Shugaban NITDA ya Karɓi Baƙuncin Jakadan ƙasar Sweden a Nageriya
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), a wannan rana, ya karɓi baƙuncin jakadan ƙasar Sweden a Nageriya, mista Carl-Micheal Gräns, a Abuja.
Maƙasudin ziyarar shi ne don tattaunawa akan harkokin fasahar zamani, gami da duba iyuwar ƙulla alaƙar aiki a tsakanin ƙasashen biyu a fannin ƙere-ƙeren kayayyakin fasahar zamani.
Laraba, 23 ga watan Fabarairu, 2022.











