Ba ma Goyon Bayan a Riƙa Tura Sojoji Domin Aikin Tsaro a Lokacin Zaɓe – INEC
Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta ce ba ta goyon bayan a riƙa tura sojoji domin aikin tsaro a lokacin zaɓe
INEC ta ce ya kamata a riƙa amfani da sojoji ne kawai a lokutan da yanayin tsaro ya zama tilas ba wai a maida hakann al’ada ba.
Read Also:
- Ƴan Sandan Legas Sun Kama Mutum 4 da Ake Zargi da Fashin Daji, Sun Kwato Wayoyin Hannu 25, Kwamfutoci da Kayan Ado na Zinare
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Rusa Wuraren Tace Mai Ba bisa Ka’ida Ba, Ta Kwato Lita 350 na AGO a Rivers
- 2027: Yahaya Bello Ya Tara Masu Daidaita Ayyuka na A4A a Arewa ta Tsakiya Domin sake Zaban Tinubu
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan ta bakin Daraktan Sashen Shari’a na INEC, Al-Hassan Umar, yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron karawa juna sani da aka gudanar a Kwalejin Yaƙi ta Sojoji da ke Abuja.
Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya INEC ce ke da alhakin shiryawa, gudanarwa da kuma sa ido kan zaɓe.
Ya kuma ce rundunar ƴan sandan Najeriya ita ce hukuma ta farko da ke da alhakin tabbatar da tsaro a lokacin zaɓe
“Rawar da rundunar soji ke takawa ta musamman ce. Ana tura dakarun soji ne kawai idan halin tsaro ya yi muni domin su taimaka wa sauran hukumomi, kuma hakan yake a kundin tsarin mulki,” in ji shi












