Gidauniyar Malam Inuwa ta Ɗauki Nauyin Koyar da Ƴa’yan Fulani Al-ƙur’ani
A ƙoƙarinta na ba da gudunmawa wajen magance matsalar tsaro, gami da fatanta na kyautata rayuwar al’umma, gidauniyar Malam Inuwa, ta ɗauki nauyin koyar da yara Fulani da iyayensu da ke rayuwa a cikin daji Ilimin Alƙur’ani mai girma na tsawon shekara guda.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mutanen “Rugar Gidan Maje” da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Tauran Jihar Jigawa, su ne su ka amfana, bisa ɗaukan nauyin jagoran gidauniyar, mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi (CCIE).
A ya yin bikin yaye ɗaliban da aka gudanar a wannan rana a (Rugar Ta Maje), Sarkin Taura Alhaji Rabi’u, gami da Wakilin Hakimin Taura, Dagacin Ƴan Yanga, Alhaji Auwalu Usman, sun yi jinjina tare da godiya da addu’ar fatan alheri ga mai girma jagoran gidauniyar, Malam Kashif Inuwa kan ƙoƙarinsa na ilimantar da jama’arsu.
Wannan cigaba ne mai girma wanda zai taimakawa jama’a matuƙa wajen sanin Allah gami da daƙile matsalar gurɓacewar tunani da ake samu a cikin jama’ar ƙasa da ke zaune a dazuka ko rugage wanda hakan ke haifar da ta’addanci saboda rashin ilimi tun daga tushe.












