Hukumomi a Afirka ta Kudu sun ce suna ci gaba da sa ido kan al’ummi bayan ƙaruwar ambaliya da ake fuskanta na tsawon makonni sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu.
A karshen mako, jami’ai suka buɗe hanyoyin ruwa a lardin Gauteng domin rage ruwan da ya cika a madatsar ruwa ta Vaal – wanda shi ne mafi girma a lardin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ambaliyar ruwan ta tafi da kayayyaki da dama.
Jami’ai sun ce a yi hakan ne domin kaucewa ɓallewar madatsar ruwan da kuma barazanar ta kan dubban mutane.
Sun kuma shawarci mutane da ke kusa da madatsar ruwan ta Vaal da su koma zuwa wani wuri har sai ruwan ya ragu.
PRNigeria hausa












