Dakarun rundunar sojojin Najeriya ta Birged na 29 wadanda aka fi sani da Operation Hadin kai sun sanar cewa sun kama wasu mutum 13 masu sayar wa mayakan ISWAP kayayyakin da suke amfani da su a hare-haren da suke kai wa al’umomi a Jihar Borno.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Rahotanni daga yankin tafkin Chadi na cewa an kama mutanen ne ranar talata yayin wani samame da dakarun Najeriya da na Civilian JTF suka kai kasuwar Benishek a karamar hukumar Kaga.
Rahoton ya kuma ce an kama su ne yayin da suka kokarin fitar da man fetur mai yawa da abinci zuwa wurin da mayakan ISWAP suke.
Ga abin da wani ke cewa: “A duk ranar kasuwa, ‘yan kasuwa da ke wa mayakan ISWAP aiki kan tafi kasuwanni dmin sayo musu kayayyakin abinci da man fetur da layukan salula da kayan sanyawa da sauran kayayyain da suke bukata.”












