Hukumar Kula da Jami’o’in Najeriya ta Bada Umarnin Rufe Jami’o’i Saboda zaɓe
Wata sanarwa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya ta fitar ta umurci a rufe dukkanin jami’o’in ƙasar tsawon lokacin da za a gudanar da babban zaɓen ƙasar na 2023.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar, wadda ta samu sa hannun mataimakin shugaban hukumar, mai kula da harkar gudanarwa, Chris J. Maiyaki, ta ce za a rufe jami’o’in ne domin kare lafiyar ma’aikata, da ɗalibai a tsawon lokacin zaɓen.
Bayanin ya ce umurnin ya fito ne daga ministan ilimi na Najeriyar, Adamu Adamu, inda aka umurci dukkanin shugabannin jami’o’i su rufe daga 22 ga watan Fabrairu zuwa 14 ga watan Maris.
Matasa dai na daga cikin mafiya yawa a kundin rajistar zaɓen Najeriya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a babban zaɓen mai zuwa.












