Home SIYASA Jam’iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani...

Jam’iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya Sheƙa

Jam’iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya Sheƙa

 

Jihar Kano – Jam’iyyar NDC ta bukaci Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga, da tsohon gwamnan Kano, Kabiru Ibrahim Gaya, da su sake tunani kan rade-radin da ke cewa suna shirin komawa jam’iyyar APC.

Kiran ya biyo bayan ziyarar da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, tare da Hanga da Gaya suka kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli, 2026.

Jaridar Punch ta wallafa yadda shugaban APC na kasa ya kai ziyara gidajen Hanga da Gaya, lamarin da ya kara tayar da jita-jitar cewa suna dab da sauya sheka.

Kiran NDC ga Hanga da Gaya Shugaban NDC na jihar Kano, Hussaini Isah Mairiga, ya shaida wa Daily Trust cewa jam’iyyar ta damu da rahotannin da ake yadawa kan sauya shekar manyan siyasar biyu.

Ya ce:

“Labarin cewa APC mai mulki na kokarin jan hankalin Sanata Rufai Sani Hanga da tsohon gwamnan Kano Kabiru Gaya ya bazu ko’ina.

Har yanzu ba su sanar da mu a hukumance cewa za su sauya sheka ba, amma jiya ma mun gan su sun ziyarci Shugaba Tinubu. Wannan na nuna cewa labarin na iya zama gaskiya.”

Mairiga ya ce jam’iyyar ba za ta ji dadin rasa irin wadannan manyan jiga-jigai ba saboda haka su yi hakuri, su yi zamansu a NDC.

Ya kara da cewa:

“A matsayinmu na shugabanni, ba za mu yi farin ciki idan suka sauya sheka ba. Ko mamba na gari ya fita ba ma jin dadi, balle irin wadannan manyan mutane. Muna da kyakkyawar alaka da su kuma muna girmama juna.”

NDC ta roki su Hanga Mairiga ya amince cewa Hanga ya taba nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake tafiyar da wasu al’amura a cikin NDC, amma ya ce jagoran jam’iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zabi kada ya mayar masa da martani nan take.

A cewarsa:

“Tun da ba su sanar da sauya shekar ba a hukumance, muna rokon su su sake tunani su dakatar da wannan shiri. Mu zauna mu tattauna idan akwai abin da muka yi musu ba daidai ba.” “Kwankwaso ya ce bai ba shi amsa ba ne saboda yana cikin fushi, don haka ya jira ya huce kafin su zauna su tattauna.” Duk da kusancin da jam’iyyar APC mai mulki ke nunawa Sanata Hanga da Gaya, shugaban NDC na Kano ya ce har yanzu mutanen biyu cikakkun ƴaƴanta ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mabiya Addinai Biyu a Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Sabuwar YarjejeniyaAn Kashe Matashi Kan Murfin Tayar Adaidaita Sahu a KanoMutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga Sojoji
X whatsapp