Gwamnatin Bauchi ta ce za ta dauki matasa akalla dubu 20,000 aiki domin yakar matsalar tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, karkashin wata rundunar tsaro da za ta kirkiro ta musamman a jihar.
An ruwaito cewa rundunar tsaron za ta kasance ne kamar wadda jihohin kudu maso yammacin kasar suka kirkiro wadda ake kira Amotekum.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gwamnan jihar Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ne ya bayyana matakin jim kadan da sake rantsar da shi a wa’adi na biyu a matsayin gwamnan a jiya Litinin.
Mai sharia Rabi Talatu ce ta rantsar da shi tare da mataimakinsa Mohammed Auwal Jatau a lokacin.
Gwamnan ya ce rundunar wadda za ta taimaka gaya ga tsarin tsaron da tuni ake da shi a kananan hukumomin jihar za ta kunshi matasa 20,000 da za a fara dauka a kashin farko.
PRNigeria hausa












