Home Taska Mafi Munin Abu a Jikin Mace: Dr Mansur Sokoto ya yi Karin...

Mafi Munin Abu a Jikin Mace: Dr Mansur Sokoto ya yi Karin Bayani Kan Maganar Sheikh Daurawa

Mafi Munin Abu a Jikin Mace: Dr Mansur Sokoto ya yi Karin Bayani Kan Maganar Sheikh Daurawa

Dr Mansur Sokoto ya yi karin bayani kan maganar Sheikh Daurawa game da abin da wasu mata suka kira kushe halittarsu.

Dr Mansur ya bayyana tushen maganar Daurawa, inda ya kawo bayani daga katafaren littafin tafsiri sananne a duniya.

Dr Mansur ya ce sam ba Daurawa bane ya fara fadin haka, Sayyidina Ali ne ya fadi hakan yayin da yake magana kan gudun duniya.

A makon nan ne wasu ‘yan sohiyal midiya suka sa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a gaba tun bayan da wani bidiyon karatunsa ya fita, inda ya yi bayani kan gudun duniya da abin da ke cikinta.

Malamin ya yi tsokaci da cewa, mafi munin abu a jikin halittar diya mace ba komai bane fa ce farjinta, lamarin da bai yiwa wasu mata da yawa dadi ba.

Duk da cewa, bidiyon gajere ne, kuma wasu mutane da yawa sun bayyana bukatar a je a kalli cikakken karatun, mata da yawa sun fusata, inda suka ce babu wani karin bayani da suke bukata.

Martanin Dr Mansur Sokoto

Gawurtaccen malamin nan mazaunin jihar Sokoto, Dr Mansur Ibrahim Sokoto ya yi karin haske kan wa’azin na Sheikh Darurawa, inda yace ba Daurawa bane ya fara fadin wannan magana.

Malamin ya ambaci littafin wani babban malamin tafsirin al-Kur’ani, kuma mabiyin mazahabar Malikiyya dan kasar Andalus, inda malamin ya nakalto wata maganar sahabin Annabi (SAW) kuma surukinsa; Sayyidina Ali (RA) cewa shi ya fadi cewa farjin mace ne mafi muni a jikinta.

Dr Mansur Sokoto dai ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta ruwayar maganar Sayyidina Ali (RA) cikin harshen Larabci, kana ya fassara zuwa Hausa.

Ya bayyana inda sahabin ke magana kan jin dadin duniya cewa guda shida ne, yace abinci, abin sha, abin sakawa, abin shaka, abin hawa, sai kuma aure su ne mafi dadi a duniya.

Sayyidina Ali ya yi bayanin kan tushe da kololuwar dadin kowanne daga cikin shidan da ya lissafa, inda yace bai kamata dan Adam ya shiga damuwa saboda su ba.

To, a bayanin batun aure da kuma mace ne Sayyidina Ali (RA) yace:

“Aure kuma jin dadinsa yana wajen mata; wurin fitsari ne yake haduwa da wurin fitsari irin sa. Wallahi duk adon da ka ga mace ta yi, inda ya fi munin ne ake bukata (Farji)”.

– Tafsirin Qurtubi (17/255) Wannan batu na sayyina Ali (RA) daidai yake da abin da Sheikh Daurawa ya fada, don haka Dr Mansur yace ba fadin Daurawa bane, fadin surukin Annabi (SAW) ne A tsokacin Dr Mansur Sokoto, ya ce ya kamata mutane su lura cewa:

“Wa’azi akan a kiyayi duniya da kushe jin dadinta sanannen abu ne a cikin Alkur’ani da Hadisan Annabi (S) da maganganun magabatan Musulmi. Su kuma shakiyyan mutane neman wurin kushe Annabawa da karantarwarsu suke yi. Mai imani yana nisantar irin wannan tafarki nasu domin ya tsira da imaninsa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

Comments are closed.

Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp