Home Taska Jami’an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a...

Jami’an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar Kebbi

Jami’an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar Kebbi

 

Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta 10 a wani artabu da ƴanbindiga a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar Litinin 10 ga watan Agusta, a yankin Rafin Makuku da ke ƙaramar hukumar Sakaba.

A sanarwar da kakakin rundunar na ƙasa CSP Ani Iniedu ya fitar, ya ce jami’anta sun tare ƴanbindigar ɗauke da muggan makamai ne yayin da suke ƙoƙarin wucewa daga jihar Zamfara zuwa Kebbi, inda suka yi musayar wuta.

Rundunar ta ce an kashe aƙalla ƴanbindiga 17 tare da lalata babura huɗu na maharan.

Sai dai jami’an ƴansanda 10 sun rasa rayukansu a artabun, yayin da wasu biyu suka samu raunuka inda a yanzu suke samun kulawa.

Rundunar ta kuma ce wasu fararen hula biyu sun mutu a yayin musayar wutar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp