Home Bincike Bincike: Shin da gaske ne masu zanga-zanga sun yi wa fadar sarkin...

Bincike: Shin da gaske ne masu zanga-zanga sun yi wa fadar sarkin Musulmi bisa bukatar Obi ko kuma a chanja Gwamnati?

Wani faifen Bidiyo da yayi ta yawo a kafafen internet da kafafen sada zumunta, musamman manhajar WhatsApp da shafin Facebook, wanda ta nuna wasu tarin mutane masu zanga-zanga sun yi wa fadar sarkin musulmi da ke sokoto tsinke in da suke bukatar sauyin gwamnatin idan wakilan gwamnatin tarayya sun kai ziyara jihar.

An rubuta cewa: “Sokoto a ya! Yadda ma su zanga-zanga suka taro a fadar Sarkin Musulmi, suna ihun “ ba ma Tinubu…. Sai Obi ko kuma Sojoji su karbi kasar.”

To amma, tawagar binciken sahihancin labarai ta PRNigeria ta bi diddigin asalin bidiyon da ake ikirari a kai, wadda aka wallafa a shafukan sada zumuntar da suka hadar da Facebook, bayan da karamin minstan tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya jagorancin tawagar manyan sojoji zuwa Sokoto, domin duba ayyukan sojojin na kawar da matsalar rashin tsaro da ta addabi shiyyar Arewa maso yammacin Nijeriya.

https://www.premiumtimesng.com/regional/nwest/731118-matawalle-security-chiefs-arrive-in-sokoto-following-tinubus-order.html

haka kuma, wani bincike da aka fadada ya tabbatar da cewa bidiyon tsoho ne da aka dauka lokacin zanga –zangar ‘EndBadGovernance’, wadda ta gudana a watan Agustan 2024, akalla wata guda bayan ikirarin.

Zanga-zangar #EndBadGovernance, wadda aka fi sani da  #EndbadGovernanceInNigeria ta kunshi jerin zanga-zangar da babu wadanda suka shirya ta wadanda suka gudana a mabanbanta wurare a fadin Nijeriya da ka gudanar a 1 ga watan Agustan 2024 zuwa 10 ga watan. Wannan zanga-zanga ta faru ne sakamakon tsadar kayan masarufi a fadin kasar abin da ya haifar da tsadar rayuwa da wahalhalun rayuwa ga al’ummar kasar.

KAMMALAWA: binciken da jaridar PRNigeria ta gudanar ya tabbatar da wannan bidiyon da aka yada aka ce masu zanga-zanga ne a fadar sarkin musulmi da ke Sokoto lokacin da tawagar karamin ministan Tsaron Nijeriya da shuwagabannin tsaron kasar suka ziyarci fadar, gaskiya tsohon bidiyo ne na zanga-zangar EndBadGovernance da aka gudanar a watan Agustan 2024.

Don haka,  PRNigeria ta yanke hukuncin kan ikirarin da ake da ke cewa masu zanga-zanga a fadar mai Alfarma sakin musulmi da ke jihar Sokoto, da ke nuna goyon bayan Peter Obi ko sauya gwamnati labarin karya ne.

By PRNigeria

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp