Home Taska An Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan...

An Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin Gargajiya

An Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin Gargajiya

 

Yaro na hudu, wanda aka tsinta a sume tare da sauran, an ceto shi kuma aka yi hanzarin kai shi asibiti, inda yan sanda suka ce, halin da yake ciki yana da hadari sosai.

An sami yara uku matattu a gidan wata mata Mai maganin gargajiya, wadda aka fi sani da “Ezenwanyi”, a kauyen Umuoduba, Ideani cikin karama hukumar Idemili north a jihar anambra.

Lamarin, wanda ya faru a tsakar daren Laraba, ya jefa al’umma cikin kaɗuwa, yayin da mazauna garin ke ƙoƙarin fahimtar yanayin da ya kai ga mutuwar yaran.

Mazauna garin sun ce, an tsinci yara huɗu, waɗanda ake ƙiyasin shekarunsu tsakanin 6 zuwa 15, a sume a cikin tsakar gidan matar.

Yayin da aka tabbatar da mutuwar uku daga ciki, yaro na huɗu kuwa, wanda ke da sauran numfashi, mazauna garin ne suka kai shi asibiti kafin jami’an agajin gaggawa su ƙaraso.

Bayanan asalin yaran da kuma yadda suka tsinci kansu a gidan ba a gama tabbatarwa ba a lokacin da ake haɗa wannan rahoto.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga PantamiGazawar Demarketing: Yadda Sukar Rarara Mai Cike da Kiyayya ga Pantami Ya Rushe Daga Yushau A. ShuaibƘungiyar NARD ta yi Barazanar Shiga Yajin AikiDakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga 3 Sun Ceto Mutane 9 da akai Garkuwa da suƳan Bindiga sun kai Hari a Kotun Shari'a da ke Jihar KatsinaBa ma Goyon Bayan a Riƙa Tura Sojoji Domin Aikin Tsaro a Lokacin Zaɓe - INECJam'iyyar NDC ta Buƙaci Sanata Hanga da Gaya da su Sake Tunani Kan Sauya SheƙaYan Bindiga Sun Kashe Kanal Abdussalam Ude Sun Raunata Matarsa
X whatsapp