Home SIYASA Yanzu – Yanzu: Karin Kwamishinoni Sun yi Murabus a Jihar Kano

Yanzu – Yanzu: Karin Kwamishinoni Sun yi Murabus a Jihar Kano

Wasu Karin Kwamishinonin da Mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da suka hadar da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Sunusi Sa’idu Kiru da babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar kano Faruq Sule Garo sun yi murabus daga mukaman su.

Ta cikin takardar Murabus da kwamishinan Ilimin Sunusi Sa’idu Kiru ya aiki wa gwamnan, ya gode masa matuka bisa damar da ya bashi na yiwa al’umma aiki a karkashin gwamnatin sa.

Ganduje ya bayar da umarni ga dukkan masu Muradin tsayawa Takara a cikin jami’an Gwamnatin Jihar Kano suyi murabus daga nan zuwa  ranar litinin. Umarnin da yayi daidai da sashe na 84(12) na sabuwar dokar zabe da aka yiwa gyaran fuska.

Tuni dai wasu kwamishinoni uku daga cikin kwamishinonin kunshin gwamantin Jihar Kano suka sanar da ajje aikin nasu, ta cikin takaddun sanarwa da suka aike ga Gwamnan.

Kwamishinonin sun hadar da Kwamishinan Kananan Hukumomi Murtala Sule Garo, Kwamishinan Karkara Musa Iliyasu Kwankwaso da na Kasafi da Tsare Tsare Nura Dankadai.

Sunusi Kiru ya bayyana Murabus din nashi matsayin abinda zai bashi damar wakiltar Bebeji/Kiru a Zauren Majalisar Wakilan Nijeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp