{"id":80250,"date":"2026-08-06T20:38:54","date_gmt":"2026-08-06T19:38:54","guid":{"rendered":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?p=80250"},"modified":"2026-08-06T20:38:54","modified_gmt":"2026-08-06T19:38:54","slug":"rufe-asusun-gwamnatin-osun","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/","title":{"rendered":"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?"},"content":{"rendered":"<p><strong>Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun, har yanzu cece-kucen da suka biyo bayan matakin ba su lafa ba.<\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Osun ta nuna adawa mai \u0199arfi da matakin da hukumar EFCCn ta \u0257auka na rufe asusunta bisa zargin wasu kura-kuran ku\u0257i.<\/p>\n<p>Gwamnatin Gwamna Ademola Adeleke ta \u0199alubalanci EFCC da ta bayyana dokar da ta yi amfani da ita wajen \u0257aukar matakin, tana mai cewa dole ne hukumar ta nuna yadda hukuncin da ta yanke ya yi daidai da dokokin Najeriya da kuma dokar da ta kafa hukumar.<\/p>\n<p>Mene ne ainihin abin da ya faru?<\/p>\n<p>A ranar 5 ga watan Agustan 2026, Hukumar Ya\u0199i da Cin Hanci da Rashawa da Yi wa Tattalin Arziki Ta&#8217;annati (EFCC) ta sanar da cewa ta sanya umarnin hana cire ku\u0257i (Post No Debit Order) kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun.<\/p>\n<p>Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, inda ta ce an \u0257auki wannan mataki ne a matsayin wani \u0253angare na binciken da take gudanarwa kan harkokin ku\u0257a\u0257en jihar.<\/p>\n<p>Sai dai Gwamnatin Jihar Osun ta yi watsi da zarge-zargen da EFCC ta yi mata, tana mai jaddada cewa ba ta aikata wani laifi ba, tare da tambayar dokar da hukumar ta dogara da itawajen \u0257aukar wannan mataki.<\/p>\n<p>Masu sukar matakin da dama, tare da Gwamnatin Jihar Osun, sun yi ikirarin cewa matakin EFCC yana da nasaba da siyasa.<\/p>\n<p>Gwamna Ademola Adeleke, wanda a baya-bayan nan ya sauya sheka daga Jam&#8217;iyyar PDP zuwa Jam&#8217;iyyar Accord Party, ya zargi hukumar da nuna goyon baya ga wasu mutane masu ala\u0199a da jam&#8217;iyyar APC mai mulki domin kawo cikas ga \u0199o\u0199arinsa na sake lashe za\u0253e.<\/p>\n<p>Adeleke ya jaddada cewa ana sa ran EFCC za ta gudanar da ayyukanta ba tare da nuna bambancin siyasa ba, kuma bai kamata ta bari siyasa ya yi tasiri kan yadda take sauke nauyin da doka ta \u0257ora mata ba.<\/p>\n<p>Me dokar Najeriya ta ce kan matakin na EFCC?<\/p>\n<p>Hukumar EFCC ta sanya wani umarni na &#8220;hana cire ku\u0257i&#8221; (Post No Debit Order) kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun, matakin da ya haifar da muhawara da suka daga masu sa ido kan harkokin siyasa da masana shari&#8217;a da sauran masu ruwa da tsaki.<\/p>\n<p>Masu sukar matakin sun rika aza ayar tambaya kan lokacin da aka \u0257auke shi, suna mai nuni da cewa an yi hakan ne kwanaki ka\u0257an kafin za\u0253en gwamnan jihar da ke tafe nan da wasu makonni.<\/p>\n<p>Da dama sun bayyana cewa lamarin ya \u0199ara haifar da damuwa kan yiwuwar akwai manufar siyasa a cikinsa, duk da cewa EFCC ta dage cewa matakan da take \u0257auka suna da ala\u0199a ne kawai da nauyin da doka ta \u0257ora mata na binciken zarge-zargen laifuffukan ku\u0257i.<\/p>\n<p>A yayin da cece-kucen ke ci gaba, an fara tayar da muhimman tambayoyi kan wace doka EFCC ta dogara da ita wajen \u0257aukar wannan mataki da hanyoyin da doka ta tanada kafin a sanya umarnin hana cire ku\u0257i daga asusu, da kuma ko irin wannan iko na iya shafar asusun gwamnatin jiha.<\/p>\n<p>BBC ta yi duba kan muhimman bayanan da suka shafi lamarin da hujjojin da \u0253angarorin biyu ke gabatarwa, da kuma abin da masana shari&#8217;a da masu sharhi kan harkokin jama&#8217;a ke cewa game da sahihancin matakin EFCC a \u0199ar\u0199ashin kundin tsarin mulkin Najeriya.<\/p>\n<p>Mene ne &#8216;rufe asusun banki&#8217; kuma ya halasta?<\/p>\n<p>Umarnin hana cire ku\u0257i (Post No Debit Order) wani takunkumi ne da ake sanyawa kan asusun banki wanda ke hana cire ku\u0257i ko tura su zuwa wani asusu har sai an janye umarnin.<\/p>\n<p>Da yake magana da BBC, Barista Joe Onyeabor, lauya mai zaman kansa da ke zaune a Jihar Enugu kuma tsohon jami&#8217;in hul\u0257a da jama&#8217;a na \u0198ungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) a jihar, ya ce Dokar EFCC ta bai wa hukumar ikon neman a sanya umarnin hana cire ku\u0257i kan asusun banki yayin da take gudanar da bincike kan zargin laifuffukan ku\u0257i.<\/p>\n<p>A cewarsa, duk da haka, wajibi ne hukumar ta bi matakan shari&#8217;a da suka dace kafin ta \u0257auki irin wannan mataki, ciki har da samun izinin kotu da ake bu\u0199ata.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa Dokar EFCC ba ta bayyana \u0199arara ko za a iya sanya irin wannan umarni kan asusun bankunan gwamnatin jiha ba.<\/p>\n<p>A ra&#8217;ayinsa, dokar ta fi magana ne kan asusun wani &#8220;mutum&#8221;, kuma ba ta fito fili ta tanadi rufe asusun bankunan gwamnatin jiha ba.<\/p>\n<p>Kodayake ya amince cewa EFCC na iya fassara kalmar &#8220;mutum&#8221; ta yadda za ta ha\u0257a da gwamnatin jiha, Onyeabor ya ce sahihancin irin wannan fassara abu ne da a \u0199arshe kotu ce za ta yanke hukunci a kansa.<\/p>\n<p>Zuwa wane lokaci doka ta bai wa EFCC damar rufe asusun banki?<\/p>\n<p>A cewar kakakin EFCC, Dele Oyewale, hukumar ya\u0199i da cin hancin na da ikon rufe asusun banki yayin gudanar da bincike, kuma za ta iya ci gaba da sanya irin wannan takunkumi fiye da sa&#8217;o&#8217;i 72, ko da akwai umarnin kotu ko babu.<\/p>\n<p>Da yake magana da BBC, Oyewale ya ce matakan da hukumar ke \u0257auka suna bisa dokar binciken laifuffukan ku\u0257i da kuma hana motsa ku\u0257a\u0257en da ake zargin suna da ala\u0199a da haramtattun ayyuka.<\/p>\n<p>Lokacin da aka tambaye shi abin da zai faru bayan cikar sa&#8217;o&#8217;i 72 \u0257in, Oyewale ya \u0199i bayar da cikakken bayani.<\/p>\n<p>Abin da ya sa muka rufe asusun gwamnatin jihar Osun &#8211; EFCC<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da EFCC ta fitar, ta bayyana dalilan da suka sa ta sanya umarnin hana cire ku\u0257i (Post No Debit Order) kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun, tana mai cewa tana binciken jihar tun daga watan Maris na shekarar 2026.<\/p>\n<p>Hukumar ta yi zargin cewa ta gano wasu kura-kurai a yadda aka sarrafa ku\u0257a\u0257en gwamnatin jihar, ciki har da ku\u0257a\u0257en Asusun Muhalli (Ecology Fund) da Asusun Tallafi (Intervention Fund) da kuma asusun da jihar ke kar\u0253ar rabon ku\u0257a\u0257e daga Kwamitin Raba Ku\u0257a\u0257en Tarayya (FAAC).<\/p>\n<p>A cewar hukumar, ma&#8217;amalolin da take bincike sun shafi kusan naira biliyan 11.<\/p>\n<p>Da take bayani kan dalilin rufe asusun, EFCC ta ce kasancewar binciken ka\u0257ai bai isa ya sa ta sanya umarnin hana cire ku\u0257i ba.<\/p>\n<p>Sai dai ta ce ta lura da wasu motsa ku\u0257a\u0257e da take ganin suna da alamar tuhuma daga asusun da abin ya shafa, wa\u0257anda aka fara tun ranar 2 ga watan Agustan 2026.<\/p>\n<p>Gwamnatin Osun ta musanta \u0253arnatar da naira biliyan 11<\/p>\n<p>Da take mayar da martani ga zarge-zargen na EFCC, gwamnatin Jihar ta musanta aikata wani laifi tare da yin watsi da ikirarin cewa an wawure naira biliyan 11, tana mai bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe.<\/p>\n<p>Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Wayar da Kan Jama&#8217;a, Oluomo Kolapo Alimi, ya fitar ya bayyana zarge-zargen a matsayin &#8220;\u0199o\u0199arin da ya gaza na kare wani matakin da ya sa\u0253a wa doka ta hanyar jingina shi da zarge-zarge marasa tushe.&#8221;<\/p>\n<p>Ya kuma yi zargin cewa rufe asusun bankunan jihar na da manufar siyasa, yana mai cewa an \u0257auki matakin ne bisa bu\u0199atar tsohon gwamna Gboyega Oyetola domin hana gwamnatin jihar biyan tallafin rage ra<\/p>\n<p>\u0257a\u0257in halin matsin tattalin arziki da ta yi wa ma&#8217;aikata al\u0199awari.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ? &nbsp; Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan asusun bankunan Gwamnatin Jihar Osun, har yanzu cece-kucen da suka biyo bayan matakin ba su lafa ba. [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":453,"featured_media":75405,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_feature_clip_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2},"jetpack_post_was_ever_published":false},"categories":[20115],"tags":[21513,165],"byline":[],"class_list":["post-80250","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-ademola-adeleke","tag-efcc"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v28.1 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ? - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"description\" content=\"Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan\" \/>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ? - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-08-06T19:38:54+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2024\/07\/ademola-adeleke.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1350\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"1335\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"garbakubura\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"garbakubura\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"garbakubura\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"headline\":\"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?\",\"datePublished\":\"2026-08-06T19:38:54+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/\"},\"wordCount\":1282,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2024\\\/07\\\/ademola-adeleke.jpg\",\"keywords\":[\"Ademola Adeleke\",\"efcc\"],\"articleSection\":[\"Labarai\"],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/\",\"name\":\"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ? - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2024\\\/07\\\/ademola-adeleke.jpg\",\"datePublished\":\"2026-08-06T19:38:54+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\"},\"description\":\"Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/#primaryimage\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2024\\\/07\\\/ademola-adeleke.jpg\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/wp-content\\\/uploads\\\/sites\\\/3\\\/2024\\\/07\\\/ademola-adeleke.jpg\",\"width\":1350,\"height\":1335},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2026\\\/08\\\/06\\\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450\",\"name\":\"garbakubura\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g\",\"caption\":\"garbakubura\"},\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/garbakubura\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ? - PRNigeria Hausa","description":"Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ? - PRNigeria Hausa","og_description":"Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2026-08-06T19:38:54+00:00","og_image":[{"width":1350,"height":1335,"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2024\/07\/ademola-adeleke.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"garbakubura","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"garbakubura","Est. reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/"},"author":{"name":"garbakubura","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"headline":"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?","datePublished":"2026-08-06T19:38:54+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/"},"wordCount":1282,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2024\/07\/ademola-adeleke.jpg","keywords":["Ademola Adeleke","efcc"],"articleSection":["Labarai"],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/","name":"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ? - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2024\/07\/ademola-adeleke.jpg","datePublished":"2026-08-06T19:38:54+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450"},"description":"Kodayake an ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar EFCC, mai yai da cin hanci ta cire takunkumin da ta sanya kan","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/#primaryimage","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2024\/07\/ademola-adeleke.jpg","contentUrl":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2024\/07\/ademola-adeleke.jpg","width":1350,"height":1335},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2026\/08\/06\/rufe-asusun-gwamnatin-osun\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Mene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/14efdb4a99818511db4e5c5aea6b9450","name":"garbakubura","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/a87591c4213ea1bfb76b1d51935503f4749212002b9b0cf68b065366e9acf130?s=96&r=g","caption":"garbakubura"},"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/garbakubura\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-content\/uploads\/sites\/3\/2024\/07\/ademola-adeleke.jpg","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80250","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/453"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=80250"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/80250\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/75405"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=80250"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=80250"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=80250"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=80250"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}