Home Taska Rundunar Sojin Najeriya ta Gudanar da Hare-Hare Kan Maɓoyar ƴan Bindiga a...

Rundunar Sojin Najeriya ta Gudanar da Hare-Hare Kan Maɓoyar ƴan Bindiga a Jihar Katsina

Rundunar Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta Gudanar da Hare-Hare Kan Maɓoyar ƴan Bindiga a Jihar Katsina

 

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da wasu zafafan hare-hare kan ƴan bindiga a wasu yankuna na jihar Katsina da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan mutuwar tsohon Janar na soja a hannun ƴan bindiga.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa an fara wannan farmakin mai taken ‘Operation Clean Sweep III’ domin fatattakar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Matazu da wasu yankunan Katsina.

Ya ce sun fara wannan farmaki ne tun ranar 14 ga watan Yunin 2026.

Rundunar ta ƙaddamar da hare-haren ne ƙarƙashin Operation Fansan Yamma da ke aiki a yankin Arewa maso yammacin ƙasar.

Sanarwar ta ce an samu nasarori musamman a yankunan tsaunukan Dikkawa da sauran ƙauyukan da ke kusa.

Ta ce ta kai samamen ne a yankunan Adua, Nasarawa da Karaduwa, inda ya kai ga gano da lalata maboyar ‘yan ta’adda, wuraren ajiye kayayyaki da sauran cibiyoyin da suke amfani da su.

“A lokacin harin, an lalata maɓoyar ƴan ta’adda da kayayyakinsu da motocinsu, kuma hakan ya rage musu ƙarfin kai hari a yankin,” in ji sanarwar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga PantamiGazawar Demarketing: Yadda Sukar Rarara Mai Cike da Kiyayya ga Pantami Ya Rushe Daga Yushau A. ShuaibƘungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin AikiDakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da suƳan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari'a da ke Jihar KatsinaBa ma Goyon Bayan a Riƙa Tura Sojoji Domin Aikin Tsaro a Lokacin Zaɓe - INECJam'iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya SheƙaYan Bindiga Sun Kashe Kanal Abdussalam Ude Sun Raunata MatarsaMutane 15 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Benue Zaɓen 2027: Uba Sani ya zaɓi MataimakinsaJami'an Tsaro Sun Kuɓutar da Mutane 32 Yayin da 4 Suka Mutu a Jihar Sokoto 
X whatsapp