Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bayan nasarar da suka samu wajen ceto mutane 308 da ƴanbindiga suka sace a jihohin Kwara da Neja da ke arewa ta tsakiya.
A cikin mutanen da aka ceto, 163 an sace su ne daga yankin Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, yayin da 145 kuma aka sace su daga jihar Neja.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an ce an ceto mutanen ne daga dajin Kainji Lake National Park da ke ƙaramar hukumar New Bussa a jihar Neja.
Read Also:
Sanarwar ta ce an gudanar da aikin ne bisa sahihan bayanan sirri, tare da haɗin gwiwar Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Rundunar Sojin Najeriya, Hukumar DSS da kuma ‘Yan Sandan Najeriya.
“Wannan shi ne mafi girman aikin ceto mutane da aka taɓa gudanarwa cikin rana guda ta hannun jami’an tsaron haɗin gwiwa,” a cewar shugaban ƙasa.
Tinubu ya yaba da jarumtaka da haɗin kan jami’an tsaron, inda ya ce nasarar ta nuna yadda ayyukan tsaro da tattara bayanan sirri ke ƙara inganta.
Mutanen da aka ceto na karɓar kulawar gaggawa a asibitin Wawa Cantonment, kafin daga bisani a miƙa su ga gwamnatocin jihohinsu domin ci gaba da kula da su da kuma haɗa su da iyalansu.
Shugaban ya sake tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kawar da matsalolin tsaro da dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.










