Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano Murtala Sule Garo ya yi murabus daga mukamin sa domin Cika Umarnin Gwamna Ganduje.
Murabus din na zuwa ne sa’aoi kadan bayan gwamna jihar kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci masu Muradin tsaywa Takara a cikin jami’an Gwamantin jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Murabus din na kunshe ciki wata sanarda da POLITICS DIGESTta samu game da ajiye aikin na Murtala Garo, inda yace ya ajiye mukamin nasa ne domin yana da sha’awar yin takarar Gwamnan Jihar Kano a zaben shekarar 2023.
Murtala Garo na guda cikin manyan wadanda ke zawarcin kujerar gwamnan Jihar Kano, karkashin inuwa Jam’iyyar APC mai mulkin jihar.
” Ina yabawa Gwamna Ganduje bisa damar da ya bani nayin aiki da shi a Matsayin Kwamishinan Kananan Hukumomi, Ina godiya da dama da Kuma Sauran abokan aikin da mukai aiki da su”. A cewar Murtala Sule Garo












