{"id":9759,"date":"2022-02-16T12:39:53","date_gmt":"2022-02-16T12:39:53","guid":{"rendered":"https:\/\/hausa.arewaagenda.com\/?p=9759"},"modified":"2022-02-16T12:39:53","modified_gmt":"2022-02-16T12:39:53","slug":"karancin-fetur-matsaloli","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/","title":{"rendered":"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#8216;Yan Najeriya Matsaloli 5"},"content":{"rendered":"<p><strong>Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#8216;Yan Najeriya Matsaloli 5<\/strong><\/p>\n<p>An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da ya dinga lalata ababen hawan mutane, zuwa samun dogwayen layuka a gidajen mai da kuma sayen man da matu\u0199ar tsada.<\/p>\n<p>Hukumomi dai tuni suka yi bayanin dalilan da suka sa aka samu ya\u0257uwar gur\u0253atacen man, wanda zuwa yanzu an dakatar da sayar da shi.<\/p>\n<p>Amma har yanzu ba su bayar da wani bayani mai gamsarwa na dalilin da ya sa man yake wahala ba.<\/p>\n<p>Sai dai kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce wannan rashin man da ake fama da shi a yanzu ya samu ne saboda killace miliyoyin litocin gurbataccen man da ya yadu a kasuwa.<\/p>\n<p>BBC ta tambayi masu bin shafukanta na intanet kan su bayyana halin da arancin an fetur din ya saka su a ciki a yakuna daban-daban na Najeriya.<\/p>\n<p>Kuma daga wallafa hakan a ranar Talata an samu bayanai daga kusan mutum 200 da suka bayar da labaran irin matsalolin da \u0199arancin man fetur ya jawo wa \u01b4an Najeriya.<\/p>\n<p>Bayan bin diddigin bayanan da aka turo, mun gano manyan matsaloli biyar da \u0199arancin man ya jawo wa yan Najeriya.<\/p>\n<p>1. Cunkoso a titunan da ke kusa da gidajen mai<br \/>\nLayukan a gidajen mai sun yi tsawo fiye da yadda aka saba gani a baya-bayan nan a manyan biranen Najeriya da suka ha\u0257a da Abuja da Lagos, amma duk da haka gidajen mai \u0199a\u0257an ne ke sayar da fetur din.<\/p>\n<p>A manyan birane irin su Abuja mazauna unguwannin da suke ma\u0199wabtaka da gidajen mai na ganin bone, kamar yadda muka samu bayanai daga mutane.<\/p>\n<p>A misali babban titin Murtala Muhammad Way na hanyar Kubwa wanda ke \u0257auke da manyan gidajen mai da dama, ya kan cushe da cunkoso saboda motocin da ke kan layuka.<\/p>\n<p>Hakan yana jawo damuwa da matsalar \u0253ata lokaci ga ma wa\u0257anda ba man za su saya ba.<\/p>\n<p>Ga abin da wasu ke cewa:<\/p>\n<p>2. \u0198arin ku\u0257in abin hawa da tsadar wasu abubuwan<\/p>\n<p>Wata matsala ta biyu da al&#8217;umma ke kokawa a kanta ita ce ta yadda masu ababen hawa suka \u0199ara farashi.<\/p>\n<p>A wasu wuraren ma ba farashin abin hawa ne kawai ya yi tashin gwauron zabi ba, har da na wasu abubuwan yau da kullum, kamar dai yadda wasu suka shaida mana.<\/p>\n<p>Ga abin da wasu masu bin shafukanmu suka aiko mana:<\/p>\n<p>3. Yini da kwana a layi<br \/>\nBabban tashin hankalin da \u0199arancin rashin mai ya jawo wa \u01b4an Najeriya shi ne shafe lokaci da suke yi a gidajen man.<\/p>\n<p>A wasu lokutan ma bayan mutum ya yini ya kwana, da zarar layi ya kusa zuwa kansa sai a ce man ya \u0199are.<\/p>\n<p>Wannan lamari na matu\u0199ar tunzura mutane. Ga abin da wasu da dama ke cewa.<\/p>\n<p>4. Tsadar man fetur &#8211; Ko da ku\u0257inka sai da rabonka<\/p>\n<p>Lamarin man fetur ya zama ko da ku\u0257inka sai da rabonka. Tadarsa ta yi yawa ta kai intaha kamar yadda mutane da dama suke kokawa.<\/p>\n<p>A wasu wuraren ma sai dai a sayi mai a hannun \u01b4an bumburutu, wadanda suke nunka kudin kowace lita sau uku ko hu\u0257u kan yadda aka saba saya.<\/p>\n<p>Ga bain da wasu suka shaida mana:<\/p>\n<p>5. Dambe da zage-zage<\/p>\n<p>Wannan shi ne abu mafi \u0253ata rai dangane da matsalar \u0199arancin man.<\/p>\n<p>Wasu gidajen man sun zma kamar filin dambe da kokawa duba da yadda fa\u0257a ke rincabewa tsakanin masu saye da ke kan layi, sakamakon musun na riga ka, ko na ka sha gaba na.<\/p>\n<p>Rabon fa\u0257a ya zama shi ne babban abin da aka fi mayar da hankali a kai a wasu gidajen man. Har ta kai wasu gidajen kan rufe su dakatar da ba da man har sai komai ya lafa.<\/p>\n<p>Matashiya<br \/>\nNajeriya ita ce \u0199asar da ta fi kowacce arzi\u0199in man fetur a Afirka, sai dai an shafe gwaman shekaru tana fama da samun matsalar \u0199arancin man fetur akai-akai.<\/p>\n<p>Hakan ya samo asali ne kan rashin matatun man fetur da ke cikin hayyancinsu a \u0199asar.<\/p>\n<p>Wannan ne dalilin da ya sa a dole \u0199asar ke sayo tataccen man fetur daga \u0199asashen wajen da take sayar musu da \u0257anyen.<\/p>\n<p>Batun shirin gwamnati na janye bayar da tallafin mai yana yawan jawo tarna\u0199i a wajen samar da man.<\/p>\n<p>Amma kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce wannan rashin man da ake fama da shi a yanzu ya samu ne saboda killace miliyoyin litocin gurbataccen man da ya yadu a kasuwa.<\/p>\n<p>A yanzu NNPC ya ce yana shirin samar da lita biliyan 2.3 na fetur a fadin \u0199asar &#8211; kuma cibiyoyin NNPC \u0257in za su fara rarraba man ba dare ba rana a fa din \u0199asar don samar da sau\u0199i.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#8216;Yan Najeriya Matsaloli 5 An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da ya dinga lalata ababen hawan mutane, zuwa samun dogwayen layuka a gidajen mai da kuma sayen man da matu\u0199ar tsada. Hukumomi dai tuni [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":2620,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20098],"tags":[20145,20146,927],"byline":[],"class_list":["post-9759","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-taska","tag-yan-najeriya","tag-man-fetur","tag-nnpc"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#039;Yan Najeriya Matsaloli 5 - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"description\" content=\"An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da\" \/>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#039;Yan Najeriya Matsaloli 5 - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2022-02-16T12:39:53+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Web Engineer\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Web Engineer\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"4 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"Web Engineer\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/83f574a943a8093187e906308f785266\"},\"headline\":\"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#8216;Yan Najeriya Matsaloli 5\",\"datePublished\":\"2022-02-16T12:39:53+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/\"},\"wordCount\":805,\"commentCount\":0,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"\",\"keywords\":[\"'Yan najeriya\",\"man fetur\",\"NNPC\"],\"articleSection\":[\"Taska\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/\",\"name\":\"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa 'Yan Najeriya Matsaloli 5 - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"\",\"datePublished\":\"2022-02-16T12:39:53+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/83f574a943a8093187e906308f785266\"},\"description\":\"An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#primaryimage\",\"url\":\"\",\"contentUrl\":\"\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/16\\\/karancin-fetur-matsaloli\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#8216;Yan Najeriya Matsaloli 5\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/83f574a943a8093187e906308f785266\",\"name\":\"Web Engineer\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g\",\"caption\":\"Web Engineer\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/deborian.com\\\/\"],\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/adebo\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa 'Yan Najeriya Matsaloli 5 - PRNigeria Hausa","description":"An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa 'Yan Najeriya Matsaloli 5 - PRNigeria Hausa","og_description":"An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2022-02-16T12:39:53+00:00","author":"Web Engineer","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Web Engineer","Est. reading time":"4 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/"},"author":{"name":"Web Engineer","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/83f574a943a8093187e906308f785266"},"headline":"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#8216;Yan Najeriya Matsaloli 5","datePublished":"2022-02-16T12:39:53+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/"},"wordCount":805,"commentCount":0,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"","keywords":["'Yan najeriya","man fetur","NNPC"],"articleSection":["Taska"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/","name":"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa 'Yan Najeriya Matsaloli 5 - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"","datePublished":"2022-02-16T12:39:53+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/83f574a943a8093187e906308f785266"},"description":"An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Najeriya, kama daga bazuwar wanigur\u0253ataccen man da","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#primaryimage","url":"","contentUrl":""},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/16\/karancin-fetur-matsaloli\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Yadda Karancin Man Fetur ya Jawo wa &#8216;Yan Najeriya Matsaloli 5"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/83f574a943a8093187e906308f785266","name":"Web Engineer","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g","caption":"Web Engineer"},"sameAs":["https:\/\/deborian.com\/"],"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/adebo\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9759","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9759"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9759\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9759"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9759"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9759"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=9759"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}