Home Labarai An kama ‘yan daba da masu ƙwacen waya 98 a Kaduna

An kama ‘yan daba da masu ƙwacen waya 98 a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kama ‘yan daba da masu ƙwacen wayoyi da aka fi sani da ‘yan ‘Sara-Suka’ 98 a jihar.

Gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai ne ya buƙaci ɗaukar tsattsauran mataki kan ɓata-garin, sakamakon ƙaruwar ayyukan ‘yan daba da masu ƙwacen wayoyi a ƙwaryar birnin Kaduna.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar ya ce an gurfanar da 19 daga cikinsu a gabon kotu, yayin da ake ci gaba da bincike kan mutane 61, kafin a gurfanar da su.

Ɓata-garin kan farmaki mutane tare da ƙwace musu wayoyi da sauran kayayyaki, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka tare da jikkata mutane masu yawa.

Rahoton kamen wanda ‘yan sanda suka fitar, ya ce an kama ‘yan dabar a ranakun 26 da 28 ga watan Afrilu.

Rahoton ya ce 18 daga cikin ɓata-garin an kai su sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar domin faɗaɗa bincike, gabanin gurfanar da su a gaban kotu.

Gwamnan jihar ya umarci rundunar ‘yan sandan da su tabbatar da yin abin da ya dace domin gurfanar da su a gaban kotu, tare da faɗaɗa bincike don kamo duk masu aikata irin wannan ta’asa a faɗin jihar.

El-Rufai ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata, sanadiyyar ayyukan ‘yan bindigar.

Daga ƙarshe gwamnan ya yi kira ga al’umma musamman mazauna unguwannin da ake wannan ta’asa da su kai sunayen ‘yan dabar da ke addabar yankunansu ga jami’an tsaro domin a bibiye su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Sojojin Ruwa da na Ƙasa Sun Kashe Ƴan Ta'adda 34 a Sabon Hari a Tafkin ChadiHukumar FRSC ta Kaddamar da Samame a Faɗin Ƙasa Kan Lambar Mota na BogiJama'ar Jigawa na Rera Taken "Dole Tinubu ya Tsaya" Yayin da Shugaban NITDA ke Jagorantar GangaminSanata Buba ya Kai Ta'aziyya ga Masarautar Misau Kan Waɗanda Suka Samu Hadari, Ya Kaddamar da Ofishin Yaƙin Neman Zaɓen Jam'iyyar PRPFBI ta Yabi Najeriya Kan Yakar Cin Zarafin Yara, Tinubu ya Yabawa Hukumar EFCCIGP Disu ya Samu Haɗin Kan Amurka da Italiya Don Horar da Ƴan Sanda 5000Kano: NSCDC ta Kai Samame Haramtacciyar Matatar Dizal, ta Kama Mutane 5Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda 71 a Borno da YobeƳan Sanda Sun Tabbatar da Ceto Malamai 3 da Aka Sace a ZamfaraRahoton Siyasa: Rikicin Rijistar INEC da Zargin Sace Sowore Yayin da APC ta fi Ɗaukar HankaliNBSA ta Kaddamar da Sabon Tsarin Dijital Domin Magance Karancin Jini a NajeriyaABU da Jami'ar Copenhagen Sun Kaddamar da Bincike Don Magance Rikicin Manoma da Makiyaya da Kara Samar da MadaraYushau Shuaib ya Zama Babban Memba a IPRA, Ya Sami Matsayin FIPRATinubu Ya Kaddamar da Jiragen Helikwafta Biyar na NAF Yayin da Rundunar ke Jiran Karin Jiragen 67NSA Ya Bawa Kwamitin Bita Dokar Tsaron Kasa Wa'adin Makonni Hudu
X whatsapp