Home Taska Mahaifina ne ya Ɗora ni Akan Cewa Duk Abin da na Samu...

Mahaifina ne ya Ɗora ni Akan Cewa Duk Abin da na Samu ba Nawa ne ni Kaɗai ba – Shugaban NITDA, Malam Kashifu Inuwa

Kashifu I

Mahaifina ne ya Ɗora ni Akan Cewa Duk Abin da na Samu ba Nawa ne ni Kaɗai ba – Shugaban NITDA, Malam Kashifu Inuwa

 

A wani mataki da ke nuni da irin tarbiyyar da mahaifinsa ya ɗora shi a kai tun a lokacin da ya ke kan tasowa gabanin rasuwarsa, mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), ya bayyana cewa ayyukan da gidauniyarsa ta ke gudanarwa su na faruwa ne saboda irin tarbiyya tagari da mahaifinsa ya yi.

Malam Kashif Inuwa Abdullahi, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni, 2022 a garin Haɗejia, jim kaɗan bayan sun kammala rabon kayan tallafin sana’o’i da gidauniyar ƙasar Qatar da haɗin gwiwar tasa gidauniyar su ka samarwa al’umma a Jigawa.

Tunda farko, Malam Kashif Inuwa, ya fara ne da bayyana cewa: “Ita wannan gidauniya mun fara ta ne a saboda abin da mahaifinmu ya ɗora mu a kai tun a lokacin da mu ke tasowa cewa: duk abin da ka samu ba naka ne na kai kaɗai ba, naka ne na kai da ƴan uwanka. Tun a lokacin ko irin an aike ka an ba ka wani abu, ko ka zo da wani abu, zai ce ka raba ka ba wa ƴan wanka”. Inji Malam Kashif Inuwa Abdullahi.

Daga nan ya cigaba da cewa: “A lokacin da na fara karɓan tallafin karatu (Schoolarship) shi ne ya sa ni na rabar da kuɗin nan gabaɗaya ga ƴan uwa, a lokacin har zuciyata ma na cewa mai ya sa zai sa na yi haka ni ma da zan koma makaranta, amma saboda bin umarni dole na rabar da kuɗin duka. Lokacin da zan koma makaranta ya ɗauko kuɗi daga aljihunsa ya ba ni. Tun lokacin duk lokacin da na karɓi kuɗin tallafin karatu (Schoolarship) zai sa na raba shi gida (4) ya ce na raba kashi (1), kashi (3) cikin (4) kuma na ɗauka na yi amfani kaina da shi”.

Malam Kashif Inuwa, ya kuma ƙara da cewa: “Ko lokacin da na fara ɗaukan albashi da na fara aiki, albashin farko haka shi ma ya sa duka na rabar, na biyun ya sa na raba kashi huɗu na rabar kashi ɗaya kashi uku kuma na ɗauka na yi amfani da shi. To tun lokacin abin da na ke yi kenan har yau. Da na ga abin kuma ya na bunƙasa masu buƙatar kuma su na da yawa kuma Allah Ya hore za ka ga mutum ba wai iya ƴan’uwanka ne kawai ba, akwai maƙota, akwai abokai da sauransu, da haka sai mu ka fara taimakawa abokai da ƴan’unguwa da sauransu,”. Cewar Malam Kashif Inuwa.

Daga nan kuma sai ya cigaba da cewa: “Sai na ga domin a samu ɗorewar abin zai fi kyau a samu wata gidauniya saboda idan yau ina da hali gobe ba dole ne ya zama ina da hali ba, amma su waɗanda ka saba taimakawa wani idan ba ka nan shi kuma ƙarshen jin daɗinsa kenan, amma in aka samu irin gidauniyar nan sai a samu ƴan’uwa da abokan arziƙi su riƙa taimakawa, haka mu ka fara abubuwan mu ke abubuwan da zai taimakawa mutane da wanda zai kawo cigaba a gari”. Cewar Malam Kashif.

Dangane da batun alaƙar gidauniyar tasa da ƙungiyoyin ba da agaji na Duniya kuwa, Malam Kashif Inuwa ya yi bayanin cewa: “kuma sai mu ka ga ashe ma za mu iya zuwa mu yi haɗin gwiwa da wasu gidauniyar musamman ita wannan gidauniya ta ƙasar Qatar da kuma ta matasa musulmai ta Duniya, (WAMY). Mu na da kykkyawar fahimta da su, mu na da haɗin gwiwa da su, duk wani aiki da za su yi a Nageriya mu na cikin waɗanda su ke shawara da su, su ga a ina ya dace a yi, mai ya kamata a yi, shi ya sa mu ka ga indai an yi shawara in bai fi ƙarfinmu ba, za mu ce a kawo gida saboda komai an ce ka fara daga inda ka fito, shi ya sa za ka ga mu na kawo su,”. Iniji Malam Kashif”.

Da ya ke tsokaci dangane da nasarorin da aka samu daga lokacin da su ka ƙulla alaƙar haɗin gwiwar da ƙungiyoyin ba da agajin na Duniya zuwa yau, Malam Kashif Inuwa ya bayyana cewa: “Daga lokacin da mu ka fara da su zuwa yanzu, akwai masallatai waɗanda aka kammala da waɗanda ake kan aikinsu kimanin guda ɗari uku da hamsin a cikin Jihar nan (Jigawa), akwai rijiyoyin ruwa masu amfani da hasken rana guda ɗari biyu da tamanin da su ka yi”.

Da ya juya kan batun shirinsu na rabon kayan tallafin sana’a kuwa, Malam Kashif Inuwa ya bayyana cewa: “Dan haka yanzu sai su ka ce ai za su iya ma wasu abubuwan, shi ne mu ka fara wannan harka ta baiwa mutane abin da za su yi sana’a. Kamar yau an rabawa mutane wajen ɗari uku da hamsin kayayyakin sana’a daban-daban, akwai waɗanda aka ba su keken ɗinki, akwai waɗanda aka ba su mashin, akwai waɗanda aka ba su injin niƙa, akwai waɗanda aka ba su na’ura mai ƙwaƙwalwa”. -Inji shi.

Da ya juya kan batun shirinsu na gina gidaje kuwa, Malam Kashif Inuwa ya yi tsokaci kamar haka: “Bayan haka kuma, sai su ka ce ai akwai waɗanda ma ba su da gida, ba za su iya gidansu na kansu ba a rayuwa, shi ya sa su ka ce za su zo su gina gidaje guda hamsin da makaranta da masallaci waɗanda su ma za a ba wa mabuƙata, (mutanen da ba za su iya gina gida ba), a ba su wannan gidajen don su samu sauƙin rayuwarsu”. Cewar Malam Kashif Inuwa.

Daɗi da ƙari kuma, ya cigaba da cewa: “Duka abubuwan da mu ke yi ba wai abubuwa ne da kuɗi ya ke fitowa daga aljihunmu ba, yawanci mutanen da aka sani ne su ke taimakawa da kuma irinsu gidauniyar ta ƙasar Qatar”. Inji shi.

Malam Kashif Inuwa ya kuma ƙarƙare da nanata cewa: “Kamar yadda na faɗa tunda farko, wannan abu ne da na taso mahaifinmu ya ɗora ni a kai, duk sanda na yi ina jin daɗi. Na farko na yi abin da mahaifina ya ce na yi, na biyu kamar na sauke wani nauyi ne a kaina saboda shi Allah ma ya ce idan ya ba ka ba wai kai kaɗai ya ba wa ba, har ƴan’uwanka da abokan arziƙi. Ba abin da ya fi faranta min rai irin na ga wani mutum mai damuwa ya zo irin damuwarsa ta kai damuwa in taimaka ya samu wani sauƙi,”. Cewar mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa A. (CCIE).

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp