{"id":80151,"date":"2026-06-25T21:11:07","date_gmt":"2026-06-25T20:11:07","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=80151"},"modified":"2026-06-25T21:11:07","modified_gmt":"2026-06-25T20:11:07","slug":"mutane-tallafawa-addaci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/","title":{"rendered":"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#8217;addaci a Najeriya\u00a0"},"content":{"rendered":"<p><strong>Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#8217;addaci a Najeriya<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta&#8217;adanci a \u0199asar.<\/p>\n<p>Matakin na zuwa ne kwanaki bayan da Amurka ta bayyana sunan wani mutum mazaunin Legas, mai sana&#8217;ar musayar ku\u0257a\u0257en waje a matsayin wanda take zargi da tallafa wa ayyukan ta&#8217;addanci a \u0199asar.<\/p>\n<p>Najeriya ta jima tana fama da \u0199ungiyoyin ta&#8217;addanci masu ala\u0199a da \u0199asashen waje, lamarin da ya sa ake zargin wasu daga ciki da wajen \u0199asar da tallafa wa ayyukan \u01b4anbindigar ta hanyar taimaka musu da hada-ha\u0257ar ku\u0257i da safarar makamai.<\/p>\n<p>Wannan ya sa gwamnatin \u0199asar ta du\u0199ufa domin gano mutanen da ke taimaka wa wa\u0257annan \u0199ungiyoyin ta hanyar taimaka musu da ku\u0257a\u0257e ko wasu kayan aiki.<\/p>\n<p>Kan haka ne gwamnatin \u0199asar ta fitar da sunayen mutum shida da tace tana zargi da \u0257aukar nauyin ta&#8217;addanci a \u0199asar bayan \u0257aukar lokaci tana bincike a kansu.<\/p>\n<p>Su wane ne mutanen?<\/p>\n<p>Kwamitin sanya takunkumai na \u0199asar, \u0199ar\u0199ashin jagorancin shugabar kwamitin, Beatrice Jedy-Agba, ya fitar da sunayen ne bayan tantancewa ta hanyar hukumomin tattara bayanan sirri.<\/p>\n<p>&#8220;Mun fitar da sunayen ne bayan tattara bayanan sirri, da binciken hada-hadar ku\u0257i da tantance bayanai tsakanin hukumomi, wa\u0257anda suka tabbatar da hujjojin zarge-zargen da muke da su a kansu&#8221;, kamar yadda ta bayyana.<\/p>\n<p>Mutanen da ake zargi sun ha\u0257a da:<\/p>\n<p>Mazauni birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, da ake zargi da taimaka wa ayyukan \u0199ungiyar ISWAP reshen Okene, ta hanyar yi wa \u0199ungiyar hada-hadar ku\u0257i da kamfaninsa na canji.<\/p>\n<p>An zarge shi da tura wasu ku\u0257in da suka kai kimanin naira miliyan uku zuwa wani asusu da ake zargi na wani mutum ne \u0257an ISWAP a 2023.<\/p>\n<p>A ranar Laraba ne Amurka ta bayyana sunansa a matsayin wanda ke taimaka wa ta&#8217;addanci a Najeriya.<\/p>\n<p>Ibrahim Yakubu Ogirima<\/p>\n<p>Gwamnati ta zargi mutumin da bayar da kayan aiki da tallafin ku\u0257i da maya\u0199an ISWAP na yankin Kogi.<\/p>\n<p>An zarge shi da aiki da umarnin shugabancin ISWAP, wajen kar\u0253a tare da rarraba ku\u0257i da iyalan mambobin ISWAP da suka mutu, wanda hakan ke taimakawa wajen ci gaba da wanzuwar ayyukan \u0199ungiyar.<\/p>\n<p>Adamu Chiroma<\/p>\n<p>Yana fuskantar zargin hannu a tallafa wa ta&#8217;addanci ta hanyar amfani da kamfanonin musayar ku\u0257a\u0257ensa na waje zuwa wasu mutane masu ala\u0199a da ISWAP.<\/p>\n<p>Gwamnatin ta ce bincikenta ya zargi Chiroma da amfani da kamfanonin canji wajen tura ku\u0257a\u0257e zuwa asusun wasu mutane masu ala\u0199a da \u0199ungiyar ISWAP ta yankin Okene.<\/p>\n<p>Ibrahim Abubakar<\/p>\n<p>An zarge shi da hannu a \u0257aukar nauyin ta&#8217;addanci da kuma kasancewa mamba a \u0199ungiyar ta ISWAP.<\/p>\n<p>Gwamnatin ta ce bincikenta ya gano cewa Ibrahim ya ta\u0253a zama sansanin ISWAP na yankin Tafkin Chadi tsakanin 2015 zuwa 2017.<\/p>\n<p>Binciken ya kuma gano cewa yan taimakawa wajen tura ku\u0257i ga manyan mambobin ISWAP da mutanen da suka yi fice wajen \u0257aukar nauyin \u0199ungiyar.<\/p>\n<p>Abdullahi Umar Usman<\/p>\n<p>Ana zarginsa da samar wa ISWAP rashen Okene tallafin ku\u0257i. Binciken gwamnati ya gano cewa yana amfani da kamfanin musayar ku\u0257insa da aka yi wa rajista a Kano wajen tura ku\u0257a\u0257e ga mambobin ISWAP.<\/p>\n<p>Bayanan hada-hadar ku\u0257i sun nuna yadda ya tura ku\u0257i har naira miliyan 3.5 zuwa asusun bankin Abdulkareem Abdulsamad Ohida, \u0257aya daga cikin manyan mambobin \u0199ungiyar ISWAP reshen Okene.<\/p>\n<p>Babangida Muhammed Adamu Hammajam<\/p>\n<p>Mutum na \u0199arshe cikin jerin sunayen da gwamnatin Najeriya ta fitar a baya-bayan nan, ana zarginsa da hannu wajen hada-hadar ku\u0257a\u0257en da \u0199ungiyar ke gudanar da ayyukanta.<\/p>\n<p>Ana kuma zarginsa samar da ku\u0257i da amfani da su wajen saya wa ISWAP abubuwan da take bu\u0199ata ciki har da sayen na&#8217;urar intanet ta Starlink domin bun\u0199asa sadarwa da ayyukan \u0199ungiyar.<\/p>\n<p>An kuma zarge shi da ala\u0199a da Abdulhamid Muazu, tsohon kakakin Boko-Haram da ya koma ISWAP daga baya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sauran kamfanonin canji uku da aka zarga<\/p>\n<p>Abbal Bako &amp; Sons Bureau De Change Limited.<\/p>\n<p>Nine to Nine BDC.<\/p>\n<p>Generation BDC Limited.<\/p>\n<p>Me ya sa ake yawan zargin \u01b4an canji da taimaka wa ta&#8217;addanci?<\/p>\n<p>Ba wannan ne karon farko da aka kama \u01b4an canji da wasu kamfanonin canji bisa zargin tallafa wa ta&#8217;addanci a Najeriya ba.<\/p>\n<p>Lamarin da ya sa wasu \u01b4an\u0199asar ke mamakin yadda ake zargin \u01b4an canjin da hannu a ayyukan \u0199ungiyoyin masu \u0257auke da makamai a \u0199asar.<\/p>\n<p>To sai dai Dr. Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro a yankin Sahel ya ce wannan ba abin mamaki ba ne, la&#8217;akari da cewa kowace sana&#8217;a a kwai bara-gurbi.<\/p>\n<p>&#8221;Akwai wasu bara-gurbi a cikinsu wa\u0257anda ke ganin kamar ba a sanya idanu a ayyukansu, kasada ce wadda kusan a iya cewa gwamnati ta fahimce ta, tana kuma \u0199o\u0199arin maganceta&#8221;, in ji masanin tsaro.<\/p>\n<p>Martanin \u01b4an canjin<\/p>\n<p>Ha\u0257a\u0257\u0257iyar \u0198ungiyar masu canjin ku\u0257a\u0257en waje ta Najeriya, ABCON ta yi Allah wadai da dukkan ayyukan ta&#8217;addanci da na masu tallafa musu.<\/p>\n<p>Cikin wata sanar da \u0199ungiyar ta fitar, ta jaddada cewa takunkuman da gwamnati ta sanya wa wa\u0257ancan kamfanoni ya shafi \u0257ai\u0257aikun mutane da kamfanonin da aka ambata ne, ba duka mambobi da kamfanonin \u0199ungiyar ba.<\/p>\n<p>ABCON ta kuma ce za ta \u0257auki matakan da\u0199ile amfani da harkar canjin ku\u0257in waje domin tallafa wa ta&#8217;addanci.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta ce za ta ri\u0199a amfani da wasu dabaru da suka ha\u0257a da sanin abokin ciniki kafin tura masa ko canja masa ku\u0257i.<\/p>\n<p>Da kuma kai rahoton musayar ku\u0257in da ba a yarda da shi ba, da shirya tarukan \u0199ara wa juna sani da kuma bai wa hukumomin gwamnati ha\u0257in kai.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#8217;addaci a Najeriya &nbsp; Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta&#8217;adanci a \u0199asar. Matakin na zuwa ne kwanaki bayan da Amurka ta bayyana sunan wani mutum mazaunin Legas, mai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":453,"featured_media":73150,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20098],"tags":[20251,21483],"byline":[],"class_list":["post-80151","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-taska","tag-yan-addan-iswap","tag-canji"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.7 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#039;addaci a Najeriya\u00a0 - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"description\" content=\"Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta&#039;adanci a \u0199asar.\" \/>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#039;addaci a Najeriya\u00a0 - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta&#039;adanci a \u0199asar.\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-06-25T20:11:07+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/01\/iswap-gashigar.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"500\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"281\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"garbakubura\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"garbakubura\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"5 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"garbakubura\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"headline\":\"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#8217;addaci a Najeriya\u00a0\",\"datePublished\":\"2026-06-25T20:11:07+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/\"},\"wordCount\":981,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/01\\\/iswap-gashigar.jpg\",\"keywords\":[\"'Yan Ta'addan ISWAP\",\"\u01b3an Canji\"],\"articleSection\":[\"Taska\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/\",\"name\":\"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta'addaci a Najeriya\u00a0 - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/01\\\/iswap-gashigar.jpg\",\"datePublished\":\"2026-06-25T20:11:07+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"description\":\"Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta'adanci a \u0199asar.\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/01\\\/iswap-gashigar.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2023\\\/01\\\/iswap-gashigar.jpg\",\"width\":500,\"height\":281},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/06\\\/25\\\/mutane-tallafawa-addaci\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#8217;addaci a Najeriya\u00a0\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\",\"name\":\"garbakubura\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"caption\":\"garbakubura\"},\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/garbakubura\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta'addaci a Najeriya\u00a0 - PRNigeria Hausa","description":"Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta'adanci a \u0199asar.","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta'addaci a Najeriya\u00a0 - PRNigeria Hausa","og_description":"Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta'adanci a \u0199asar.","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2026-06-25T20:11:07+00:00","og_image":[{"width":500,"height":281,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/01\/iswap-gashigar.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"garbakubura","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"garbakubura","Est. reading time":"5 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/"},"author":{"name":"garbakubura","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"headline":"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#8217;addaci a Najeriya\u00a0","datePublished":"2026-06-25T20:11:07+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/"},"wordCount":981,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/01\/iswap-gashigar.jpg","keywords":["'Yan Ta'addan ISWAP","\u01b3an Canji"],"articleSection":["Taska"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/","name":"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta'addaci a Najeriya\u00a0 - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/01\/iswap-gashigar.jpg","datePublished":"2026-06-25T20:11:07+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"description":"Gwamnatin Najeriya ta bayana sunayen wasu mutum shida da kamfanonin canji uku da take zargi da tallafa wa ayyukan ta'adanci a \u0199asar.","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/01\/iswap-gashigar.jpg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/01\/iswap-gashigar.jpg","width":500,"height":281},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/06\/25\/mutane-tallafawa-addaci\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta&#8217;addaci a Najeriya\u00a0"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450","name":"garbakubura","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","caption":"garbakubura"},"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/garbakubura\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2023\/01\/iswap-gashigar.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80151","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/453"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=80151"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80151\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/73150"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=80151"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=80151"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=80151"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=80151"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}