Hukumar INEC za ta ƙaddamar da Na’urar Bibiyar shirye-shiryen Zaɓen 2027 kai Tsaye
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce tana shirin ƙaddamar da wata na’ura da za ta ba ta damar bibiyar shirye-shiryen babban Zaɓen 2027 kai tsaye daga kowace jiha.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Legas, yayin wani taron bita na musamman da aka shirya wa sakatarorin gudanarwar hukumar.
Ya ce taron bitar na da nufin samar da ingantacciyar na’urar bibiyar ayyuka ta amfani da Excel, wadda za a haɗa da dandamalin intanet na Cibiyar Sa-Ido da Taimakon Zaɓe ta INEC da kuma Tsarin Ayyukan Zaɓe.
Amupitan ya ce a baya hukumar ba ta da tsarin bai ɗaya da zai ba ta damar bibiyar ayyukan da ke gaban sakatarorin gudanarwar INEC a faɗin ƙasar.
Read Also:
- Ƴan Sandan Legas Sun Kama Mutum 4 da Ake Zargi da Fashin Daji, Sun Kwato Wayoyin Hannu 25, Kwamfutoci da Kayan Ado na Zinare
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Rusa Wuraren Tace Mai Ba bisa Ka’ida Ba, Ta Kwato Lita 350 na AGO a Rivers
- 2027: Yahaya Bello Ya Tara Masu Daidaita Ayyuka na A4A a Arewa ta Tsakiya Domin sake Zaban Tinubu
Ya bayyana cewa sabuwar na’urar za ta ba kwamishinonin zaɓe na jihohi, manyan jami’an sa-ido, sakataren hukumar da kuma hedikwatar INEC damar samun bayanai nan take kan yadda shirye-shiryen zaɓe ke gudana.
Ya ce bayanan za su haɗa da rarraba kayayyakin zaɓe, horar da ma’aikatan wucin-gadi da kuma matakin shirye-shiryen zaɓe a kowace jiha.
“Wannan zai ba mu damar sauyawa daga mayar da martani ga matsaloli bayan sun faru, zuwa tsarin gudanarwa mai hangen nesa da ɗaukar mataki tun kafin matsala ta taso,” in ji shi.
Shugaban INEC ya ce matakin ya zama dole musamman ganin cewa adadin masu rajista a rajistar masu zaɓe ta ƙasa na dab da kai wa miliyan 100.
Ya ce taron bitar zai kuma tattauna batutuwa da suka shafi ci gaba da rajistar masu zaɓe, sufuri da sarrafa kayayyakin zaɓe, amfani da fasahar zaɓe, inganta ayyukan ma’aikatan wucin-gadi da kuma bin ƙa’idojin kuɗi.
Amupitan ya ce hukumar za ta yi amfani da nasarori da darussan da ta koya daga zaɓukan da aka gudanar a wasu jihohi domin inganta shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Ya ce INEC na fatan tabbatar da cewa irin nasarorin da aka samu a waɗancan zaɓukan sun zama ginshiƙin inganta tsarin zaɓe a duk faɗin ƙasar yayin zaɓen 2027.












