Majalisar zartaswar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da kashe Naira 8,199,635,732.07 domin gudanar da manyan ayyuka 15 a fadin jihar.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan tattaunawa a taron majalisar zartarwa karo na 24 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano ranar Laraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
An ware naira 2,737,518,204.96 domin gina ajin karatu mai ajujuwa huɗu a fadin kananan hukumomin jihar 44.
Haka kuma majalisar ta amince da fitar da naira 2,311,388,177.70 domin sake aikin gina titin shataletalen gidan gwamnati zuwa titin Lodge Road, zuwa Race Course zuwa shataletalen otal ɗin Daula, tare da ƙarin ayyukan da suka shafi titin asibitin Nasarawa, titin Dawaki da kuma titin Lugard.
An ware Naira 1,870,814,360.10 domin gyaran babban ɗakin taro na Africa House da ayyukan tuntuɓa a gidan gwamnati.











