Juyin Mulki: DSS ta Gurfanar da Mutane 5 kan ɓoye Timipre Sylva
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Najeriya, DSS, ta gurfanar da wasu mutum biyar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zarginsu da ɓoye bayanai kan inda tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva yake.
DSS ta kuma zarge su da haɗa baki wajen aikata laifi ta hanyar ɓoye inda Mista Sylva yake, wanda ta ce mutum ne da hukumomi ke nema ruwa a jallo.
Dukkan waɗanda ake tuhuma sun musanta zarge-zargen da aka karanta musu a gaban kotu.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Lauyan DSS, Emmanuel Orubor, ya roƙi kotun ta sanya ranar da za a fara sauraron shari’ar, inda hukumar za ta gabatar da shaidu.
Sai dai lauyan wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma, Sanusi Musa, SAN, ya nemi a ba su beli bayan gabatar da hujjoji.
Mai shari’a Peter Lifu ya umarci magatakardar kotu da a tantance waɗanda suka tsaya wa waɗanda ake tuhuma har sai an cika sharuddan beli, inda kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali na Kuje.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Yuli.
Ana zargin Mista Sylva, tsohon ministan man fetur, da kasancewa jagoran yunkurin juyin mulki da ake zargin an shirya wa Shugaba Bola Tinubu.












