Hukumar da ke sanya ido a kan kafafen watsa labaran Najeriya, National Broadcasting Commission (NBC) ta kwace lasisin wasu kafafen watsa labarai saboda gaza sabunta shi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A wata sanarwa da shugaban hukumar, Malam Balarabe Shehu Illela, ya fitar ranar Juma’a ya ce kafafen watsa labaran da aka kwace lasisinsu sun hada da Silverbird TV, AIT, Raypower FM, Rhythm FM da karin wasu da dama bisa gaza biyan kudin da suka kai N2.66 bn don sabunta lasisin nasu.
Sanarwar ta ce an dauki matakin ne bayan an wallafa jerin kafafen watsa labarai da ba su sabunta lasisinsu ba.
A cewar hukumar, an bai wa kafofin watsa labaran karin makonnin biyu a watan Mayu domin su sabunta lasisinsu ko kuma su fuskanci yiwuwar saoke su amma suka ki.












