{"id":9777,"date":"2022-02-17T12:19:19","date_gmt":"2022-02-17T12:19:19","guid":{"rendered":"https:\/\/hausa.arewaagenda.com\/?p=9777"},"modified":"2022-02-17T12:19:19","modified_gmt":"2022-02-17T12:19:19","slug":"haramta-bukukuwa-aure-adamawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/","title":{"rendered":"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure"},"content":{"rendered":"<p><strong>Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure<\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta dukkanin bukukuwa da ake yi kafin da kuma bayan \u0257aurin aure a \u0199aramar hukumar ne don \u0199o\u0199rin samar da iyali na gari.<\/p>\n<p>A baya-bayan nan ne aka \u0257auki wannan a \u0199aramar hukumar, wanda shugaban majalisar Ahmadu Liman Aminu ya ce an yi hakan ne domin samar wa matasa masu niyyar aure sau\u0199i da kuma samar da zuri&#8217;a ta gari ga matasa da ke auren.<\/p>\n<p>Daga yanzu dai irin wa\u0257annan ka\u0257e-ka\u0257e da a baya aka saba yi yayin bukukuwan aure sun zo \u0199arshe, amma fa idan matakin dakatar da su \u0257in ya fara aiki kamar yadda majalisar harkokin addinin Musulunci ta karamar hukumar Mayo Belwa take bu\u0199ata.<\/p>\n<p>Malam Ahmadu Liman Aminu ya bayyana wa BBC dalilin daukar wannan matakin na dakatar da bukukuwa da aka saba yi kafun da kuma bayan aure.<\/p>\n<p>&#8220;Saboda ganin wahalhalun da al&#8217;ummarmu suke sha a yayin wa\u0257annan bukukuwa na aure da kuma yawan matasa da ke jibge da ba su yi aure ba, saboda dokokin da ya kamata a bi su a yayin \u0257aura auren ma an bar su.<\/p>\n<p>&#8220;Wa\u0257annan dalilai ne suka sa ake haifar yaran da ba da tarbiyya wa\u0257anda ke zame mana tashin hankali a \u0199asa.<\/p>\n<p>To ko wa\u0257anne irin bukukuwa ne aka haramta?<\/p>\n<p>An haramta tarukan liyafa irin su Cocktail Party da \u0198auyawa Day da Luncheon da Fulani Day da Budar Kai da ake gauraya tsakanin maza da mata.<\/p>\n<p>Ta yaya za su tabbatar da an bi dokar?<\/p>\n<p>Malam Ahmadu ya ce matakin da za su \u0257auka a kan wanda duk ya \u0199i bin dokar shi ne a \u0199aurace wa mutum.<\/p>\n<p>&#8220;Idan ka \u0199i bin dokar to matakin da muka \u0257auka na \u0199aurace maka ne, idan za ka yi \u0257aurin aure ko suna duk ba za ka ganmu ba.<\/p>\n<p>&#8220;Ko rasuwa aka yi maka za mu \u0199aurace ba za a je jana&#8217;izarka, wannan shi ne kawai matakin da muka \u0257auka.&#8221;<\/p>\n<p>Wasu \u0199arin matakan da aka \u0257auka<\/p>\n<p>Har&#8217;ilayau majalisar ta kuma \u0199ayyade kayan aure zuwa akwati biyu kacal da za su \u0199unshi atamfa bakwai da takalma uku da hijabai uku da gyale uku da da \u01b4an kunne uku da warworo uku da kayan kwalliya iya gwargwado.<\/p>\n<p>Majalisar ta haramta kar\u0253ar ko wane irin ku\u0257i idan ba na sadaki ba, sannan ta hana yin kayan uwa da na uba da na dangi.<\/p>\n<p>Majalisar ta kuma kafa wata cibiya da za ta ri\u0199a yi wa wa\u0257anda ke da niyyar aure lakca kan hakkokin da suka rataya a wuyansu.<\/p>\n<p>Me masu niyyar aure ke cewa?<\/p>\n<p>Salihu Adamu na BBC ya tattauna da wasu da ke sa ran zama ango da amarya a \u0199arshen wannan makon kan yadda suka ji da wannan matakin.<\/p>\n<p>Wani da muka sakaya sunansa ya ce: &#8220;Idan ka ce za a ka yi biki sai ka duba, za ka \u0257auko hayar mai ki\u0257a da rumfuna wata\u0199ila ma sai a gama bikin ba ka samu ku\u0257in da za ka biya wa\u0257annan abubuwa ba.<\/p>\n<p>&#8220;Don haka ni kam abin ya zo min yadda nake bu\u0199ata.<\/p>\n<p>Ita ma wata mai shirin zama amarya ta ce &#8220;matakin da aka \u0257auka ya yi kyau, dama bidi&#8217;o&#8217;in ba su da wani amfani.&#8221;<\/p>\n<p>Da Salihu ya tambaye ta ko yaya za ta yi da \u0199awayenta da suka shirya wata\u0199ila don ra\u0199ashewa a bikin?<\/p>\n<p>Sai ta ce: &#8220;Na gaya musu ni dama ba na wa\u0257annan abubuwa.&#8221;<\/p>\n<p>Wannan matakin na zuwa ne shekara \u0257aya bayan da \u0199aramar hukumar Gumel da ke jihar Jigawa ta dauki makamancinsa inda ta \u0199ayyade naira 100,000 a matsayin ku\u0257in kayan lefe.<\/p>\n<p>Sau da dama dai malaman addinin Islama na nuna bu\u0199atar soke wasu bukukuwa da ake yi yayin aure musamman wa\u0257anda suke ganin sun sa\u0253awa koyarwar addinin Musulunci da kuma \u0199ara wa aure tsada lamarin da suka ce na tilastawa wasu matasa shafe tsawon lokaci ba tare da yin aure ba.<\/p>\n<p>To sai dai kuma irin wadannan matakan basu cika tasiri ba kasancewar a matakin kananan hukumomi ake sanyasu sannan babu wasu hukumomi dake tabbatar da sai mutane sun bi irin wadannan matakan.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure &nbsp; Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta dukkanin bukukuwa da ake yi kafin da kuma bayan \u0257aurin aure a \u0199aramar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":1,"featured_media":9778,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":"","jetpack_publicize_message":"","jetpack_publicize_feature_enabled":true,"jetpack_social_post_already_shared":true,"jetpack_social_options":{"image_generator_settings":{"template":"highway","default_image_id":0,"font":"","enabled":false},"version":2}},"categories":[20098],"tags":[624,20160,20163,20164,20165,20166],"byline":[],"class_list":["post-9777","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-taska","tag-adamawa","tag-biki","tag-cocktail-party","tag-fulani-day","tag-kauyawa-day","tag-majalisar-musulunci"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v27.3 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure - PRNigeria Hausa<\/title>\n<meta name=\"description\" content=\"Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta\" \/>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_US\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure - PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"PRNigeria Hausa\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2022-02-17T12:19:19+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Web Engineer\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Web Engineer\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Est. reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"4 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\\\/\\\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/\"},\"author\":{\"name\":\"Web Engineer\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/83f574a943a8093187e906308f785266\"},\"headline\":\"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure\",\"datePublished\":\"2022-02-17T12:19:19+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/\"},\"wordCount\":748,\"commentCount\":0,\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"\",\"keywords\":[\"Adamawa\",\"Biki\",\"Cocktail Party\",\"Fulani Day\",\"Kauyawa Day\",\"Majalisar Musulunci\"],\"articleSection\":[\"Taska\"],\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/\",\"name\":\"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure - PRNigeria Hausa\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"\",\"datePublished\":\"2022-02-17T12:19:19+00:00\",\"author\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/83f574a943a8093187e906308f785266\"},\"description\":\"Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-US\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#primaryimage\",\"url\":\"\",\"contentUrl\":\"\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/2022\\\/02\\\/17\\\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\\\/#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#website\",\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/\",\"name\":\"PRNigeria Hausa\",\"description\":\"Reliable Platform for Press Release Syndication\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-US\"},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/#\\\/schema\\\/person\\\/83f574a943a8093187e906308f785266\",\"name\":\"Web Engineer\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-US\",\"@id\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g\",\"url\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\\\/\\\/secure.gravatar.com\\\/avatar\\\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g\",\"caption\":\"Web Engineer\"},\"sameAs\":[\"https:\\\/\\\/deborian.com\\\/\"],\"url\":\"https:\\\/\\\/prnigeria.com\\\/hausa\\\/author\\\/adebo\\\/\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure - PRNigeria Hausa","description":"Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/","og_locale":"en_US","og_type":"article","og_title":"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure - PRNigeria Hausa","og_description":"Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta","og_url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/","og_site_name":"PRNigeria Hausa","article_published_time":"2022-02-17T12:19:19+00:00","author":"Web Engineer","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Web Engineer","Est. reading time":"4 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/"},"author":{"name":"Web Engineer","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/83f574a943a8093187e906308f785266"},"headline":"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure","datePublished":"2022-02-17T12:19:19+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/"},"wordCount":748,"commentCount":0,"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"","keywords":["Adamawa","Biki","Cocktail Party","Fulani Day","Kauyawa Day","Majalisar Musulunci"],"articleSection":["Taska"],"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/","name":"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure - PRNigeria Hausa","isPartOf":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#primaryimage"},"thumbnailUrl":"","datePublished":"2022-02-17T12:19:19+00:00","author":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/83f574a943a8093187e906308f785266"},"description":"Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#breadcrumb"},"inLanguage":"en-US","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#primaryimage","url":"","contentUrl":""},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/2022\/02\/17\/haramta-bukukuwa-aure-adamawa\/#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan \u0257aurin Aure"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#website","url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/","name":"PRNigeria Hausa","description":"Reliable Platform for Press Release Syndication","potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-US"},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/#\/schema\/person\/83f574a943a8093187e906308f785266","name":"Web Engineer","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-US","@id":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/60c13b341a258564c1ea64f00fb1e0ff41a1a00f761c465c31fc4b112b217550?s=96&r=g","caption":"Web Engineer"},"sameAs":["https:\/\/deborian.com\/"],"url":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/author\/adebo\/"}]}},"jetpack_publicize_connections":[],"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9777","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/1"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9777"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9777\/revisions"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9777"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9777"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9777"},{"taxonomy":"byline","embeddable":true,"href":"https:\/\/prnigeria.com\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/byline?post=9777"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}