Gwamnan Enugu Ya Naɗa Mataimaka 101
Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya amince da nadin sabbin mataimakan siyasa 101 da suka kunshi masu ba da shawara na musamman bakwai, manyan mataimakan musamman shida da kuma mataimakan musamman 88.
An sanar da nadin, wanda ya fara aiki nan take, a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Chidiebere Onyia ya fitar.
An bai wa sabbin masu ba da shawara na musamman da aka naɗa mukamai waɗanda suka shafi harkokin gwamnati da haɗin gwiwa, harkokin manufofi da nazarin manufofi, dangantakar masu ruwa da tsaki da harkokin al’umma, ci gaban tattalin arziki, haɗin gwiwar jama’a, kasuwanci da haɓaka kasuwanci, da kuma warware rikici da sulhu.
Fidelis Odo, Augustine Okoli, Pedro Nwankwo, Chimezie Nkwuo, Vitalis Okonkwo, Peter Omeje da Sam Nwagu.
Read Also:
Manyan mataimaka na musamman guda shida sune Rachael Okonkwo, Okey Ude, Chinedu Chukwunwike, Peter Ogbe, Chinedu Ozoeluba da Frank Udemezue.
Jagororinsu sun haɗa da haɓaka masana’antar fina-finai da ƙirƙira, harkokin jam’iyyu da tattara jama’a, sa ido kan jam’iyyu, bin doka da ƙa’idoji, warware takaddamar iyakoki da filaye, da kuma haɓaka ƙananan da matsakaitan kasuwanci.
A cewar sanarwar, mataimakan na musamman za su kula da nauyin da ya rataya a wuyansu na kare dazuzzuka, tsaftar kasuwa, kula da cibiyoyin kiwon lafiya, kare muhalli, ci gaban al’umma, shigar da matasa cikin harkokin jama’a, wayar da kan jama’a, sa ido kan kayayyakin more rayuwa, ci gaban karkara, fasaha da kirkire-kirkire, da sauransu.
Sanarwar ta ce nadin nadin wani bangare ne na kokarin da gwamnatin ke yi na karfafa hadin gwiwa da kuma samar da ayyuka a sassa daban-daban na jihar.










