Home Labarai Gwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi...

Gwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi wa ƴan ƙasarta

Biance Ojukwu

Gwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi wa ƴan ƙasarta

 

Najeriya ta ce tana nazarin matakan da za ta ɗauka kan Afrika ta Kudu, bayan samun rahotannin kai hare-hare kan ƴan ƙasarta da take shirin fara kwashe su a gobe Laraba.

Ministar harkokin wajen Najeriyar Bianca Ojukwu ta ce gwamnatin ƙasar na duba yiwuwar mayar da martani kan abin da ke faruwa.

Ministar ta ce duk da yake wannan matakin abu ne da za a cimma matsaya kansa nan gaba, amma ana ci gaba da tattaunawa kan abin da ya dace a yi.

Ta zargi hukumomin Afrika ta Kudu da gaza yin komai kan hare-haren da ƴan ƙasarta ke kaiwa Ƴan Najeriya, inda ministar ta ce yawancin waɗanda ke zaune a can suna da takardu kuma sun cika duk wasu ƙa’idojin da suka kamata.

Bianca ta ce sun samu bayanan yadda aka wawushe shagunan ƴan Najeriya da ke sana’o’insu a ƙasar, wasu kuma an cinna wa shagunan nasu wuta tare da haramtawa yaransu zuwa makaranta saboda yadda ake cin zarafinsu.

Ta caccaki gwamnatin Afrika ta Kudu kan yadda har yanzu ba ta fito fili ta yi bayani da kakkausar murya ko ta ɗauki tsattsauran mataki kan abi da ke faruwa ba.

Ministar ta ƙara da cewa Najeriya ba ta ji daɗin hakan ba, ganin yadda ta ba Afrika ta Kudu gudummuwa sosai wajen gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata a ƙasar.

Kalama nata na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan ci rani ke ci gaba da zaman ɗarɗar a Afrika ta Kudu, inda ƴan ƙasar ke yin zanga-zangar ƙyamar baƙi da kuma buƙatar ƴan kama wuri zauna su bar ƙasar nan da 30 ga watan Yuni.

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da wasu matakai da ƙasar ke ɗauka wajen daƙile kwararar baƙin haure.

Sai dai kuma ya gargaɗi ƴan ƙasarsa da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp