{"id":80114,"date":"2026-06-13T21:14:28","date_gmt":"2026-06-13T20:14:28","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=80114"},"modified":"2026-06-13T21:14:28","modified_gmt":"2026-06-13T20:14:28","slug":"rabe-rasu-hannun-yanbindiga","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/","title":{"rendered":"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga"},"content":{"rendered":"<p><strong>Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun \u01b4anbindiga a jihar katsina.<\/p>\n<p>Gwamnatin Katsina ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Nasiru Mu&#8217;azu ya fitar, inda ya ce tsohon hafsan ya rasu ne sakamakon ta&#8217;azzarar ciwon siga da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.<\/p>\n<p>Sanarwar ta bayyana cewa duk da \u0199o\u0199arin da gwamnatin jihar tare da jami&#8217;an tsaro suka yi na ganin an ku\u0253utar da shi cikin \u0199oshin lafiya, ba su samu nasarar ceto shi da rai ba.<\/p>\n<p>Mutuwar tasa ta jefa iyalansa da al&#8217;ummar jihar Katsina da ma \u0199asa baki \u0257aya cikin alhini da jimami.<\/p>\n<p>Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya mi\u0199a sa\u0199on ta&#8217;aziyyarsa ga iyalan marigayin tare da bayyana lamarin a matsayin babbar asara.<\/p>\n<p>Ya ce wannan wata alama ce da ke nuna bu\u0199atar a \u0199ara ha\u0257a kai domin tunkarar matsalar tsaro da ke addabar al&#8217;umma.<\/p>\n<p>Yadda aka sace Janar Rabe<\/p>\n<p>A kwanakin baya ne dai \u01b4anbindida suka sace Janar Rabe da matarsa a Katsina, inda suka nuna su a bidiyo suna kira ga hukumomin Najeriya su ceto su.<\/p>\n<p>\u01b3anbindiga sun sace tsohon janar \u0257in tare da maidakinsa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.<\/p>\n<p>Jim ka\u0257an bayan samun rahoton garkuwa da shi ne hukumomi a \u0199asar suka ce suna bakin \u0199o\u0199arinsu wajen ganin yadda za su amso sojan, wanda \u0257an asalin jihar ta Katsina ne amma ya fi yawan zama a Kaduna, kamar yadda mai magana da yawun rundunar sojin Nakeriya Janar Michael Onoja ya sanar.<\/p>\n<p>Katsina na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar \u01b4anbindiga masu satar mutane domin neman ku\u0257in fansa, sai dai a baya-bayan nan lamarin ya yi sau\u0199i bayan matakan da al&#8217;umma da kuma gwamnati ta dauka.<\/p>\n<p>Sai dai ci gaba da irin wannan garkuwa da mutane na nuna \u0199aruwar wannan matsala ta rashin tsaro wadda ta addabi arewa maso yammacin Najeriya.<\/p>\n<p>A baya-bayan nan irin wannan garkuwa da mutane sun faru a wasu makarantu da ke jihohin \u0199asar, lamarin da ya tayar da hankula, kuma har shugaban \u0199asar ya sha walwaahi karbo wadanda aka sace.<\/p>\n<p>A ranar 25 ga watan Disamban 2025 Amurka ta kaddamar da wani hari kan jihar Sokoto mai makwaftaka da Katsina, kan sansanin wasu masu dauke makamai wa\u0257anda aka ce suna da ala\u0199a da \u0199ungiyar IS.<\/p>\n<p>Katsina na daga cikin jihohin da suka fi fama da wannan matsala.<\/p>\n<p>Wane ne Janar Rabe?<\/p>\n<p>Manjo Janar Rabeh Abubakar, wanda ya taba zama mai magana da yawun rundunar sojin kasa ta Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2017, an sace shi daga cikin matorsa a lokacin da yake kan hanyarsa ta shiga Katsina daga Kaduna a ranar Asabar.<\/p>\n<p>A watan Agustan shekarar 2015 ne Abubakar ya kar\u0253i ragamar mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, inda ya maye gurbin Janar Chris Olukolade bayan ritayarsa daga aiki bayan shekara 35.<\/p>\n<p>An haife shi ne a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar 1965. \u018aan asalin \u0199aramar hukumar Batsari ne na jihar Katsina.<\/p>\n<p>Ya yi karatun firamare da sakandare, sanna ya yi digiri a fannin tarihi, sannan ya shiga aikin soja.<\/p>\n<p>Ya fara aikin soja ne a shekarar 1989, inda ya fito da mu\u0199amin laftanal, inda daga nan ya yi aikace-aikace da dama a wurare daban-daban.<\/p>\n<p>Daga cikin mu\u0199aman da ya ri\u0199e akwai kodinetan sashen watsa labarai na hedkwatar aikin soji na musamman a yankin Neja Delta da kwamandan makarantar horar da jami&#8217;an hul\u0257a da jama&#8217;a na rundunar sojin \u0199asa wato NASPRI da ke jihar Legas da babban daraktan hul\u0257a da jama&#8217;a a kamfanin jin da\u0257i da walwalar sojojin \u0199asan Najeriya.<\/p>\n<p>Daga cikin \u0199asashen da ya je samun horo akwai China, inda ya samu horo na musamman a kwalejin horar da manyan hafsoshin tsaron \u0199asar da sauransu.<\/p>\n<p>Najeriya ta yi rashi &#8211; Rundunar tsaro<\/p>\n<p>A sa\u0199on jaje da rundunar tsaron Najeriya ta fitar, ta bayyaa rashin a matsayin babba, inda ta ce za ta \u0199aimi wajen ya\u0199i da matsalar tsaro a \u0199asar baki \u0257aya.<\/p>\n<p>&#8220;Muna mi\u0199 sa\u0199on ta&#8217;aziyya da jaje kan rasuwar abokin aikinmu Manjo Janar Abubakar ga iyalansa da sauran \u01b4an Najeriya baki \u0257aya. A lokacin da yake aiki a matsayin mai magana da yawun rundunar tsaro, ya taimaka matu\u0199a wajen ya\u0199i da matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta.&#8221;<\/p>\n<p>Rundunar ta \u0199ara da cewa jajircewarsa da \u0199o\u0199arinsa wajen tabbatar a zaman lafiya da ha\u0257in kan Najeriya abin koyi ne babba.<\/p>\n<p>Sai dai rundunar ta ce sun yi shiru ne game da sacen shi da aka yi saboda yun\u0199urin da ake yi ne ceto shi, inda jami&#8217;an tsaron Najeriya sun kasance suna ta \u0199o\u0199arin tabbatar da ceto shi cikin \u0199oshin lafiya.<\/p>\n<p>&#8220;Mutuwarsa za ta sa jami&#8217;anmu su \u0199ara \u0199aimi wajen cigaba da aiki ba dare ba rana domin kare martabar \u0199asarmu Najeriya da kuma tabbatar da kariyar al&#8217;ummar \u0199asar baki \u0257aya,&#8221; kamar yadda sanarwar ta nuna.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa, &#8220;muna tabbatar wa \u01b4an Najeriya cewa ba za mu yi \u0199asa a gwiwa ba har sai mun tabbatar da tsaro a \u0199asar, tara da cimma duk wa\u0257anda suke da hannu a matsalolin tsaro.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga &nbsp; A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun \u01b4anbindiga a jihar katsina. Gwamnatin Katsina ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":453,"featured_media":80115,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20098],"tags":[20103,21212,21461],"byline":[],"class_list":["post-80114","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-taska","tag-yan-bindiga","tag-dikko-radda","tag-janar-abubakar-rabe"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.7 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"description\" content=\"A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun\" \/>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-06-13T20:14:28+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/06\/Janar-Rabe.jpeg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"508\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"603\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"garbakubura\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"garbakubura\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"4 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"garbakubura\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"headline\":\"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga\",\"datePublished\":\"2026-06-13T20:14:28+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/\"},\"wordCount\":908,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/06\\\/Janar-Rabe.jpeg\",\"keywords\":[\"'yan bindiga\",\"Dikko Radda\",\"Janar Abubakar Rabe\"],\"articleSection\":[\"Taska\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/\",\"name\":\"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/06\\\/Janar-Rabe.jpeg\",\"datePublished\":\"2026-06-13T20:14:28+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"description\":\"A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/06\\\/Janar-Rabe.jpeg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2026\\\/06\\\/Janar-Rabe.jpeg\",\"width\":508,\"height\":603,\"caption\":\"Janar Rabe\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/13\\\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\",\"name\":\"garbakubura\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"caption\":\"garbakubura\"},\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/garbakubura\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga - PRNigeria Hausa","description":"A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga - PRNigeria Hausa","og_description":"A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2026-06-13T20:14:28+00:00","og_image":[{"width":508,"height":603,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/06\/Janar-Rabe.jpeg","type":"image\/jpeg"}],"author":"garbakubura","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"garbakubura","Est. reading time":"4 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/"},"author":{"name":"garbakubura","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"headline":"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga","datePublished":"2026-06-13T20:14:28+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/"},"wordCount":908,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/06\/Janar-Rabe.jpeg","keywords":["'yan bindiga","Dikko Radda","Janar Abubakar Rabe"],"articleSection":["Taska"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/","name":"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/06\/Janar-Rabe.jpeg","datePublished":"2026-06-13T20:14:28+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"description":"A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ce tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Abubakar Rabe ya rasu a hannun","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/06\/Janar-Rabe.jpeg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/06\/Janar-Rabe.jpeg","width":508,"height":603,"caption":"Janar Rabe"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/13\/rabe-rasu-hannun-yanbindiga\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tarihin Rayuwar Janar Rabe da ya Rasu a Hannun \u01b4an Bindiga"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450","name":"garbakubura","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","caption":"garbakubura"},"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/garbakubura\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2026\/06\/Janar-Rabe.jpeg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80114","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/453"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=80114"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80114\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/80115"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=80114"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=80114"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=80114"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=80114"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}