Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja Kan Mutuwar Masu Hakar Ma’adinai da Ake Zargi
Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin dakatar da Kwamandan Rundunar Tsaron Farar Hula ta Jihar Neja (NSCDC), Suberu Siyaka Aniviye nan take, bayan rahotannin mutuwar wadanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a jihar.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da dakatarwar a ranar Juma’a, inda ya kuma jagoranci gudanar da cikakken bincike kan yanayin da ya faru.
Rahotanni sun ce mace-macen sun faru ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a kusa da yankin MI Wushishi/Lukoto da ke Minna, babban birnin jihar Niger.
Read Also:
A cewar wata sanarwa da mai ba Ministan shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Alao Babatunde ya sanya wa hannu, mamatan suna cikin wadanda ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da aka kama yayin ayyukan tabbatar da doka da aka gudanar a wurare daban-daban a faɗin Jihar Neja a ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026.
Ministan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma ya ce binciken zai tabbatar da yanayin da ya shafi mutuwar.
“Wannan lamari ne mai ban takaici, duk da haka, za a gudanar da cikakken bincike yayin da kwamandan da abin ya faru a ƙarƙashin kulawarsa ke ci gaba da kasancewa a dakace,” in ji Tunji-Ojo.
Ya ƙara da cewa fifikon Gwamnatin Tarayya ya kasance kare rayuka da tsaron ‘yan ƙasa.
Ministan ya ce, “Muna gudanar da gwamnati wacce babban abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne tsaron rayuka kuma mun yi aiki tukuru don tabbatar da hakan.”
Tunji-Ojo ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu su kuma bi doka yayin da ake gudanar da binciken, yana mai jaddada bukatar a bar aikin ya ci gaba da gudana cikin gaskiya.
Ya kuma yi ta’aziyya ga gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da kuma iyalai da ‘yan uwan wadanda suka mutu a lamarin.










