Home Taska Dakarun Soji Sun Bankaɗo Wajen ƙera da Rarraba Bindigogi ga Ƴan Ta’adda

Dakarun Soji Sun Bankaɗo Wajen ƙera da Rarraba Bindigogi ga Ƴan Ta’adda

Rundunar Soji

Dakarun Soji Sun Bankaɗo Wajen ƙera da Rarraba Bindigogi ga Ƴan Ta’adda

 

Dakarun Rundunar sojoji na Operation FANSAN YAMMA sun bankaɗo wata masana’antar ƙera bindigogi haramtacciya da ake zargin tana samar da makamai ga ’yan ta’adda a Jihar Kebbi.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja ya ce dakarun sun kai samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan wani wuri da ake amfani da shi wajen ƙera da rarraba bindigogi.

A yayin binciken da aka gudanar, an ƙwato bindigogin AK-47 guda biyar da aka ƙera a cikin gida, sannan an kama mutum biyu da ake zargin masu ƙera da safarar makaman ne.

Ya ce, an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, yana mai cewa hakan wani gagarumin ci gaba ne a ƙoƙarin da ake yi na daƙile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma dakile hanyoyin da ’yan ta’adda ke samun kayan aiki.

A cewarsa, waɗanda aka kama na tsare a hannun sojoji domin ci gaba da bincike, yayin da ake farautar sauran mambobin ƙungiyar da masu ɗaukar nauyinsu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp