Home Taska Rayuwar DCP Abba Kyari a Baya Kadan da Kuma Yanzu

Rayuwar DCP Abba Kyari a Baya Kadan da Kuma Yanzu

Rayuwar DCP Abba Kyari a Baya Kadan da Kuma Yanzu

Daga dakatarwar da aka yi masa daga hukumar ‘yan sanda har zuwa kama shi bisa zargin alaka da miyagun kwayoyi, labarin DCP Abba Kyari ya zama wani babban abin fade a kasa, lura da irin bajintarsa a baya da yadda rayuwa ta yi masa atishawar tsaki.

Dajarar Kyari ta fara zubewa ne a watan Yulin 2021 lokacin da wata takardar kotu a Amurka ta bankado alakarsa da wani shahararren dan damfara, wato Hushpuppi.

Hushpuppi, yana fuskantar tuhumar zamba a Amurka. Takardun kotun sun nuna cewa, hukumar binciken manyan laifuka ta tarayya (FBI) ta tuhumi Kyari da hada baki da Hushpuppi a badakalar dalar Amurka miliyan 1.1.

Ko da yake Kyari ya musanta zargin, ‘yan sanda sun dakatar da shi yayin da aka kafa kwamitin da zai binciki zargin nasa da hannu wajen zambar.

A ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, Abubakar Malami (SAN), babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), ya ce gwamnatin tarayya da gwamnatin Amurka suna tattaunawa kan yiwuwar mika Kyari.

AGF ya kuma ce an tattara dalilai masu ma’ana kan zargin da ake yiwa Kyari.

Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da luguden lebe kan yiwuwar mika Kyari, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta bankado boyayyar harkallar Kyari a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.

Sa’o’i kadan bayan sanarwar, ‘yan sanda sun sanar da kama shi tare da mika shi a hannun hukumar NDLEA.

Kyari: Sarki ya zama bawa

Kafin a fara tabarbarewar shaharar Kyari da fadawa wulakanci, ya kasance dan sanda mai farin jini a kafafen yada labaran Najeriya, inda ake bayyana shi da “super cop”.

Sunansa ya shiga bakin ’yan Najeriya da dama a lokacin da ake tsaka da fuskantar barazanar tsaro mai sarkakiya da ta addabi Najeriya.

A 2019, lokacin da yawan sace-sacen jama’a a kan titin Abuja zuwa Kaduna ya tunzura, Kyari da tawagarsa ne aka tura domin magance matsalar.

Majalisar wakilai ta karrama Kyari saboda “fice a aiki”

A watan Yuni 2020, an gayyaci DCP Kyari zuwa zauren majalisar wakilai kuma an karrama shi “saboda kwazonsa da fice a aiki na tsawon shekaru a rundunar ‘yan sandan Najeriya”.

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya ce karramawar da aka yi wa Kyari ba wai daga ‘yan majalisar ne kadai ba, daga al’ummar Najeriya ne, inji rahoton TheCable.

A kalamansa yayin gabatar da lambar yabo ga Kyari:

“Ba dan abin da suke yi a kowane lokaci ba ne kuma ga kowa ba sai dai ga wadanda suka bambanta kansu a fannonin hidima daban-daban.

“Haka kuma don nuna wa ‘yan Najeriya cewa duk da rashin kyawun martabar ‘yan sandan Najeriya, akwai jami’ai na kwarai a rundunar.

“Wannan ita ce babbar karramawa domin wannan ita ce cibiya daya tilo da dukkan ‘yan Najeriya ke da wakilci. Wannan ba lambar yabo ce daga majalisar wakilai kadai ba sai dai daga daukacin al’ummar Najeriya.”

Silverbird: ‘Gwarzon Jarumin Shekara, 2018’

Shekaru biyu gabanin karramawar majalisar wakilai, DCP Kyari ya kasance amintacce kuma gwarzon shekarar 2018 ta Silverbird Communications.

Da yake mika lambar yabo ga Kyari a madadin Silverbird, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya yabawa DCP da aka dakatar saboda kokarinsa na “tabbatar da kowa ya samu damar yin barci da dare”.

Ya kara da cewa:

“Yana da kyau a karrama duk wanda ke ba da gudummawa don tabbatar da cewa mun sami damar yin barci mai kyau. Idan aka yi la’akari da abin da ya aikata, na gode wa Silverbird da ta zabe shi.

“Abin da muke bukata ke nan a kasar nan, mu karrama wadanda ke aiki, lokaci ya yi da za a daina karrama wadanda ke ruguza kasa.”

Aisha Buhari ta karrama Kyari Haka kuma a shekarar 2018, Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta karrama DCP Kyari, kamar yadda jaridar TheCabble ta ruwaito.

An ba shi wani allon karramawa, wanda aka rubuta, “don nuna godiya da kuma sanin irin rawar da yake takawa wajen dakile laifuka a Najeriya”.

An ba shi lambar yabon ne a Aso Rock, inda aka yaba wa Kyari bisa rawar da ya taka wajen magance wasu manyan matsalolin da suka addabi al’ummar kasar nan.

A yanzu kuma, da alamu darajarsa ta yi kasa, sannan ‘yan Najeriya na ci gaba da mamakin yadda batutuwa suka fito kansa, hakazalika ya shiga tarihi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp