Home SIYASA Zaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan...

Zaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasa

Zaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasa

 

Jam’iyyar PDP tsagin Kabiru Turaki ta ce ta miƙa sunan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Tsagin ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar, Ini Ememobong, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, rikicin shugabanci da ya dabaibaye PDP bayan hukuncin Kotun Ƙoli ya haifar da kafa kwamitin riƙon ƙwarya domin tafiyar da harkokin jam’iyyar da kuma gudanar da muhimman ayyukanta.

Tsagin Turakin ya nace cewa shi ne halastaccen shugabancin PDP, wanda ya tsayar da Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa tare da sauran ‘yan takarar gwamnoni, majalisun dokoki na tarayya da na jihohi.

Haka kuma ya ce ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke kwanan nan dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar.

 

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Haba, Abba Bichi — Waɗannan Tallace-Tallacen Ranar Haihuwa Sun Wuce Iyaka! Daga Yushau A. ShuaibNAF ta Kaddamar da Aikin Ceto Bayan Jirgin Saman Soja ya Fado a OndoSojoji Sun Kashe Mayakin B'Haram, Sun Kama Wani a GeidamRijistar Masu Kaɗa Kuri'a a Najeriya ta Kai Miliyan 103 - INECMuna Kafa Sabbin Sansanonin Sojoji Domin Kare Al'ummomin da ke Cikin Hatsari – TinubuJirgin Sojojin Sama (NAF) ya Fado a Ondo Dauke da Mutane 32Sojojin Najeriya Sun Kaddamar da Sabbin Bataliyoyi 3 Don Karfafa Tsaro a ZamfaraCOAS ya Nemi Karin Hadin Kan Sojoji da ECOWAS Kan Barazanar Ketare IyakokiSojoji Sun Kai Hari Sansanin Ƴan Ta'adda, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Kama Wanda Ake Zargi a Benue Yunwa da Tsananin Rayuwa Sun Sa Ƴan Tawaye 73 da Iyalansu Sun Mika Wuya — HQ TsaroDakarun Soji  Sun Ceto Sojan da Aka Sace a FilatoAn Tattara Bayanai Kan Hare-Haren Ta'addaci 367, An kashe Ƴan Ta'adda 52 a Watan SatumbaNajeriya @66: Gwamnatin Tarayya ta Karkata Kan Cigaba, Ayyukan Yi, da Inganta RayuwaNajeriya @66: Ministan Tsaro ya yi kira ga  Ƴan Najeriya da su Hada kai Domin Zaman Lafiya da TsaroPDP ta Zargi Gwamnatin Inuwa Yahaya da Shirya Katin Mambobi na Bogi Gabanin Zaben Fidda Gwani a Gombe
X whatsapp