Rahotannin daga jihar Bauchi na tabbatar da cewa Jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya rasu.
Malamin ya rasu ne da asubahin ranar Alhamis. a wani asibiti da ke jihar Bauchi, sakamakon ƴar gajeriyar jinya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Majiyoyi daga iyalansa sun ce za a yi jana’izar shehin malamin ne a ranar Juma’ah.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya rayu tsawon shekaru 100 a duniya, inda ke guda cikin hafizan Al’qurani mai tsarki, masanin tafsi, ya rasu ya bar ƴaƴa da jikoki masu yawa.












