Home Labarai Jami’an DSS Sun Kama Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji

Jami’an DSS Sun Kama Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji

Jami’an DSS Sun Kama Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji

 

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) sun kama tsohon ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, a safiyar ranar Laraba a filin jirgin saman Akanu Ibiam da ke Enugu.

Rahotanni sun ce an kama Nnaji ne yayin da yake shirin hawa jirgi zuwa Abuja.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce jami’an DSS sun kama shi ne bisa buƙatar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, wadda ake zargin tana bincikensa kan zargin amfani da takardun bogi

Daga bisani an miƙa shi ga hukumar ICPC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyin sun kuma ce ICPC ta taɓa gayyatar tsohon ministan sau da dama bayan samun koke-koke kan yadda ya gudanar da ma’aikatar da yake jagoranta, lamarin da ya sa ta nemi taimakon DSS domin cafke shi.

Uche Nnaji ya yi murabus daga muƙaminsa a ranar 7 ga Oktoban 2025, bayan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan takardun karatunsa daga Jami’ar Najeriya (UNN) da kuma takardar kammala bautar ƙasa ta NYSC.

A lokacin, ya ce murabus ɗin ba yana nufin amincewa da laifin da ake zarginsa da shi ba ne, illa dai mataki ne na mutunta tsarin shari’a, inda ya ce zarge-zargen suna da alaƙa da siyasa.

A watan Nuwamban 2025, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya domin tilasta wa Jami’ar da shugaban jami’ar su ba shi kwafin cikakken bayanan karatunsa.

Lamarin ya sake ɗaukar sabon salo ne bayan jam’iyyar PDP ta zaɓi Uche Nnaji a matsayin ɗan takararta na gwamnan jihar Enugu a zaɓen 2027.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp