Home Labarai LITTAFIN NADAMA: CUTAR SANKARA A FAYYACE

LITTAFIN NADAMA: CUTAR SANKARA A FAYYACE

Nadama

Littafin Wasan kwaikwayo na NADAMA yana dauke da labarun ma su sanya fargaba, tashin hankali, tausayi, farin ciki, da bakin ciki a zukatan masu karatu, tare da nu ni ga mahimmancin hakuri, gaskia da rukon Amana.

NADAMA, littafin wasan kwaikwayo ne da ya kunshi salo na ilimantarwa, fadakarwa, da wayar da kan Al’umma a kan cututtukan mata da yara irin su cutar sankara da yoyon fitsari, tare da alfanun karatun ‘ya mace domin cigaba da inganta rayuwar alumma gaba daya.

Marubuciyyar, Malama Fatima Sanda Usara, tayi amfani da rayuwar Sa’adatu, wacca ta kasance ‘yar gwagwarmaya me nemawa mata hakkin su domin inganta rayuwar su, tare da basu Kwarin gwiwa da magance matsalolin da ka iya addabar su.

A cikin littafin me shafuka 145, marubuciyar ta Kara fayyacewa cikin salo na fikira a kan mahimmancin ruko da gaskia da amana.

Ta hanyar haska rayuwar Malam Salman da Mariya, duk da kasancewar su a cikin talauci, hakan be hana su inganta rayuwar saadatu ba, yarinyar da su ka tsinta, suka raine ta har takai munzalin girma da aure kafin gaskiar asalin su waye iyayen ta ya bayyana.

Sannan marubuciyar tayi tsokaci ta hanyar fayyace irin kalubalen da marasa Galihu musamman daga karkara kan iya fuskanta Yayin ziyartar asibitoci ko Wajan ‘yan Sanda domin taimakon su.

Duba da yadda Malam Salman da Mariya suka ki amince wa da ‘Yansanda a lokacin da suka tsinci sa’adatu, da kuma yadda rashin bincike ya Janyo sanadiyyar mutuwar Salman.
Duk da kasancewar Littafin wasan kwaikwayo ne, amma marubuciyar tayi nasarar bayyana sakon da take son isar wa cikin fejina 145.

Ta yi amfani da salon rubutu me sanyaya tausayi, fargaba, da Tashin hankali a zuciyar masu karatu. Littafin NADAMA ya kan iya sanya NADAMA a zcuiyar wanda bai karanta shi ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp