Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 7 a Kwara
An ruwaito cewa an yi garkuwa da fasinjoji bakwai a kan hanyar Eruku zuwa Iyemero da ke jihar Kwara.
Wata majiya da ba a tabbatar ba ta ce wasu ma’aurata da aka yi aure kwanan nan suna cikin wadanda abin ya shafa.
Majiyoyin yankin sun ce wadanda abin ya shafa suna dawowa daga wani biki a Eruku a yammacin ranar Asabar, sai ‘yan bindigar suka tare motarsu.
Amma, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya ce bayanan da ke hannunsa sun nuna cewa an yi garkuwa da mutane uku a kan hanyar Eruku ranar Asabar.
Read Also:
Ya ce haɗin gwiwar jami’an tsaro, ciki har da sojoji, ‘yan sanda da kuma ‘yan banga na yankin, sun fara aiki don tabbatar da an sako waɗanda abin ya shafa.
“Bayanan da muke da su sun nuna cewa an sace mutane uku a kan titin Eruku ranar Asabar. Ba a tantance ainihin wurin da lamarin ya faru ba tukuna.”
“Amma, jami’an tsaro na haɗin gwiwa, gami da sojoji, ‘yan sanda da kuma ‘yan banga na yankin sun riga sun fara bincike a cikin daji a wannan yankin don tabbatar da sakin waɗanda abin ya shafa. Zan bayar da ƙarin bayani da zarar mun sami cikakken bayani game da lamarin,” in ji kwamishinan ‘yan sanda.










