount":1944,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/Juyin-Mulki.jpg","keywords":["Juyin Mulki","Mohammed Ma'aji","Timipre Sylva"],"articleSection":["Taska"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/","name":"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/Juyin-Mulki.jpg","datePublished":"2026-04-25T20:41:53+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"description":"An shafe watanni ana jita-jita game da juyin mulkin da ake zargin an kitsa, wanda aka so aiwatarwa a ranar bikin \u01b4ancin kan \u0199asar","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/Juyin-Mulki.jpg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/Juyin-Mulki.jpg","width":686,"height":386,"caption":"Juyin Mulki"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/04\/25\/bayani-juyin-mulki-najeriya\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Cikakken Bayani Game da Kitsa Juyin Mulki a Najeriya"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450","name":"garbakubura","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","caption":"garbakubura"},"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/garbakubura\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/04\/Juyin-Mulki.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80014","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/453"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=80014"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80014\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/80015"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=80014"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=80014"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=80014"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=80014"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}