Home Labarai Gwamnati ta shirya muƙabala da Sheikh Idris game da kalamansa a kan...

Gwamnati ta shirya muƙabala da Sheikh Idris game da kalamansa a kan Annabi

Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi a Arewa mask gabashin Najeriya ta shirya muƙabala tsakanin malamai da kuma Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi kan kalaman da ya yi game da Annabi Muhammadu (SAW).

Wata wasiƙa da hukumar ta aike wa malamin, ɗan asalin jihar Bauchi, ta ce za a gudanar da tattaunawar ilimin ne gobe Asabar, 8 ga watan Afrilu a birnin Bauchi.

A farkon makon nan ne kalaman malamin suka fara tayar da hazo musamman a shafukan zumunta, bayan ya yi iƙirarin cewa “ba ya buƙatar taimakon Annabi”.

“Ana gayyatar ka zuwa tattaunawa ta ilimi [munaƙasha] game da kalamanka cewa ‘kai! …Manzon Allah ma ba ma son taimakonsa, ƙarewarta kenan’,” kamar yadda hukumar ta bayyana cikin wasiƙar.

An ga malamin ya bayyana cikin wani bidiyo a ranar Alhamis yana cewa ya ji daga wata majiya cewa zai yi muhawara da wakilan wasu ƙungiyoyin addini a jihar, waɗanda suka haɗa da Izala da ɗariƙa.

An yi irin wannan muhawara a Kano cikin watan Yulin 2021 lokacin da aka zargi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da yin kalaman ɓatanci ga Annabin Muhammadu.

Bayan muhawarar ne kuma, hukumomi suka gurfanar da malamin a gaban kotu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
TMS ta Horar da Mata Sama da 200 a Jihar Kogi Kan Tallan Dijital da Kasuwancin IntanetYadda Jami'an Tsaron Fadar Daura Suka Gaza Wa Mutanen Gari… Daga Abdullahi O HarunaBankin Duniya ya Sanya Lamunin Noma na $500m ga Gyare-Gyare, Rijistar Manoma ta DijitalGwamnatin Tarayya Ta Bukaci Bankuna Su Ba Wa Ƙananan da Matsakaitan Kamfanoni Lamuni Ba Tare Da Jingina BaMan Fetur da aka Shigo da Shi Daga Waje ya fi na Dangote Rahusa Da N102, PETROAN ta Shaida wa NMDPRANRS na Neman Dokokin Haraji Masu Sauƙi ga Masana'antar Kere-kereLabarin Siyasa: Gwani ya Bayyana Tikitin Obi-Kwankwaso a Matsayin Auren da ya DaceBayani: Daga Zargin Kisan Kiyashi zuwa Haɗin Gwiwar Tsaro Tsakanin Amurka da Najeriya Na Abbas BadmusTinubu Ya Taya Shugaban ICPC Murnar Zaɓensa a Matsayin Shugaban Ƙungiyar Kwato Kadarorin AfirkaSojoji Sun Kawar da Ƴan Ta'adda 3, Sun Kwato Babura a KatsinaNCS ta Tabbatar da Naɗin Manyan Jami'ai 3 na Fasaha a Hukumar Kwastam ta Duniya2027: Rikici ya Barke a Jam'iyyar NDC Yayin da Ake Zargin Jam'iyyar ta Ajiye N6.5bn a Banki, ta Yunwatar da Kamfen2027: Manyan ADC 5 Tare da Masu Ruwa da Tsaki Sun yi Watsi da Atiku, Sun Goyi Bayan TinubuKashifu Inuwa: Jagorantar Kamfen Na Dimokuraɗiyya Na "Tinubu Must Stay" Mai Inganci Na Abdulkadir IbrahimTsakanin Ƙuri'u Da Haihuwa: Lokacin Da Lambobi Suka Zama Ƙarfin Ƙasa Da Ba A Yi Amfani Da Shi Ba Na Haroon Aremu Abiodun, ANIPR
X whatsapp