Home Taska Ƴan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je...

Ƴan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je Sulhu a Zamfara

'Yan Bindiga

Ƴan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je Sulhu a Zamfara

Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da mutum kusan 40 bayan sun tafi yin sulhu da yanfashin daji a ƙaramar hukumar Maradun na Jihar Zamfara sun buƙaci a biya naira miliyan 100 kafin su sako su.

Mutanen da aka yi garukuwar da su a ranar Lahadi da yamma galibinsu dattawa ne, kamar yadda danmajalisar dokokin jiha mai wakiltar yankin na Maradun Maharazu Salisu ya shaida wa BBC.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Magamin Diddi wanda rahotanni suka ce yana a kusa da ɗaya daga cikin dazukan da ƴan fashin daji ke da sansani

A tattaunawarsa da BBC, Sunusi Ahmed Dosara ya ce: “Tun wata uku da suka wuce (ɓarayi) sun hana su (ƙauyen) zaman lafiya, ana cikin haka ne sai ɓarayin suka kwaɗaita musu cewa su zo a yi sulhu domin su bar su, su riƙa cin kasuwa.

“To daga nan sai dattijai suka je daji domin haɗuwa da ƴan bindiga, amma a lokacin da suka je sai ɓarayin suka riƙe su, sanan suka sako wasu daga cikinsu suka ce ba za su sake su ba sai an cika musu wasu sharuɗaɗa”.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce daga ƙididdigar da suka yi mutanen da ƴan fashin dajin suka riƙe “sun kai 39”.

Ya ƙara da cewa dukkanin mutanen da ake riƙe da su “maza ne dattawa”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp