Home Labarai Dangote ya kaddamar da tallafin rabon abinci na Naira Biliyan 15

Dangote ya kaddamar da tallafin rabon abinci na Naira Biliyan 15

A wani mataki na rage radadin talauci a tsakanin al’umma, gidauniyyar Dangote ta kaddamar da tallafin rabon abinci na kasa a jihohin kasar nan inda mutane miliyan daya suka amfana.

Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da cewa tallafin zai game dukkanin kananan hukumomin Nijeriya 774, na kimanin buhunan shinkafa miliyan daya me nauyin kilo 10.

Jihar Kano ta samu kaso mafi girma inda mutane 120,000 suka amfana wanda daga bisani rabon zai ci gaba a sauran jihohin kasar.

Haka zalika rabon shinkafa mai kilo 10 zai ci gaba a dukkanin sauran kananan hukumomi na Jihar Kano.

Bikin kaddamar da rabon abincin dai ya gudana ne a budadden dakin taro na fadar Gwamnatin Kano da shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya samu halarta da kuma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A cewar Alhaji Aliko Dangote , sun ga dacewar raba kayan abincin ne ba wai kawai don magance matsalar yunwa ba, har da batun saukakawa al’umma wajen gudanar da rayuwa a kasa ba-ki daya.

“Hakan kuwa ya zama wajibi duba da muhimmancin zumunci da ‘yan uwan taka dake tsakanin mu, da kuma hadin kai a wannan lokaci da ake fusakantar kalubalen rayuwa.

“A wannan wata na Ramadan, lokaci ne da muke sadar da halayen nagarta, wanda ke taimakawa wajen tallafawa al’umma”.

“Ina da kwarin gwuiwar sanar daku cewa wannan tallafin na yanzu na musamman ne, duk da cewar mun yi irin sa a kasa da wata guda da ya gabata, amman muka ga dacewar sake tallafawa al’umma musamman a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan.

Attajirin Alhaji Aliko Dangote, ya shaidawa gangamin taron al’ummar cewa wannan kari ne akan tallafin da ya gudana na mutane dubu goma da ake ciyarwa kullum a Jihar Kano, yace Tallafin shinksfar Mai kilo goma da ya kaddamar kimanin miliyan Daya wanda ya lakume kudade Naira bilyan 15 a kasa ba-ki daya.

Da yake jawabi Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shirin rabon tallafin kayan abincin inda yace yazo a dai-dai lokacin da dimbin al’umma ke bukatar hakan.

Gwamnan ya bukaci kwamitin da aka dorawa nauyin rabon kayan abincin ciki har da hukumar HISBAH ta jiha da su maida hankali wajen aiwatar da aikin cikin gaskiya da rikon amana don cimma manufar shirin.

“Wannan shirin zai taimaka wajen rage saukaka rayuwa, a cewar Gwamnan Kano.

“Inda ya sake kara jinjina kaso mafi tsoka da jihar ta samu”.

Zouera Yousoufou dake zaman shugaban gidauniyyar ta Aliko Dangote tayi karin haske kan kokarin Alhaji Aliko Dangote wajen tallafawa al’umma, inda yace shakka babu gidauniyyar zata ci gaba da baiwa wannan bangaren muhimmanci.

“Mune a gidauniyyar Dangote muke ganin ya zama wajibi a sanar da al’umma irin kokarin da yake yi don sauran al’umma masu kudi su kwaikwayi halayensa na gari na tallafawa al’umma”, a cewar Yousoufou.

Rabon tallafin kayan abincin da Alhaji Aliko Dangote ya jagoranta na shinkafa miliyan Daya dake dauke da kilo goma na nuni da kokarin sa wajen rage radadin rayuwa da marasa galihu ke fuskanta da kuma kara dankon zumunci a tsakanin al’umma.

“Mune a gidauniyyar Dangote muke ganin ya zama wajibi a sanar da al’umma irin kokarin da yake yi don sauran al’umma masu kudi su kwaikwayi halayensa na gari na tallafawa al’umma”, a cewar Yousoufou.

Rabon tallafin kayan abincin da Alhaji Aliko Dangote ya jagoranta na shinkafa miliyan Daya dake dauke da kilo goma na nuni da kokarin shi wajen rage radadin rayuwa da marasa galihu ke fuskanta da kuma kara dankon zumunci a tsakanin al’umma.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp