Rahotanni na bayyana cewa ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 34 a wani hari da suka kai sansanin ‘yan gudun hijira da ke wata makarantar firamari a ƙauyen Mgaban da ke Ƙaramar Hukumar Benue ta Arewa a ranar Juma’a da daddare.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai cewa maharan sun isa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 9 na daren Juma’a.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce cikin waɗanda aka kashe akwai wata mata mai ciki da ɗanta sannan kuma da dama sun jikkata.
Ka zalika mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na Ƙaramar Hukumar Guma Christopher Waku, ya shaida wa jaridar cewa an kashe mutum 34 yayin da aka jikkata wasu 40 na daban.
Kakakin ‘yan sanda ta jihar SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar sakon waya da ta turawa wakilin jiridar, sai dai ba ta yi wani cikakken ƙarin bayani ba.











