Ministan kudin Nijeriya ya mika sabon daftarin mafi karancin albashin ma’aikatan Nijeriya naira dubu 105 ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ministan kudin Mr. Wale Edun da takwaransa na kasafi da tsare tsare Atiku Bagudu sun mika wa shugaban kasar daftarin dake dauke da sabon mafi karancin ALbashin na ma’aikata a fadar shugaban kasar dake birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis.
Solacebase ta ruwato jaridar Western Post na cewa daftarin na kushe da naira dubu 105 matsayin mafi karancin albashin ga ma’aikatan wanda yake daidai da dalar Amurka ($90).
Tuni dai Tinubu ya karbi Daftarin, wanda nan ba da jimawa ba ake tsammanin yin jawabi kan albashin a hukumance.
PRNigeria Hausa











